KANA SON MANZON ALLAH S.A.W..?(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

KANA SON MANZON ALLAH
S.A.W..?
Annabi Muhammad dan Abdullahi
tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi shine fiyayyen halitta. Allah
ya zabe shi da zama shugaban
mazanni, kuma Annabin karshe.
Allah yayi masa baiwa da daraja
mai yawa da bawanda ya samu
kamar nasa cikin dukkan talikai.
Mu sani fa an aiko shi ne da sakon
yadda zamu bautawa Allah, don
haka aikinsa, shurunsa,
magananarsa, haninsa, umarninsa
da duk yadda ya gudanar da
rayuwar sa shine musulumci.
Babu wanda ake amincewa da
fadin sa, ko da umarnin sa cikin
addini sai ya dace da shiriyar
Manzon Allah saw. Wanda duk ya
kaucewa tafarkin Annabi saw, to ya
tabe kuma yayi hasara a duniya da
lahira.
Son manzon Allah saw ibada ne
kuma wajibi ne a garemu duka,
don haka mu kiyaye sunnar sa,
mubi umarnin sa, mu hanu daga
hanin sa, kuma mu gaskata
dukkan labaran da suka inganta
daga gare shi, sannan karmu
bautawa Allah sai bisa koyarwa sa.
Hakika dabi’a da halayen Manzon
Allah saw sune manyan abin koyi
ga rayuwar kowa, wato halin
karimci, tausayi, kyauta, yafewa,
hucewa, yawan ibada, dattaku,
hakuri, tausasawa, tsantseni da
zama cikin mutanen kirki, etc
Lallai Allah da mala’ikun sa suna
yiwa Annabi salati, ya ku wadanda
kukayi imani, kuyi salati a gareshi
tare da sallamewa. Allah yasa mu
dace, amin

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates