KARANTARWAR SHEHU USMAN
DAN FODIYO A KAN BIN SUNNAH
(2)
Ci gaba …
4. An yi tambaya, shin ko ya
halatta ga wanda ya riga ya kama
wata mazhaba ayyananniya ya fita
daga gare ta? A wajen jawabi an
ce, “Na’am,” zai iya fita yanke.
Rafi’i shi ne ya inganta wannan
ra’ayi. Ko da yake wani qaulin an
ce ba zai iya fita yanke ba, domin
ya riga ya daure kansa. A qauli na
uku kuwa aka ce bai halatta ya fita
da wadansu mas’alolin mazhaba
ba, sannan ya ci gaba da riqo da
wasu mas’alolin.
5. Duk Mujtahidi da ya sava wa
nassin Alqur’ani da Hadisi ko
Ijma’i, ba za a bi shi ga wannan
magana ba.
6. Duk abin da almajiran mujtahidi
suka fahimta daga maganar
mujtahidin nan ba za a lissafa da
shi ba a cikin mazhabarsa. Amma
daga baya, sakacin mutane ya yi
yawa har suka riqa jingina
ra’ayoyin masu wallafar littafi da
masu yi wa littafi sharhi ga
mazhabar wadanda suke koyi da
shi, suka mai da su kamar
ra’ayoyin mujtahidin nan na asali.
Sai daga qarshe al’amari ya koma
ga su almajiran suna koyi da
ratayawa da junansu. Ta haka har
ya zama kowane littafi ya kai Juz’i
ashirin, alhali kuwa ainihin
maganar mujtahidin a cikinsa idan
an tara ba za ta kai Juz’i daya ba.
Wajibi ne a kan kowane Musulmi
mukallafi ya qudurta cewa dukkan
Imaman Musulmi a kan shiriya ta
Ubangijinsu su ke. (Wato ba sa
cikin bata). Wato su Imamu Abu
Hanifa, Maliki, Shafi’i da Imamu
Ahmad bin Hambal.
8. Wajibi ne a kan kowane
Musulmi Mukallafi kada ya yi
qyamar aiki da maganganunsu
(Mujtahidan). Wadansu mutane a
yau sun kasance idan waninsu ya
yi amfani da maganar da ba ta
Imaminsa ba, sai ya ce, “Bari in yi
koyi da shi don larura.” Watau ya
yi aiki da hukuncin a kan hukuncin
larura wadda take halartar da abin
da aka hana. Sai ya ga kamar dai
ya afka ne a cikin zunubi. To ya
sani cewa wannan aiki nasa da ya
yi na qyamar hukuncin Mujtahidin
nan, shi ne babban zunubi wanda
ya wajaba ya tuba saboda aikata
shi, kuma ya nemi gafara a wurin
Allah. Domin da su irin wadannan
mutane sun yar da cewa dukkan
Imaman Musuluunci a kan shiriya
su ke, da ba su yi qyamar aiki da
magabatansu ba, domin shiriya ba
a qyamar ta matuqar dai an
tabbata ita ce.
9. Duk wanda ya bar aikin da aka
yi sabani a kan zamowarsa wajibi,
ko kuwa ya aikata abin da aka yi
sabani a kan zamowarsa haram, to
ba za a yi masa inkari ba, idan har
ya dogara da qaulin malami. Sai fa
idan ya dogara ga maganganunsa
wadanda suka saba wa nassin
Alqur’ani da Sunnah ko Ijma’i.
Amma matuqar aikinsa ya yi daidai
da wata maganar Mujtahidi na
Alhalus-Sunnah, to ba za a yi
masa musu ba. Amma da a ce an
yi musu shi ne a ce abin da
wannan mutum ya yi haram ne.
Amma da a ce an yi musu ne da
nufin shiryarwa ko don yi masa
nasiha, to shi wannan ba za a kira
shi inkari ba. Amma a wajen babin
fatawa, malamin da ke yi wa
mutane fatawa da wani qauli
manisanci ga hankali, ko kuma mai
raunin hujja, ya bar mashahuriyar
magana mai qarfin hujja, to za a
iya yi masa inkari domin bai
halatta a yi fatawa ba sai da
mashahuriyar magana mai qarfi.
10. Mutum wanda za a yi wa inkari
na hukunci, shi ne wanda ya sava
wa nassin Alqur’ani da Sunnah ko
na Ijma’i.
Wannan bayani na Shehu Usmanu
dan Fodiyo ya nuna mana irin
tsarin karantarwar Shehun
Malamin. Sannan za mu fahimci
cewa riqo da mazhaba guda daya
ba tilas ba ne cikin addinin Islama.
Haka kuma riqo da mazhabar ba
laifi ba ne, sai dai in ka yi watsi da
maganar Manzon Allah (S.A.W.)
ingantacciya don riqo ko bin
jagoran mazhabar, to a nan kam an
kauce wa karantarwar Annabi
(S.A.W.) da Sahabbai da sauran
magabata na qwarai har da shi
jagoran Mazhabar da kake bi din.
Domin dukkansu sun ce in an ga
Hadisi ingantacce ya sana da
fatawa ko karantarwarsu to a ajiye
maganarsu a dauki ta Manzon
Allah (S.A.W.) ita ta fi daidai
(Wallahu A’alamu).
Leave a Reply