Mu guje wa Girman Kai

Girman kai yana daga cikin munanan halaye wanda zai iya hana Mutum Shiga Aljanna, Kuma yakan sa mai wannan Hali yayi baƙin jini a tsaƙanin Mutane.

Menene girman kai?

Shine mutum ya rinƙa ganin kansa cewa yafi kowa, Yana jiji da kansa yana ganin kowa a ƙasansa yake, Sannan ya rinƙa ƙasƙantar da wanda ya kamata a girmama su.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya Fassara Girman kai da cewa

Girman kai shine Ƙin gaskiya, da kuma Raina mutane da ƙasƙantar dasu

Muslim :91

Wannan yana nuna cewa yana daga cikin girman kai a faɗa wa mutum gaskiya yasan gaskiya ne amma kuma yaƙi ƙarba.

Zargin mai Girman kai

Girman kai laifi ne mai girma wanda idan mai ita bai tuba ya daina ba zai iya zama dalilin halakarsa kamar yadda Girman kai itace dalilin halakar iblis. Lokacin da Allah ya umarci Mala’iku suyi wa Annabi Adam Alaihissalam Sujada sai Iblis girman kai ta kama shi ya nuna cewa ai yafi Annabi Adam falala ta yaya zaiyi masa sujada? A dalilin Haka Allah ya fitar dashi daga cikin Aljanna sannan kuma ya la’ance shi. Kamar yadda Allah ya bada labari acikin Suratul Baqara Ayah ta: 34

Hakanan girman kai shine sababin halakar da da yawa daga cikin Al’ummomi da suka gabata, lokacin da Annabawansu suka zo musu da gaskiya sai suƙi karɓan ta, kamar yadda ta faru da Mutanen Annabi Nuhu Alaihissalam. Lokacin da yaje musu da gaskiya sai suka rinƙa sanya yatsansu a kunnensu suna rufe shi ta yadda ma bazasuji meye yake faɗi ba, sabida girman kai da ƙin gaskiya. Allah ya bada labarinsu acikin Suratu Nuh.

Hakanan ba komi ya halakar da Fir’auna da Qaruna ba sai girman kai da ƙin gaskiya, wanda a dalilin Haka Allah ya halakar dasu dukkansu.

An rawaito daga Abdullahi bin Mas’ud Allah ya ƙara masa yarda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

لا يدخل الجنَّة من كان في قلبه مثقال ذرَّة من كبر! فقال رجل: إنَّ الرَّجل يحبُّ أن يكون ثوبه حسنًا، ونعله حسنة؟ قال: إنَّ اللَه جميل يحبُّ الجمال، الكبر: بطر الحقِّ وغمط النَّاس

Muslim: 91

Ba zai shiga Aljanna ba, duk wanda akwai kwatankwacin ƙwayan zarra(mafi ƙanƙantan abu) na girman kai a zuciyarsa. Sai wani mutum yace: Mutum zai so ace tufansa yana da kyawu, takalminsa na da kyawu, Sai Annabi yace: Allah mai kyawu ne yana son Abu mai kyawu. Girman kai shine ƙin gaskiya da kuma raina mutane.

Muslim: 91

Wannan hadisi yayi bayanin Abinda ake nufi da girman kai.

Sanya tufa mai kyawu, ko shiga mota mai kyawu bashi ne girman kai ba, girman kai shine Ƙin gaskiya da kuma raina mutane da Wulaƙanta su.

Baya halatta Musumi ya zama mai girma kai domin girman kai yana daga alama ta Jahilci.

Musani cewa duk abinda Allah ya baiwa mutum a yau yakeyi wa Mutane girman kai Allah zai iya ƙwaceshi a kowani lokaci, in dukiya ne, Allah zai iya ƙwace wa, Mun sha ganin masu dukiya sun talauce, Hakanan mun sha ganin talakawa Allah ya basu kuɗi kuma duka cikin ƙanƙanin lokaci. To idan har haka lamarin yake menene na girman kai domin Allah ya baka dukiya? Baka tunanin wanda kake wulakanta wa yau zai iya yiwuwa gobe shine a samanka?

Hakanan idan kyawun halitta ne Allah ya baka kake wulaƙanta mutane baka tunanin Allah zai iya aiko maka da wata cuta tazo ta tafiyar da wannan kyawun sura taka? Ko wani haɗari?

Idan ilimin da Allah ya baka shiyasa kakeyi wa mutane girman kai baka tunanin Allah ka iya aiko maka da Wata cuta da zata rikita maka ƙwaƙwalwa ya zamto baka gane komai?

Idan Mulki ne Allah ya baka kake girman kai baka tunanin Allah zai iya ƙwace mulkin ya baiwa wani?

Duka wannan abin lura ne. Ba kafi kowa bane Allah ya zaɓe ka ya fifita ka akan mutane, yayi haka ne don ya Jarraba ka. To kada ka ɗauki tafarkin shaiɗan Wurin yin girman kai sai Allah ya ƙwace abansa ka dawo kana nadama, lokacin da nadama bazai yi amfani ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: