KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 018 AQIDAR AHLUS SUNNAH (Daga Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimin).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

8. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai shi Allah madaukakin Sarki, duk da cewa yana sama a kan Alarshi to yana tare da bayinSa da iliminSa, Yana kuma sane da halayensu, Yana kuma ganin ayyukansu, Yana juya lamuransu Yana jin zantuttukansu, Yana kuma dora wanda ya sami karaya, Yana kuma daga kafadun bayinSa, Yana ba wanda Ya ga dama mulki, Yana kuma qwace mulki daga wanda Ya ga dama, alheri a hannunSa ya ke, Shi kuma ke da ikon komai.
“Babu wani da ya yi kama da Shi (Allah) Shi ne Mai ji (Kuma) Mai gani.” (Shura:11)
Ba za mu fadi zancen nan da ’yan ‘Hululiyya’ ko kuma ‘yan ‘Jahmiyya da makamantansu ke fada ba, cewa Allah Yana ko ina tare da bayinSa a bayan qasa. Kuma duk wanda ya fadi haka muna ganin cewa ya kafirta kuma ya bata, don kuwa ya sifanta Allah da abin da bai kamace Shi ba na tauyayyun kamanni.
9. Muna kuma ba da gaskiya da duk abubuwan da Maaikin Allah (S.A.W.) ya fada game da Allah. Cewa Shi Allah Yana sauka zuwa ga saman nan ta duniya kowane dare har ya zuwa sulusin dare na qarshe, yana cewa wa zai kira Ni, in amsa? Wa zai roqe Ni in ba shi? Wa zai nemi gafara in gafarta masa?
10. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai shi Allah Mai Girma kuma da daukaka, zai zo ranar qiyama don Ya yi hukunci tsakanin bayin. Hujjar wannan ita ce fadarSa Allah ta’ala, A hir! Bari wannan maganar idan aka dandaqe qasa dandaqewa, kuma Ubangijinka Ya zo, Mala’iku kuma suka yi jere sahu-sahu. Ranar za a ga wutar Jahannama. Ranar ce mutum zai tuna da Allah, tunawar kuma ba za ta yi masa amfani ba. (Suratul Fajr :21-23).
11. Muna kuma ba da gaskiya cewa Shi Allah Shi ne mai aikata abin da Ya so. Muna kuma ba da gaskiya cewa, nufin Allah (abin da Ya so) iri biyu ne: akwai Irada kauniyya (kasantacciya). Ita ce wacce abin da ya nufa yake afkuwa, ko da kuwa wannan abin bai kasance abin soyuwa ne a gare Shi ba. Ita wannan dangi ta Irada ita ce ake nufi da Mashia wato abin da Allah Ya nufi afkuwarsa tun kafin halitta, kamar yadda Allah Taala Ya fada:
In da Allah ya so da ba su yaqi juna ba, sai dai Allah Yana aikata abin da Ya so.
Ya kuma ce:
“In Allah Ya kasance Yana nufin Ya batar da ku, Shi ne Ubangijiku.” (Hud:34)
Dangi na biyu, ita ce Irada Shar’iyya”: Ma’anarta abin da Allah Ya so, ko da kuwa bai Yi nufin afkuwarsa ba.
Kamar fadar Allah ta’ala da ya yi cewa:
“Allah Yana son Ya karbi tubanku.” (Nisa’i:27).

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates