KWALLIYAR MATA A MAHANGAR
MUSULUNCI.
Sakon da Annabi Muhd (S.A.W) ya
zo da shi, bai takaitu kan alaka
tsakanin bawa da ubangijinsa ba
kawai, ya tsallaka har zuwa ga
yadda bawa zai kula da gangar
jikinsa da kuma yadda zai gudanar
da zamantakewa da sauran
halittun Duniya.
Mata sune Allah ya bada shaida a
kansu cewa: An gina dabi’arsu kan
son kawa an kuma tayar da su a
cikinta, sannan kuma Musulunci ya
karfafi mabiyansa kan cancada
ado yayin zuwa masallaci, ya kuma
tuhumci wanda yake tsammanin
cewa ba dabi’ace ta mumunai ba.
Allah yace: “ KA CE: WANENE YA
HARAMTA KAWAR(kwalliya) DA
ALLAH YA FITARWA BAYINSA”
Manzon Allah kuma ya karfafi haka
cikin Hadisansa yace: ‘’ Allah mai
kyau ne, yana son Abu mai kyau”.
Abdullahi dan Abbas ya na cewa: “
Na kasance ina cancada ado wa
matata kamar yadda take cancada
min”.
Musulunci shine addinin da ya
sanya wanka da kawar da kazanta
daga jikin musulmi a matsayin
ibada, kamar su; yanke kumba,
tsige gashin hammata, aske gashin
gaba, tsabtace hakora{Aswaki},
balle sanya turare, shafa mai dss.
Amma musulunci bai bar wannan
Ibada kara zube ba, sai da ya
sanyawa ‘yan uwa Mata wassu
ka’idoji a matsayin yanda ya
kamata su gudanar da ita.
‘Yar uwata, Duk da cewa kwlliya
addini ne amma sai a ringa kulawa
da wadannan abubuwa:
• Kada kwalliyarki tai kama da na
Matan Arna, don Manzon Allah
yace:” wanda yai kama da wassu
yana tare da su.”
• Kar kiyi kwalliyar da za mai da ke
kamar Maza. Manzon Allah yace:
“Allah ya tsinewa mai kama da
Maza cikin Mata”.
• Kar Kwalliyar ta kunshi canja
halittar Allah, kamar kulla gashinki
da wani gashi, ko kuma canza fatar
jikinki, ko kuma bankare tsakanin
hakoranki don fitar da wushirya ko
kuma yin zane a fuska ko a wani
bangare na jikinki. Amma gyara
halittar da Allah yai miki ba Laifi,
kamar sa gashi ya yi santsi, ko
mikar dashi, ko sa masa abinda zai
kara tofar da shi.
• Kada ya zamanto cikinkin
kwalliyar akwai barnatar da dukiya,
Allah yace: “ ku ci ku sha, kar ku
barnatar da dukiya, Allah ba ya son
masu Ballagaza”
• Kar ya zamanto akwai bata
lokaci, Ta yanda mafi yawan
lokacinki zai tafi ne cikin kwalliya.
• Kada wannan kwalliyar ta
zamanto tana kunshe da cutarwa
wa jikinki, domin jikinki yana da
hakki a kanki, wannan cutarwar
yanzu yanzu ne ko kuma sai daga
baya.
• Kar ya zama cikin kayan da aka
kera wannan abin kwalliyar yana
kunshe da najasa.
• Wanda kike fatar kwalliyar ta
burgeshi ya zamanto mjinki, ba ki
ringa rabawa Jama’a kirarki fi
sabilil Shaidan ba.
Nana A’sha ta kasance tana da
kayayyaki na musamman da take
cabawa Manzon Allah ado dashi,
kamar yadda Manzon Allah yace
cikin ingantaccen hadisi: “ Duk
wanda Allah ya bashi gashi ya kula
dashi” Tirmizi cikin Shama’ilil
Muhammadiyya.
Zan rufe da Hadisin da ke cewa:
“INA JAWO HANKALINKU DA
SANYA TOZALIN ISMID LOKACIN
BARCI, DOMIN YANA KARA GANI
YANA KUMA TOFAR DA GASHI”
Leave a Reply