Ka zama Mai hakuri

Danna nan domin shiga karatu Online

Yana daga cikin ɗabi’ar da Allah ya halicci ɗan Adam akai idan an masa wani abinda baiyi masa daɗi ba yakanyi fushi, wani lokaci fushin yakan kaishi ya aikata abinda daga baya zaiyi nadama akai.

Fushi ba kawai akan gama garin mutane ya tsaya ba. Hatta annabawa suma suna fushi kamar yadda Allah subhanahu wata’ala ya bada labarin kan Annabi Musa Alaihissalam lokacin da ya tafi gana wa da Ubangijinsa. mutanensa suka Koma bautar ɗan maraƙi wanda Samiri ya Haɗa musu. Allah ya baiwa annabi musa labarin abinda yake faruwa acikin mutanensa na bautan ɗan maraƙi. Annabi Musa ya dawo wurin mutanensa yana mai fushi dasu yana cewa tir da abinda kuka aikata baya na. Bai tsaya anan ba yaje ya kama kan ɗan’uwansa Haruna yana ja yana masa faɗa sabida shi aka barwa kula da mutanen. Allah ya bada wannan labari acikin surat A’araf:

(وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰۤ إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ غَضۡبَـٰنَ أَسِفࣰا قَالَ بِئۡسَمَا خَلَفۡتُمُونِی مِنۢ بَعۡدِیۤۖ أَعَجِلۡتُمۡ أَمۡرَ رَبِّكُمۡۖ وَأَلۡقَى ٱلۡأَلۡوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأۡسِ أَخِیهِ یَجُرُّهُۥۤ إِلَیۡهِۚ قَالَ ٱبۡنَ أُمَّ إِنَّ ٱلۡقَوۡمَ ٱسۡتَضۡعَفُونِی وَكَادُوا۟ یَقۡتُلُونَنِی فَلَا تُشۡمِتۡ بِیَ ٱلۡأَعۡدَاۤءَ وَلَا تَجۡعَلۡنِی مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِینَ)

[Surat Al-A’raf 150]

Toh amma sai dai fushi yana bambanta. Kamar yadda muka gani anan annabi Musa yayi fushi ne ya kuma ɗau mataki sabida an tsaɓawa wa Allah. Anyi masa shirka. Bawai yayi fushi ne ya kuma ɗau mataki sabida wani abu da akayi masa shi a karan kansa ba.

Haka muminai suke. A lokacin da aka taɓasu sai suyi haƙuri. Amma in aka taɓa Allah toh a lokacin ne za’a ga fushinsu.

Haka Manzon Allah shima. Baya Ɗaukar mataki don anyi masa ba daidai ba, sai dai in an taɓa Allah toh a lokacin ake ganin fuahinsa. An rawaito daga matarsa Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

مَا ضَرَبَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِيَدِهِ خَادِمًا لَهُ قَطُّ، وَلَا امْرَأَةً، وَلَا ضَرَبَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِيَدِهِ شَيْئًا قَطُّ، إِلَّا أَنْ يُجَاهِدَ فِي سَبِيلِ اللهِ، وَلَا خُيِّرَ بَيْنَ أَمْرَيْنِ قَطُّ، إِلَّا كَانَ أَحَبَّهُمَا إِلَيْهِ أَيْسَرُهُمَا، حَتَّى يَكُونَ إِثْمًا، فَإِذَا كَانَ إِثْمًا كَانَ أَبْعَدَ النَّاسِ مِنَ الْإِثْمِ، وَلَا انْتَقَمَ لِنَفْسِهِ مِنْ شَيْءٍ يُؤْتَى إِلَيْهِ، حَتَّى تُنْتَهَكَ حُرُمَاتُ اللهِ عَزَّ وَجَلَّ

Bukhari: 6786

Manzon Allah bai taɓa dukan wani mai masa hidima da hanunsa ba, ko mace, bai taɓa dukan wani abu da hanunsa ba sai dai wurin yin Jihadi don ɗaukaka kalmar Allah. Ba’a taɓa bashi zaɓin wani abu guda biyu ba face ya ɗauki wanda yake yafi sauƙi acikinsu sai dai in ya kasance saɓon Allah ne(Ma’ana acikin sauƙin akwai saɓon Allah) idan har ya kasance Akwai saɓon Allah aciki toh Annabi ya kasance yafi kowa guje wa saɓon Allah. Kuma baya ɗaukar fansa kan wani abu da za’ayi masa sai dai in ya kasance ana keta hurumin Allah.

haka halin Manzon Allah yake. Mai haƙuri da jin ƙai. Mai tausayi da sanin yakamata.

Shin yin fushi haramun ne?

Yin fushi ba haramun bane idan akayi wa mutum abinda bai dace ba. Domin shi fushi ɗabi’ar ɗan Adam ce. amma ɗaukan mataki akan fushin shine ba’a so mutum yayi. Kuma sabida zafin haɗiye fushi shi yasa Allah yayi tanadin lada mai yawa ga masu haƙuri da haɗiye fushi.

Allah ya sanya su cikin Masu tsoronsa kamar yadda ya bada labari acikin surat Aal emran 133-134:

(۞ وَسَارِعُوۤا۟ إِلَىٰ مَغۡفِرَةࣲ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِینَ)

(ٱلَّذِینَ یُنفِقُونَ فِی ٱلسَّرَّاۤءِ وَٱلضَّرَّاۤءِ وَٱلۡكَـٰظِمِینَ ٱلۡغَیۡظَ وَٱلۡعَافِینَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ یُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِینَ)

Allah yayi musu tanadin Aljanna babba mai cike da Ni’imomi:

Wa’inda suke ciyarwa a cikin wadata da tsanani, Masu haɗiye fushi masu yafiya ga mutane, Allah kuma yana son masu kyautata wa.

Kunga anan sun sami sifofi biyu masu kyau wanda kowani musulmi yanaso ya samesu: wa’innan sifofin sune:

  • Masu tsoron Allah
  • Masu kyautata wa

Allah ne ya bada shaida a kansu, yace haƙiƙa masu irin wannan sifofi sune masu taƙawa. Allah ya sanya mu cikinsu

Falalar haɗiye fushi:

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

ما من جرعةٍ أعظم أجراً عند الله من جرعة غيظ كظمها عبد ابتغاء وجه الله

Ibn Majah: 4189

Babu wani abin haɗiya da mutum zai haɗiya wanda yafi girman lada a wurin Allah fiye da haɗiye fushi wanda bawa zaiyi domin neman yardar Allah

An sake rawaito wa daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:

من كظم غيظاً وهو قادر على أن ينفذه دعاه الله عز وجل على رؤوس الخلائق يوم القيامة حتى يخيره الله من الحور العين ما شاء

Wanda ya haɗiye fushi alhali yana da daman ya ɗauki mataki akai. Allah zai kirashi ranan tashin Al’Qiyamah a gaban Halittu ya bashi zaɓi acikin matan hurul Ein ya zaɓi wacce tayi masa.

wannan hadisai biyu da ayan da muka kawo a baya sun nuna mana girman ladan wanda yake haɗiye fushinsa. Sai muyi ƙoƙari muyi koyi da manzon tsira Sallallahu alaihi Wasallama. Duk da abin bashi da sauƙi amma sai mu tuna ladan da yake ciki. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates