Rana ta biyu itace ranar Arfa,
Manzon Allah saw yace, Babu
wata rana da Allah yake yanta bayi
daga wuta, kamar ranar Arfa,
Muslum
A wani Hadisin yace: Mafi alkhairin
Addu’a itace Addu’ar ranar Arfa,
Attirmiziy,
Azumin ranar Arfa, yana kankare
zunubin shekarar data gabata, da
mai zuwa, Muslum, ( wannan ya
shafi, wadanada basu zo hajji ba )
abubuwan da akeyi ranar Arfa
1- Tasowa daga mina zuwa filin
Arfa
2- Gabatar da Hudubah, ga duk
musulmin duniya akan Tauhidi, da
hadin kai, da tattauna matsalolin
Musulmi
3- Yin Sallar Azahar da Laasar,
Kasaru da Jam’i, a lokacin Azahar
4- Shagala da addua, da zikiri, da
salati, yiwa Allah kirari, da
siffofinsa da sunayansa,
5- Har zuwa faduwar Rana, kafin
shirin tafiya zuwa filin Muzdalifah,
domin gabatar da Sallar magariba
da Ishah, a kwana zuwa ranar
goma ga wata.
Muyi addua ta gari, Allah ya
daukaka musulunci da musulmi
Leave a Reply