Bayan ayoyin Alqurani, akwai maganganu na Manzon Allah (S.A.W.) da suka qara tabbatar da saqon Musulunci, wanda jigonsa shi ne bin Allah da ManzonSa. A cikin wani ingantaccen Hadisi Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa:
“Wanda ya yi mini da’a to haqiqa ya yi wa Allah da’a, wanda kuma ya saba mini, to ya saba wa Allah.”
A wani Hadisin kuma wanda ya zo da Isnadi mai kyau cikin Muwadda Imam Malik, wanda kuma Hakim ya ruwaito shi, Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: “Na bar muku al’amura guda biyu wadanda ba za ku taba bata ba mutuqar kun yi riqo da su; littafin Allah da Sunnar ManzonSa!”
Haka ma cikin wani ingantaccen Hadisi wanda Bukhari da Muslim suka rawaito, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Dukkan al’ummata za su shiga Aljanna sai dai wanda ya qi”, sai aka tambayi Manzon Allah (S.A.W.) cewa wane ne zai qi? Annabi (S.A.W.) ya ce, “Wanda ya yi mini biyayya zai shiga Aljanna, wanda ya saba mini to ya qi.”.
Wata rana Umar dan Khaddab (R.A.) ya zo ga Manzon Allah (S.A.W.) da wani yanki na Attaura ya nuna masa ita, amma sai Annabi (S.A.W.) ya yi shiru bai ce masa komai ba. Sai Umar (R.A.) ya bude takardun Attauran ya fara karantawa. Wannan ya sa Annabi ya sauya fuskarsa don damuwa. Da Abubakar Siddiq (R.A.) ya lura da haka sai ya jawo hankalin Umar (R.A.) da wannan rashin jin dadi na Manzon Allah (S.A.W.). Don haka nan da nan Umar (R.A.) ya rufe takardunsa. Shi ne Manzon Allah (S.A.W.) ya ce musu, “Na rantse da wanda numfashin Muhammadu ke hannunsa da Musa zai bayyana gareku, kuma kuka bi shi ku bar hanyata da kun bace kun fada mummunar hanya.” Sannan Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “…..Da yana raye (shi Annabi Musa) kuma ya riski Annabcina da ya bi ni.”
A kan wadannan dalilai da suka gabata daga ayoyin Alqur’ani da Hadisan Annabi (S.A.W.) za mu fahimci cewa babu makawa sai mutum ya yi muwafaqa da bin tafarkin Manzon Allah (S.A.W.) kafin ya yi addini karbabbe.
Bayan mun fahimci wajibcin bin Sunnah, lallai ne kuma mu gamsu da cewa babu wani alamari na addini, na umarni, ko hani, wanda Allah (S.W.T.) Ya hukunta, amma bai isa ga mutane ba a zamanin Manzon Allah (S.A.W.), Ubangijin halitta da KanSa Ya tabbatar da cikar addininsa, kamar yadda ya ambata cikin Alqurani cewa:
“A yau Na cika muku addininku, Na cika ni’imata a gareku Na kuma zaba muku Musulunci ya zama addininku.” (Ma’ida: 3).
Leave a Reply