Mas'alolin aure Fitowa ta 29(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Ci gaban hakkokin maza akan
matayen su;
7- Yana daga cikin hakkokin miji a
kan matarsa, ta rika yi masa
kyakkyawan zato. Domin
mummunan zato shi ne yake kawo
rashin zamantakewa ta gari sau da
yawa, zafin kishi kansa mafi.
yawan mata su rika yi wa
mazajensu kage, musamman
lokacin da aka yi niyyar yi musu
kishiya, ba tare da sun yi la’akari
da cewa wannan kage-kagen kan
iya shafar mutuncinsu da na
mazajensu da ma na ‘ya’yan da
suka haifa ba.
8- Yana daga cikin hakkokin miji a
kan matarsa, ta kudurce cewa
rayuwarsu ta aure zama ne na
ibada da rayuwa ta dindindin
wadda babu wanda ya san
iyakarta sai Allah. Don haka bai
dace ba mace ta rika jin cewa
koyaushe ta yi nufin kawo karshen
auren ta da mijinta, za ta iya. Ko
kuma ta rika jin cewa ko badade ko
bajima za su rabu da mijinta.
Domin Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallam ya ce:
ﺃﻳﻤﺎ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﺳﺄﻟﺖ ﺯﻭﺟﻬﺎ ﺍﻟﻄﻼﻕ ﻓﻲ ﻏﻴﺮ ﻣﺎ ﺑﺄﺱ
ﻓﺤﺮﺍﻡ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺭﻳﺢ ﺍﻟﺠﻨﺔ
Ma’ana:
Duk macen da ta nemi saki daga
wurin mijinta, ba tare da wani dalili
(ko cutarwa) ba, to, jin kanshin
aljanna ya haramta a gare ta.
A nan muke jan kunnen matan da
Allah ya ba su wata siffa ta kyau ko
daukaka ta ilimi ko matsayi na aiki,
ko na asali da su daina raina
mazajensu ko neman saki, ba tare
da wata cutarwa ba.
9- Yana daga cikin hakkokinin miji
a kan matarsa, kyautata
mu’amalarta da danginsa da
‘ya’yansa da kishiyarta. Domin
wasu matan musamman amare
wadanda ba su fara haihuwa ba,
mijinsu kawai suka sani, ba sa
damuwa da kyautata mu’amala
tsakaninsu da dangin mijinsu ko
‘ya’yan kishiyarsu. Wannan kuwa
kan haifar da adawa tsakaninta da
mijinta, wani lokacin ma har ta kai
ga rabuwa. Babu kuwa yadda za a
yi ki ce kina son miji, amma ba ki
son `ya`yansa. Sai dai idan
wannan son, ba na gaskiya ba ne.
10- Yana daga cikin hakkokin miji
a kan matarsa, yarda da abin da ya
kawo mata komai kankantarsa. Bai
kamata ta kallafa masa abin da ba
zai iya ba. Domin wadansu matan
sukan kalli irin wadatar da Allah ya
yi wa kawayensu, don haka sai su
dorawa mijinsu abin da ba shi da
karfin yi, su ce dole sai ya yi musu.
Ya kamata mace ta zama mai
godiya ga Allah kuma mai godiya
ga mijinta dangane da irin alherin
da yake yi mata da tsayuwa a kan
rayuwarta. Kada ta zama butulu,
mai butulci ga mijinta. Domin
hadisi ya tabbata daga Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallam ya
ce:
…ﻭﺃﺭﻳﺖ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﻓﻠﻢ ﺃﺭ ﻣﻨﻈﺮﺍ ﻛﺎﻟﻴﻮﻡ ﻗﻂ ﺃﻓﻈﻊ
ﻭﺭﺃﻳﺖ ﺃﻛﺜﺮ ﺃﻫﻠﻬﺎ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ . ( ﻗﺎﻟﻮﺍ ﺑﻢ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ؟ ﻗﺎﻝ ) ﺑﻜﻔﺮﻫﻦ . ( ﻗﻴﻞ ﻳﻜﻔﺮﻥ ﺑﺎﻟﻠﻪ ؟ . ﻗﺎﻝ
) ﻳﻜﻔﺮﻥ ﺍﻟﻌﺸﻴﺮ ﻭﻳﻜﻔﺮﻥ ﺍﻹﺣﺴﺎﻥ ﻟﻮ ﺃﺣﺴﻨﺖ ﺇﻟﻰ
ﺃﺣﺪﺍﻫﻦ ﺍﻟﺪﻫﺮ ﻛﻠﻪ ﺛﻢ ﺭﺃﺕ ﻣﻨﻚ ﺷﻴﺌﺎ ﻗﺎﻟﺖ ﻣﺎ
ﺭﺃﻳﺖ ﻣﻨﻚ ﺧﻴﺮﺍ ﻗﻂ )
Ma’ana:
…An nuna mini wuta a yau. Ban
taba ganin abu mai firgitarwa
kamar ta ba. Sai na ga mafi yawan
mutanen cikinta mata ne. Sai
Sahabbai suka ce: Mene ne ya
sanya haka ya Ma’aikin Allah
sallallahu alaihi wa sallam ? Sai ya
ce : saboda kafircewarsu. Sai suka
ce : Suna kafirce wa Allah ne? Sai
ya ce : A a! Suna butulcewa
mazajensu kuma suna butulce wa
kyautatawar da suke yi musu. Da
za ka kyautatawa daya daga
cikinsu shekara aru-aru, sannan
daga baya ta ga wani abu da ba ta
so a gare ka, sai ta ce ban taba
ganin alheri tare da kai ba.
11- Yana daga hakkiin miji a kan
matarsa, yin idda yayin da ya sake
ta da kuma yin takaba yayin da ya
rasu, ya bar ta. Wadannan
abubuwa guda biyu hakkoki ne na
Allah domin shi ne ya yi umarni da
yin su, sannan kuma hakkin miji ne
domin tabbatar da kubutar mahaifa
daga juna-biyu saboda idan aka
samu da hakkin kula da shi yana
kan mijinta.
12- Yana daga cikin hakkin miji a
kan matarsa, barin yin abin da zai
fusatar da shi. Domin yin hakan
yakan gurbata kyakkyawar
zamantakewar da ke tsakaninsu.
Wasu matan idan suna son su
fusatar da mijinsu ko su bakanta
masa, sai su zagi `ya`yansa a
gabansa (suna nufin shi suke zagi)
ko su nemi hakkinsu daga gare shi
a lokacin da ba shi da shi, ko
lokacin da yake cikin wani hali na
damuwa, domin su tayar masa da
hankali. Wannan bai kamata ba.
Muna kira ga mata da su ji tsoron
Allah, su kiyaye hakkin da Allah ya
dora musu dangane da
mazajensu, kamar yadda muke
kira ga su ma mazan da su ji
tsoron Allah, su kiyaye hakkoin da
Allah ya dora musu dangane da
matansu.
JAN HANKALI
Dukkanin bayanin da muka
gabatar na mace ta yi wa mijinta
biyayya ko kuma shi ya sauke
nauyin da yake kansa, ya shafi
abin da bai sabawa Allah ba ne
kawai. Amma matukar abu ya
sabawa umarnin Allah da
Manzonsa sallallahu alaihi wa
sallama , to, babu biyayya a kai.
Misali a nan shi ne;
i- ARON MACE: Yana daga cikin
munanan dabi’u na jahiliyyar farko,
bayar da aron mace. Mutum kan
tura matarsa ga wani jarumin
barde yayin da ta gama jinin
al’ada, domin ya rika saduwa da ita
har ta yi ciki, sannan ta dawo gidan
mijinta domin wai ta haifa masa da
wanda yake jarumi. Amma
jahiliyyar karni na 21 (wannan
zamani namu) har ta fi ta wancan
zamanin muni. Domin a yanzu har
canjin mace ake yi tsakanin abokai
ma’aurata. Sai mutum ya tura
matarsa gurin abokinsa, shi ma
abokin ya turo masa tasa domin su
rika yin lalata da junansu. Wannan
mummunar dabi’ar a da can muna
jin ta ne kawai a tsakanin `yan
Shi’a al-Imamiyya al-Isna
Ashariyya da gurbatattun `yan
boko. Amma yanzu tana nema ta
zama ruwan dare a tsakanin
al’umma. Saboda haka bai hallatta
mace ta yi wa mijinta biyayya a
kan irin wannan mummunar dabi’a
ba.
ii- TARAWA DA MACE TA
DUBURA: Wasu mazajen kan
tirsasa wa matansu wurin yin
luwadi da su, musamman ma ‘yan
mata wadanda ba su gama
fahimtar rayuwar aure ba. Wasu
ma har yaudarar matan suke yi su
janyo masu ayar Suratul Bakara da
take cewa:
… ﻧﺴﺎﺅﻛﻢ ﺣﺮﺙ ﻟﻜﻢ ﻓﺄﺗﻮﺍ ﺣﺮﺛﻜﻢ ﺃﻧﻰ ﺷﺌﺘﻢ…
ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ 223 :
Ma’ana:
Matanku gonakinku ne, to, ku zo
wa gonakinku ta inda kuke so…
Sai su fassara masu ita da cewa ko
ta dubura aka sadu ba komai. Don
haka bai kamata mace ta yi wa
mijinta biyayya a irin wannan hali
ba. Domin hadisi ya tabbata daga
Abu Huraira radhiyallahu anhu ya
ce: Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallam ya ce:
ﻣﻠﻌﻮﻥ ﻣﻦ ﺃﺗﻰ ﺍﻣﺮﺃﺗﻪ ﻓﻰ ﺩﺑﺮﻫﺎ
Ma’ana:
Wanda ya tara da matarsa ta baya
(dubura) tsinanne ne.
iii -MADIGO TSAKANIN MATA:
Wasu matan sukan yi amfani da
‘yan mata kanana ko kawayensu
domin biyan bukatar junansu,
saboda suna ganin sun fi karfin
mazajensu. Bai kamata mijin da ya
san matarsa tana da irin wannan
mummunar dabi’ar, ya zuba mata
ido ba. Domin shi ne yake da iko a
kanta, kuma Allah zai tambaye shi
game da ita.
Allah ya shirye mu baki daya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Mas'alolin aure Fitowa ta 29(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. Mohammad Danjuma Bobbo Avatar
    Mohammad Danjuma Bobbo

    Allah yakara bamu fahita akan wanda kuka rubuta ku ma muka karanta amin.

Leave a Reply

Latest updates
Categories