KALIMATU-TTAUHID(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

ﺷﻬﺎﺩﺓ ﺍﻥ ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺷﻬﺎﺩﺓ ﺍﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ
‘Yan’uwa Musulmi! Wadannan
Sentences biyu (jumloli biyu) su ne
ake kira lafuzan Tauhidi wanda shi
ne jigo na farko kuma mafi girma
cikin jigajigai biyar da ake da su
cikin Addinin Musulunci.
Shi wannan jigo na Tauhidi yana
da rassa biyu ne kamar yadda ake
gani:-
1. Shaidawa babu wani abin bauta
a bisa cancanta sai Allah Shi
kadai, saboda haka duk wanda
aka bauta wa in dai ba Allah ba ne
to zalunci a aka yi, saboda an ba
shi abin bai cancanta a ba shi ba,
an ba shi abin da yake ba hakkinsa
ba.
Tsaida wannan reshe na Tauhidi
yana nufin nisantar dukkan wani
nau’i na shirka.
2. Shaidawa Annabi Muhammad
mai tsira da amincin Allah Manzo
ne na Allah.
Tsaida wannan reshe na Tauhidi
yana nufin nisantar dukkan wani
nau’i na bidi’ah, watau kada kowa
ya bauta wa Allah Madaukakin
Sarki sai da abin da Annabi mai
tsira da amincin Allah ya shar’anta.
Ke nan za mu fahimci cewa: Shirka
da Bid’ah su ne kishiyoyin Tauhidi,
duk mutumin da yake shirka ko
yake yin bidi’ah to lalle babu
ingantaccen Tauhidi tare da shi.
Allah Ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta,
Ya nuna mana karya karya ce Ya
ba mu ikon guje mata. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates