KA KIYAYI SHARRIN BUTULU(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

KA KIYAYI SHARRIN BUTULU
Wannene Butulu? Butulu shine duk
wandan zai sakama alheri da
sharri. Mutunne kayi wa alheri, shi
kuma sai ya mayar maka da sharri.
Mutunne ka ganshi a shikkin rana
kajawo shi cikin innuwarka daga
karshe shi ne zai turaka cikin
Rana.
To menene maganin Butulci?
Watau, maganin shi, shine Ko mai
zakayi wa wani mutun kayi shi fi
sabilillahi ba don wani abu ba sai
don neman ladar Allah Madaukaki
kawai. Domin har in niyarka mai
kyau ce, tabbas Allah Zai saka
maka da alherinSa, shi kuma
butulun bai cuci kowa ba sai
kansa. Shine Allah Madaukaki Ya
muna mana darasi da masu
ayyukkan kwarai dominSa kawai,
Yace:
{ ﻭﻳﻄﻌﻤﻮﻥ ﺍﻟﻄﻌﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﺣﺒﻪ ﻣﺴﻜﻴﻨﺎ ﻭﻳﺘﻴﻤﺎ
ﻭﺃﺳﻴﺮﺍ (8) ﺇﻧﻤﺎ ﻧﻄﻌﻤﻜﻢ ﻟﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻧﺮﻳﺪ ﻣﻨﻜﻢ
ﺟﺰﺍﺀ ﻭﻟﺎ ﺷﻜﻮﺭﺍ] {ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ8 :، 9 ] “Kuma suna ciyar da abinci, a kan
suna bukãtarsa, ga matalauci da
marãya da kãmamme. (Suna
cẽwa): “Munã ciyar da ku ne dõmin
nẽman yardar Allah kawai, bã mu
nufin sãmun wani sakamako daga
gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya.”
To wanda halinsa ya kasance haka
a kyautatawa, bai kamata ya ji
takaicin butulu ba domin da ma
domin Allah ne kawai ya kyautata
masa. Saboda haka sharrinsa
bazai ragesa da komai ba.
Allah Ya nuna mana hanya
madaidai ciya. Amin!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “KA KIYAYI SHARRIN BUTULU(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)”
  1. Marwan B. Kabir Avatar

    Ameen Ya Sheikh

  2. SULAIMAN ILYASU Avatar

    Gaskiya ne Dr, Allah ya saka da alheri ya jikan malam.

Leave a Reply

Latest updates
Categories