Rashin shuwabanni na gari Yana daga cikin babban abinda mutane suke kokawa dashi a wannan zamani namu, a duk lokacin da sukayi ƙoƙarin kawo sauyi mai inganci sai abin ya juya sai suzo daga baya suna dana sani, suna nuni da cewa ai wanda ya gabata yafi wanda yake a yanzu.
A lokacin da mutane suke neman irin wannan canji na gari suna mance dasu karan kansu baki ɗaya, sai su ɗauka shi shugaba shine nauyi ke kansa na ya zama mutumin kirki amma su banda su, haka nan suke tunanin shugaba ne kaɗai ke da daman kawo gyara, sai su mance dasu kawo gyaran da zasu iya.
Akwai gyaran da sai shugaba ne zai iya, akwai kuma gyaran da idan mutane suka haɗu zasu iya kawoshi, sannan akwai gyaran da mutum ɗaya ma zai iya kawoshi, amma mutane sai su mance da wannan su rinƙa hangen shugaba kawai, hatta wasu lokuta su kan mance da neman taimakon Allah, sai su dogara da shugaba wanda wannan babban kuskure ne, domin duk wanda ka dogara dashi ba Allah ba akwana a tashi sai ya baka kunya.
Sannan mu sani yanayin mu yanayin shuwagabannin mu, in muka zamto mutanen kirki toh Allah zai kawo mana shuwabanni na gari, idan muka zamto mutanen banza toh haka Allah zai ɗaura mana shuwagabanni mutanen banza masu cin dukiyar Al’ummah da zalunci, da hukunci da abinda ba Allah ne ya sauƙar ba wanda wannan shine haƙiƙanin zalunci.
An rawaito wani daga cikin Sarakunan Banu Umayyah yaji labarin mutane suna magana akansa, da kuma mulkinsa, suna nuna bashi da adalci, kuma mulkinsa na cike da zalunci, sai yasa aka tara masa manyan mutanen garin sai yace musu: shin kuna son mu zamto kaman Abubakar da Umar? Wurin gaskiya da adalci? Sai sukace masa eh. Ai kaine Khalifa suma Abubakar da Umar halifofi ne, sai yace: toh ku kasance kaman Mabiya Abubakar da Umar, muma mu zamto kamar Abubakar da Umar. Haƙiƙa wannan magana ce mai kyau, (duk da bazata zamo hujja akan rashin adalci da yakeyi ba) domin idan mutane suna cikin Ni’imar Allah sai suka canza toh shima Allah zai canza musu wannan Ni’imar. Shiyasa lokacin su Abubakar da Umar aka samu adalci sabida lokacin suna tare da mazaje masu yin ɗa’a wa Allah. Da aka samu canji sai Allah ya turo irin wa’innan shuwagabannin. Allah maɗaukakin sarki yana cewa:
وكذلك نولي بعض الظالمين بعضا بما كانوا يكسبون
Kamar haka ne muke jiɓintar da sashin Azzalumai zuwa ga sashi domin abinda suka kasance suna aikatawa
Al-An’am: 129
Haka Allah yake lamarinsa, inka kasance azzalumi mai keta dokokin Allah sai Allah ya turo maka wani azzalumin yayi maganinka.
Sabida haka in munason shuwabanni na gari sai muma mun canza mun zamto na gari. Sannan muyi iya abinda zamu iya na wurin kawo gyara.
Wataƙila wani yace ni kaɗai me zan iya yi? Sai ka nemi masu taimaka maka, inbaka samu bai sai ka dogara ga Allah kayi iya abinda zaka iya yi, shi Allah zai maka hisabi akai, abinda bazaka iya ba Allah bazai tambayeka akansa ba, domin Allah baya ɗaura wa bayinsa wani abu sai in zasu iya yinsa.
Allah yace:
Kuma bamu ɗaura wa wata rai wani abu sai abinda zata iya.
Suratul-Mu’uminun: 62
Haka nan ya wajaba a garemu mu kame ga barin tsine wa shuwabanni da zaginsu komi lalacewarsu, abinda ya dace muyi shine muyi musu addu’a. In muna da damar yi musu nasiha muyi musu. In bamu da dama muyi shiru, domin zage zage bata da amfani.
Allah yasa mudace, ya bamu shuwabanni na gari.
Leave a Reply