KIRISTANCI II

Danna nan domin shiga karatu Online

By: Hamza Diso

Rubutaccen sabon Alqawari shine ya kamata ya zamo mikakkiyar hanya zuwa ga Allah madaukaki,

to amma abun ba haka yake ba, asalima ko gospels guda gudu ta aka yadda dasu ba wahayi ne daga Allah ba, kiristoci – da ijma’insu – sun san cewa babu wani littafi da Yesu ya wallafa, su wadannan gospels din rubutu ne da akayi wanda yake bayar da tarihin Yesu kamar yadda su marubutan suka hakaito, kenan kowanne littafi daga cikin su ana jingina shi zuwa ga mawallafinsa ne ba zuwa ga Yesu ba.

Haka suma sauran rubuce-rubucen da suke cikin sabon Alqawari, dukkannin su ana jingina su ne ga mawallafansu. Bari ma akwai wadanda sun fi kama da labaran addinin gargajiya kamar

( The revelation) na John, wanda ya kamata ace kirista suna jin kunya idan aka danganta musu wannan wasan kwaikwayo. Kenan dai duk abinda yake cikin sabon Alqawari bashi da alaqa da Yesu, bari ma Yesu bayanan aka rubuta su, kuma dukkannin su babu wanda aka rubuta da yaren yesu, don yesu yana magana ne da yaren Aramaic, su kuma duk gospels ba wanda aka rubuta da wannan yaren.

Duk da haka ba anan maganar ta kare ba, ko wanne littafi daga cikin wadannan littattafan idan ka dakko shi zakaga yana kunshe da abubuwa dayawa da zasusa ayi shakka akan sa. Bari na baka misali akan Matthew, Matthew daya ne daga cikin dalibai (manzanni) 12, wanda asalinsa mai karbar haraji ne, daga baya yesu ya zabe shi ya mayar dashi dalibinsa, yazo acikin Matthew chapter 9 verse 9 cewa: As Jesus passed on from there, he saw a man called Matthew sitting at the tax booth, and he said to him “follow me” and he rose and followed him.” Daga nan yayi imani yabi yesu, kuma har bayan dauke Yesu ya cigaba da da’awa har aka kashe shi a habasha.

To amma maganar gaskiya itace bamu da tabbas akan cewar shi wannan Matthew shi ya rubuta gospel, don a gospel din da ake jingina masa zakaga yana yawan naqalto abubuwa daga gospel din mark, shi kuma mark a rajihi bai hadu da Yesu ba, to ta yaya dalibin yesu zai dinga dogara da wanda ba dalibin yesu ba? Sannan baya hakaito labarin abinda ya faru da Yesu a gabansa!! Sannan yana yawan dogaro da tsohon Alqawari don ya nuna gaskiyar yesu har ma yana fassara wasu maganganun ba a yadda suke a tsohon Alqawari ba!!Wannan yasa wasu cikin kiristoci suke shakka akan waye wannan Matthew din, sannan bayan haka an ce ya rubuta gospel din sa ne da yaran yahudanci, sai dai bamu samu copy din asalin rubutun nasa ba, abinda ake dogara dashi shine wata tarjama da akayiwa littafin zuwa yaran girkawa, sai dai bamu san waye yayi tarjamar ba, bamu san amanarsa da Ilimin sa ba! Sannan acikin littafin akwai kusakurai ciki har da ishara akan za ayi tashin qiyama tun kafin ‘yan zamanin yesu su kare,!! Ina zaton yanzu muna 2021 ko?? Sannan ya bude littafinsa da nasabar yesu tun daga kan Annabi Ibrahim har zuwa kan yesu, mu manta da cewar nasabar taci karo da wadda luke ya kawo, shin baku lura da cewar bai kamata Allah ya zamo yana da nasaba ba??Sannan me yasa nasabar take bi takan mijin virgin marry? Wato Yusuf, shin babansa ne??Wannan fa banyi magana akan naqadin abinda littafin ya qunsa ba! To yanzu don Allah littafin da bamu san wanda ya rubuta ba, bamu san wanda ya tarjama ba, sannan ya kunshi kusakurai ta yaya zai zamo mai tsarki?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates