LITTAFAN SHI’A SUN TABBATAR
DA AUREN SAYYADI UMAR DAN
KHATTABI (RADHIYALLAHU
ANHU) DA UMMU KULTHUM
‘YAR GIDAN SAYYADI ALI
(RADHIYALLAHU ANHU) KUMA
DIYAR NANA FATIMA KANWAR
HASAN DA HUSAIN (ALLAH YA
DADA YARDA DA SU BAKI DAYA)
:
1. Ya’aqubi a cikin Tarihinsa
(2/149-150) ya ce:
ﻭﻓﻲ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺧﻄﺐ ﻋﻤﺮ ﺇﻟﻰ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ
ﻃﺎﻟﺐ ﺃﻡ ﻛﻠﺜﻮﻡ ﺑﻨﺖ ﻋﻠﻲ ﻭﺍﻣﻬﺎ ﻓﺎﻃﻤﺔ ﺑﻨﺖ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻓﻘﺎﻝ ﻋﻠﻲ : ﺇﻧﻬﺎ ﺻﻐﻴﺮﻩ
ﻓﻘﺎﻝ ﻋﻤﺮ : ﺇﻧﻲ ﻟﻢ ﺃﺭﺩ ﺣﻴﺚ ﺫﻫﺒﺖ ، ﻟﻜﻨﻨﻲ
ﺳﻤﻌﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ :
ﻛﻞ ﻧﺴﺐ ﻭﺳﺒﺐ ﻳﻨﻘﻄﻊ ﺇﻻ ﻧﺴﺒﻲ ﻭﺻﻬﺮﻱ .
ﻓﺄﺭﺩﺕ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻲ ﺳﺒﺐ ﻭﺻﻬﺮ ﺑﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺘﺰﻭﺟﻬﺎ ﻭﺃﻣﻬﺮﻫﺎ ﻋﺸﺮﺓ
ﺁﻻﻑ ﺩﻳﻨﺎﺭ )
“A cikin wannan shekarar ne Umar
ya nemi auren Ummu Kulthum
diyar Ali dan Abu Talib daga wurin
sa. Kuma ita diyar Fatima ce ‘yar
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Sai Ali ya ce, ai ta yi
karama. Sai Umar ya ce, ai ni ba
wannan nake nufi ba. Na ji
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yana cewa: “Duk wata
dangantaka ranar alkiyama zata
yanke sai dangantakata da
surukutata. Shi ya sa na so in
samu dalili da surukuta da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
Sai Umar ya aure ta, ya kuma ba ta
sadaki Dinari dubu goma”.
2. Labarin wannan aure dai ya
tabbata har a cikin manyan
Sahihan littafan Shi’a kamar Al-Kafi
da Bihar Al-anwar da Istibsar dss.
Misali, a cikin Kafi (Al- Furu’
6/115-116) ruwaya ta zo daga
Sulaiman bin Khalid ya ce, na
tambayi Abu Abdillah (AS) idan
namiji ya mutu a ina ne matarsa
zata yi idda; a gidan mijin nata, ko
a duk inda ta ga dama? Sai ya ce:
Duk inda ta ga dama. Domin
lokacin da Umar ya mutu Ali (AS)
ya zo wurin Ummu Kulthum ya rika
hannunta, ya kuma tafi da ita
gidansa.
Wannan ruwaya akwai ta a cikin
Al-Istibsar na babban Shehin
Shaihunan Shi’ah At-Tusi
(Abwabul Iddah, Bab al mutawaffa
anha zaujuha 3/353).
3. Ba auren ba ma, har haifuwar da
ke tsakaninsu littafan Shi’a sun
tabbatar da ita.
Ya zo a cikin littafin da muka
ambata na Tusi (Kitabul Mirath,
Bab al Garqa wal mahdum 9/292)
Imamin ‘yan Shi’a na shida Ja’afar
(AS) ya karbo daga mahaifinsa;
Imami na biyar Muhammad bin Ali
bin Al- Husain (AS) cewa: “Ummu
kulthum da danta Zaid bin Umar
bin Al-Khattab sun rasu a lokaci
daya, ba a san wanda ya riga wani
mutuwa ba. Don haka an yi masu
sallah a tare amma ba a gadar da
dayansu daga daya ba”.
4. Ba zai yiwu mu lisafce duk
wadanda suka tabbatar da wannan
aure ba daga cikin malaman Shi’a
a littafansu. Amma zamu bada
sunayen wasu daga cikinsu da
littafansu don mai neman karin
nazari:
– Babban malamin Shi’a As-Sayyid
Alam Al-Huda a littafansa “Al-
Shafi” da kuma “Tanzih Al-
Anbiya”.
– Ibn Shahr Aashub a littafinsa
“Manaqib Ali Abi Talib”
– Arbili a littafinsa “Kashf Al-
Gummah Fi Ma’rifat Al-aimmah”
– Ibn Abil Hadid a sharhinsa a kan
“Nahj Al-Balagah”
– Al-Qadi Nurullah Al-Shaushatri
“As-Shahid As-Salis” a littafinsa
“Majalis Al-Mu’mineen”
– Ni’imatullah Al-Jaza’iri a littafinsa
“Al-Anwar An-Nu’maniyyah” dss.
Tambaya da ta zama tilas mu yi ga
‘yan Shi’a:
Me ye matsalar da ke damun ku?
Labari ya tabbata mutawatiri a
littafanku amma sai ku murza hanci
ku ce sam, karya ne. Surukuta da
Umar laifi ce manzon Allah ya auri
‘yarsa?
Duk surukan manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam) ba ku bar kowa ba sai
guda daya. Da gaske ne kuna son
sa kuwa? Kun yarda da abinda ya
yarda da shi ko dai kuna fushi da
fushin wasu ne (Majusawa
makiyan manzon Allah)?
Babu shakka wannan aure yana
ruguza duk karairayin da kuka kitsa
daon nuna gaba da adawa a
tsakanin gidajen biyu da kuma
nuna cewa halifancin ma
kwacensa ne almajiran manzon
Allah suka taru suka yi daga wurin
wasiyyinsa.
Leave a Reply