TAMBAYA:
Idan mace ta ga mijinta ya fara
gajiya da ita, shin za ta iya zuwa
wurin ‘yan duba ko ‘yan tsibbu
domin a karkato mata da
hankalinsa?
AMSA:
Bai halatta ga mace Musulma,
Mumina, don wani abu na damuwa
ya same ta, ta je wurin boka ko
dan tsibbu ba, domin yin haka
sabawa Allah da Manzonsa
sallallahu alaihi wa sallam ne.
Babu wanda yake yayewa wani
bakin ciki ko ya sanya shi farin ciki
ko ya kimsa kauna ko kiyayya a
zuciyar bawa sai Allah, idan ma
har wani boka ko dan tsibbu ya yi
surkullensa sai abin ya yiwu, to,
jarraba ce daga Allah kuma
wannan abin ba zai dauwama ba.
Don haka, idan kika ga miji ya
canja daga yadda kika san shi, sai
ki duba halayen da za ki yi don ki
jawo hankalinsa tare da yin
addu’a.
Wasu matan rashin gyaran jiki da
almubazzaranci ko barnar
kayayyaki, ko rashin kula da
tsabtar ‘ya’ya da rashin kula da
tarbiyyarsu, ko tsananin kishi, ko
rashin iya abinci, ko rashin iya
magana mai dadi, ko tinkaho da
iyayenta ko `yan’uwanta a kan
mijinta da sauran munanan dabi’u,
su sukan sa miji ya ji ya gaji da
mace. Kai galibi ma wadannan
halaye, su ne suke jawo rashin
jituwar da takan kai har ga saki,
don haka sai ta yi kokari ta gyara
halayen ta domin shi miji ana jawo
hankalin sa ne da halayen kirki da
maganganu masu dadi; A tarbe shi
da murmushi da farin ciki idan ya
shigo, a yi tarayya da shi wurin
farin ciki, yayin da abin farin ciki ya
same shi. Haka kuma a yi tarayya
da shi a bacin rai, yayin da abin
bakin ciki ya same shi.
Mu yi nazarin rayuwar Nana
Khadija ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ mana, irin
yadda ta kasance tana nuna
damuwarta yayin da wani abu ya
sami mijinta, misali, lokacin da
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallam ya zo mata yana rawar dari,
yana cewa ta lullube shi, ta lullube
shi. Nana Khadija ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta
tare shi tana lallashin sa, tana
nuna masa ba wani abin damuwa
ba ne, ta ce masa:
… ﻛﻼ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﻳﺨﺰﻳﻚ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺑﺪﺍ…
Ma’ana:
… Ba haka abin yake ba. Wallahi
Allah ba zai tabar da kai ko ya
tozartar da kai ba har abada …
Haka ya kamata mace ta gari ta
kasance.
Amma maganar zuwa wurin boka
ko dan tsibbu kuwa, wannan
haramun ne, domin hadisi ya
tabbata a cikin Musnad na Imam
Ahmad da Sahih Muslim cewa:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallam ya ce:
ﻣﻦ ﺃﺗﻰ ﻋﺮﺍﻓﺎ ﻓﺼﺪﻗﻪ ﺑﻤﺎ ﻳﻘﻮﻝ ﻟﻢ ﻳﻘﺒﻞ ﻟﻪ ﺻﻼﺓ
ﺃﺭﺑﻌﻴﻦ ﻳﻮﻣﺎ
Ma’ana:
Wanda duk ya je wurin boka (ko
dan tsibbu), ya tambaye shi game
da wani abu kuma ya gaskata abin
da (boka ko dan tsibbun) ya fada,
Allah ba zai karbi sallarsa ta kwana
arba’in ba.
TAMBAYA:
Shin ya halatta mace ta yi amfani
da magani don jawo hankalin
mijinta?
AMSA:
Duk abin da mace za ta yi amfani
da shi don jawo hankalin mijinta
wanda zai kyautata
zamantakewarsu, ba laifi ba ne,
matukar bai sabawa shari’ar
Musulunci ba, kuma ba zai illatar
da lafiyarta ko ta mijinta ba. Ko da
yake likitoci a asibitoci suna
fadakarwa a kan cewa mafi yawan
wadannan magungunan da mata
suke amfani da su, suna cutarwa,
don haka kada. mace ta yi amfani
da wani magani face wanda likitoci
ko malaman lafiya suka tabbatar
da ingancinsa.
TAMBAYA:
Wadanne irin kawaye ya kamata
mace ta yi kawance da su?
AMSA:
Ya kamata mace ta zabi kawaye
wadanda suka samu tarbiyya ta
addini da halaye na gari kuma
masu mutunci da amana,
musamman yayin ba da shawara
da sauransu. Saboda wasu
kawayen kan cutar da ‘yan uwansu
wurin ba su gurguwar shawara,
wadda za ta iya jawo sabani
tsakaninsu, ko kuma ta fitar da ita
daga ni’imar da take ciki a gidan
auren ta don hassada. Haka kuma
wasu kawayensu su ne suke yin
jagoranci wurin zuwa ga bokaye
da ‘yan tsibbu, wasuma, su ne kan
koya wa kawayensu munanan
dabi’u, kamar madigo da abin da
ya yi kama da haka. Don haka sai
a yi hattara, Allah ya kiyaye mu,
amin.
Leave a Reply