Magabata na qwarai daga sahabban manzon Allah (S.A.W.) da wafanda suka biyo bayansu tare da kyautatawa, sun rayu ne cikin riqo da littafin Allah da kuma Sunnar manzon Allah (S.A.W.). Bayin Allah ne masu nagarta wadanda aka haramta wa musulmi aibata su. Wadannan su ne muminai na gaskiya wadanda suka sarayar da rayuwarsu kamar yadda manzon Allah (S.A.W.) ya koyar. Wanda duk ya yi riqo da wannan hanya ta magabata na qwarai to ya yi riqo ke nan da igiyar Allah. Allah (S.W.A.) ya ambaci martabar muminai na gaskiya wadanda suka bi tafarkin manzon Allah (S.A.W.) a wurare da dama cikin Alqurani. Misali akwai a cikinsu wadanda aka siffanta su da tsananin gaskatawa kuma wadanda aka yi musu tanadin kyakkyawan sakamako daga Ubangijinsu: “Kuma wadanda suka yi imani da Allah da manzonSa su ne masu cikakkiyar gaskatawa kuma suna masu shaida a wurin ubangijinsu. Suna da sakamakonsu da kuma haskensu.” (Hadid:19).
A wata ayar kuma Allah (S.W.T.) Yana cewa: “Ranar da za ka ga muminai maza da mata haskensu na tafiya a gaba garesu, da kuma damansu. Ana ce musu bushararku a yau, ita ce Aljanna. Qoramai na gudana daga qarqashinsu suna masu dawwama a cikinta. Wannan shi ne babban rabo mai girma.” (Hadid: 12).
Dukkan abin da aka yi tanadi ga muminai na yardajjiyar rayuwa a nan duniya da kuma sakamako da gidan aljanna bayan an koma ga Allah, yana samuwa ne ga wadanda suka yi riqo da Sunnar Manzon Allah (S.A.W.), wadda ita ce hanyar da magabata na qwarai suka runguma. Babu kuma martaba da ta wuce wadda Allah (S.W.A) Ya ambata ga wadannan bayi nasa na qwarai:
“Lallai ne wadanda ke cewa ubangijinmu shi ne Allah, sannan suka daidaitu, to Mala’iku na sauka a kan kawunansu (a lokacin ajalinsu, suna ce musu) kada ku ji tsoro, kuma kada ku ji baqin ciki, kuma ku yi bushara da Aljanna, wadda aka yi wa’adi a gareku. Mu ne majibantanku masoyanku cikin rayuwar duniya da lahira. Kuma da abin da rayuwarku ke sha’awa, kuma kuna da (dukkan) abin da kuka kira a cikinta.” (Fussilat:30-31).
Duk wanda ya yi riqo ga tafarkin magabata, zai samu rayuwa cikin bin sunnar manzon Allah (S.A.W.), haka kuwa zai tabbatar masa da alherin rayuwa a nan duniya da kuma bayan komawarmu zuwa ga Allah. Tsayuwa a kan koyi da karantarwar Annabi (S.A.W.) da sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu wajen bin tafarkin da suka bi shi ne, Bin tafarkin Magabata na Qwarai. (Manhajus Salafis Salih).
Leave a Reply