Kuyi Wa Kanku Hisabi Kafin Ayi Muku

Danna nan domin shiga karatu Online

Yiwa kai Hisabi

Umar Bn Khaɗɗab yana cewa: kuyi wa kanku hisabi kafin ayi muku, ku ƙididdige ayyukanku ku saka su a sikeli kafin Ayi muku. Domin hakan zaifi muku sauƙi gobe ranar Hisabi.

A kullum mumini ya dace ya rinƙa yiwa kansa hisabi yana duba ayyukansa mai kyau domin ya ƙara, mara kyau kuma domin ya ƙaurace masa, ya kuma tuba zuwa ga Allah. Amma a lokacin da mutum ya zamto baya hisabi wa kansa hakan zai gadar masa da Shagala. Yana laifi baya damuwa dashi, har laifin ya zamto masa jiki.

Babu wanda yasan ranan mutuwarsa, haka ne yasa ya kamata mumini ya lazimci hanya miƙaƙƙiya ya kuma bi dokokin Allah gwargwadon iyawansa, ya kuma ƙaurace wa Abin da Allah yayi hani akai baki ɗaya. Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallama) yana cewa: “duk abinda na Umarceku dashi kuzo dashi gwargwadon iyawanku, duk abin da hane ku akai ku ƙaurace masa”.
Shi addinin musulunci addini ne mai sauƙi. Allah baya Ɗaura wa bawa abinda yafi ƙarfinsa, kuma A duk lokacin da bawa ya gaza zuwa da abinda Allah ya umarce shi dashi domin wata lalura toh Allah bazai kamashi da laifin komai ba.
Ƴan’uwa muyi lura da wa’inda suka mutu suka barmu cikin wannan duniya, ita duniya ba komai bace face wata hanya da mutum zai wuce domin zuwa rayuwa ta Haƙiƙah. Wato rayuwar Lahira. Wani kuna tare dashi, da dare da safe kaji ance ya mutu, wani kuma kuna tare dashi da safe kafin dare kaji ya mutu. Kana nan a duniya kana ta burace burace, bakasan kwanakin ka sun riga sun ƙare ba. Ka lazimci Hanyar Allah da Manzonsa, sannan kayi amfani da lokacinka wurin bauta wa Allah domin anan duniya ake shuka hatsin da za’a girba ranan Tashin Qiyaamah.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates