KUYI RIKO DA IGIYAR ALLAH BAKI DAYA KADA KU RARRABA

·

·

ﻭﺍﻋﺘﺼﻤﻮﺍ ﺑﺤﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﻭﻟﺎ ﺗﻔﺮﻗﻮﺍ
Kuma ku yi daidami da igiyar
Allah gabã ɗaya, kuma kada ku
rarraba. Al-emran(103)
Yana Daga cikin Alamun hadin kan al’ummah da tabbatuwarta, samun shuwagabanni na gari. Da zarar Allah yayi wa al’ummah Gam da katar da samun shuwagabanni na gari toh hakika Ya mata Ni’ima babba.. Shiyasa maqiya addinin musulunci basu ci nasara akanmu ba saida suka Ruguza mana shugabancinmu, suka rarrabemu da yanayin kasa da kabila. Ya zamto kowa yana alfahari da kasarsa da kuma kabilarsa. Ya bar alfahari da addininsa.. Ya zamto musulmi yana fifita Kafuri da suka fito yanki daya akan musulmi wadda baya yankinsa ko yarensa.. Wannan ba karamin ci baya bane, awurin musulmai.. Annabi(sallallahu alaihi wasallam) yace: ‘mumini da mumini kaman ginine sashi na taimaka wa sashi’ ba’asan wannan rabe raben kasa ko na yare ko kabila ba…
Sahabban manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) dashi kansa da wadda suka biyo bayansu sunyi jihadi da takwabi sun kashe ankashesu. Sun zamto ‘yan’uwa babu bambancin yare ko kabila ko yanki. Suka tabbatar da tauhidi a ban kasa… Wanda ayanzu muke cin moriyarta.
Yanzu kuna nufin in mukaci amanar wannan jihadi tasu Allah bazai tambayemu ba?
Mu yanzu abinda ake nema daga garemu ba daukan takwabi ayi yaki ba, A’a duniya ta shiga wata sabuwar tsari da Za’a iya bi ta lumana don cimma buri. Wanda inba bukatar makami tazo ba ba’a bukatarta.
Matakai biyu zamu fara bi don dawo da Martaba ta musuluncin da muka ruguza..
1. Mu dawo da ‘yan’uwantakarmu.. Duk nisan inda kafito ka fifita ‘yan’uwantakar musulunci kan ‘yan’uwantaka ta yare kabila ko Yanki ko Dangi..
2. Tabbatar da shugabanci. Mu sami shuwagabanni damuka yarda dasu. Bawai aka daura mana ba. A’a yazamto mu muka zabesu kuma mun yarda dasu..
Wallahi Allah ya sanyamu akan wannan kasane domin muzamto khalifansa. Kuma sai ya tambayemu me muka gudanar akanta. Mu kula. Muyi abinda zamu iya don tabbatar da wa’innan abu biyu komai insha’Allah na alheri zai biyo bayansu. Cin mutunci da kisa da akeyiwa musulmai za’a dainashi inhar aka sami hadin kai akan gaskiya da kuma shugabanci da kaunar juna… Allah taimakemu ya kuma fitar damu daga qunci damuke ciki.. Ameen.

One response to “KUYI RIKO DA IGIYAR ALLAH BAKI DAYA KADA KU RARRABA”
  1. Alameen Avatar
    Alameen

    Gaskiya malam wannan shine hakikanin hanyar hadin kai allah ya saka da alkhairi amin

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: