LALLE ABUBAKAR MAI YAWAN DARAJOJI NE A GURIN ALLAH DA MANZONSA

Danna nan domin shiga karatu Online

By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo



Sayyidina Abubakar Bin Abi Quhaafah Allah Ya kara masa yarda Mutum ne mai yawan darajoji a gurin Allah da manzonSa; ga ma wasu siffofi da darajoji har guda biyar da manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya siffanta shi da su:-
1. Shi Abubakar Siddiqi ne; watau mai martabar waliyyan Allah ta biyu ne bayan martabar farko ta Annabci; kamar yadda Allah Ya jeranta wadannan martabobi hudu na waliyyanSa a cikin Suratun Nisaa’i aya ta 69 inda ya ce:-
((ومن يطع الله والرسول فأولئك مع الذين انعم الله عليهم من النبيين والصديقين والشهداء والصالحين وحسن أولئك رفيقا)).
Ma’ana: ((Kuma wadannan da suka yi da’a ga Allah da ManzonSa, to, wadannan suna tare da wadanda Allah Ya yi ni’ima a kansu, daga Annabawa, da Siddiqai, da Shahidai, da Salihai. Kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya)).
2. Shi Abubakar shi ne mutumin da Annabi ya fi son shi a cikin dukkan Mazaje.
3. Shi Abubakar mutum ne da Annabi ya ba da umurnin a yi koyi da shi.
4. Shi Abubakar mutum ne da Allah Ya ‘yanta shi daga Wuta.
5. Shi Abubakar shi ne mutumin da yake shugabantar dukkan manya majiya karfi in banda Annabawa da Manzanni a cikin Aljannah.
Lalle banda wadannan darajoji biyar da muka ambata yanzu, akwai wasu darajojin daban.

Ga hujjar wadannan darajoji biyar na Babban Sahabi Abubakar da muka ambata daga ingantattun hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah:-
(1). Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3675, da Abu Dawud Hadithi na 4653, da Tirmiziy Hadithi na 3697, da Nasaa’iy Hadithi na 8079, da Ahmad Hadithi na 12127, da Ibnu Hibban Hadithi na 6865, da Bazzar Hadithi na 7094, da Dabaraaniy Hadithi na 144, da Abu Ya’alaa Hadithi na 2910, da Abdur Razzaq Hadithi na 20401 daga Sahabi Uthman Bin Affan, da Sahabi Anas Bin Malik Allah Ya kara musu yarda sun ce:-
((ان النبي صلى الله عليه وسلم صعد احدا وأبو بكر وعمر وعثمان فرجف بهم، فقال: اثبت احد فانما عليك نبي وصديق وشهيدان)).
Ma’ana: ((Lalle Annabi mai tsira da amincin Allah ya hau (dutsen) Uhudu tare da Abubakar da Umar da Uthman, sai ya (dutsen) ya girgiza, sai ya ce: Uhudu ka nitsu ba wasu ba ne a kanka in banda wani Annabi, da wani Siddiqi, da wasu Shahidai biyu)).
(2). Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 4379, ma Muslim Hadithi na 2384, da Tirmiziy Hadithi na 3885, da Nasaa’iy Hadithi na 8052, da Ibnu Majah Hadithi ne 101, da Ahmad Hadithi na 17844, da Hakim Hadithi na 6740, da Ibnu Hibban Hadithi na 6885, da Dabaraaniy Hadithi na 18644, da Baihaqiy Hadithi na 12879 daga Sahabi Anas Bin Malik, da Sahabi Amr Bin A’as Allah Ya kara musu yarda suka ce:-
((ان النبي صلى الله عليه وسلم سيل اَي الناس أحب إليك؟ قال: عايشة. فقيل له: من الرجال؟ قال: ابوها)).
Ma’ana: ((Lalle an tambayi Annabi mai tsira da amincin Allah: wanene ne daga cikin mutane ya fi soyuwa a gare ka? Sai ya ce: A’isha. Sai aka ce da shi: daga cikin Maza fa? Sai ya ce: Mahaifinta)).
(3). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3662, da Ahmad Hadithi na 23293, da Hakim Hadithi na 4451, da Dabaraaniy Hadithi na 8344, da Bazzar Hadithi na 2827, da Baihaqiy Hadithi na 10348 daga Sahabi Abdullahi Bin Mas’ud, da Sahabi Huzaifah Allah Ya kara musu yarda sun ce:-
((قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: اقتدوا باللذين من بعدي ابي بكر وعمر)).
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Ku yi koyi da Wadannan biyun a bayana: Abubakar da Umar)).
(4). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3679, da Hakim Hadithi na 3557, da Ibnu Hibban Hadithi na 6864 daga Sahabiya uwar Muminai A’isha, da Sahabi Az-Zubair Bin Awwam Allah Ya kara musu yarda suka ce:-
((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم قال لابي بكر: انت عتيق الله من النار)).
Ma’ana: ((Lalle manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce wa Abubakar: Kai ne ‘yantaccen Allah daga Wuta)).
(5). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3665, da Ibnu Majah Hadithi na 95, da Ahmad Hadithi na 603, da Ibnu Hibban Hadithi na 6904, da Bazzar Hadithi na 490, da Dabaraaniy Hadithi na 17717, da Abu Ya’alaa Hadithi na 624 daga Sahabi Aliyyu Bin Dalib, da Sahabi Anas Bin Malik, da Sahabi Abdullahi Bin Abbas Allah Ya kara musu yarda sun ce:-
((ان النبي صلى الله عليه وسلم قال: ابو بكر وعمر سيدا كهول اهل الجنة من الاولين والاخرين الا النبيين والمرسلين)).
Ma’ana: ((Lalle Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: Abubakar da Umar shugabanni ne na manya majiya karfi na Aljannah tun na farkonsu har na karshensu amma banda Annabawa da Manzanni)).
Lalle wannan shi ne matsayin Sahabi Abubakar a idanun Shari’ar Musulunci. Kuma lalle ‘yan bidi’ar da suka maida ginshikin addininsu shi ne zagin shi da la’antar shi sun tabe. Allah Ya taimake mu Ya raba mu da sharrin bidi’ah. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates