Mas'alolin aure Fitowa ta 27(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ci gaban bayani na (2) akan
hakkokin mata:
10- Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, yayin da wata
tafiya ta kama shi, ya tafi da ita
matukar yana da ikon yin hakan,
idan kuma ba shi da iko, wajibi ne
ya bar mata abin da za ta ci, ta
sha. Idan kuma matan sun fi daya
kuma tafiyar ta kama a yi da daya
daga cikin su, sai a yi kuri’a a
tsakaninsu.
Abin takaici ne kwarai yadda za ka
ga mutum ya tafi ya bar iyalinsa da
sunan neman arziki har tsawon
lokaci, ba kuma zai bar musu wani
abu ba, har ka ga iyalinsa sun
tagayyara sun shiga wani
mawuyacin hali, wani lokaci ma
har ta kai su ga yin bara ko sayar
da mutuncinsu domin samun abin
da za su sa a bakinsu. Ya kamata
mu ji tsoron Allah, mu kiyaye
dokokin da ya shinfida mana.
11- Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, dauke mata
kewa musamman wurin yin raha
da ita. Domin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama yakan
yi raha da iyalinsa. Misalin haka
shi ne irin tseren da ya yi da Nana
A’isha ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ kamar yadda ya
tabbata a hadisin da Imam Ahmad
ya rawaito cewa Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
cewa A’isha ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ:
ﺗﻌﺎﻟﻲ ﺃﺳﺎﺑﻘﻚ، ﻓﺘﺴﺒﻘﻪ، ﺛﻢ ﻳﺴﺎﺑﻘﻬﺎ ﺑﻌﺪ ﺃﻥ ﺑﺪﻧﺖ
ﻭﺣﻤﻠﺖ ﺍﻟﻠﺤﻢ ﻓﻴﺴﺒﻘﻬﺎ ﻭﻳﻀﺤﻚ ﻭﻳﻘﻮﻝ: ﻫﺬﻩ ﺑﺘﻠﻚ .
Ma’ana:
Zo mu yi tsere, sai ta tsere masa,
bayan ta yi nauyi, sai shi kuma ya
tsere mata, sai ya yi dariya ya ce:
wannan shi ne ramuwar wancan
(tsere mini din da kika yi).
Kuma ya tabbata daga Nana
A’isha ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
ﻛﻨﺖ ﺃﻟﻌﺐ ﺑﺎﻟﺒﻨﺎﺕ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻭﻛﺎﻥ ﻟﻲ ﺻﻮﺍﺣﺐ ﻳﻠﻌﺒﻦ ﻣﻌﻲ ﻓﻜﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺇﺫﺍ ﺩﺧﻞ ﻳﺘﻘﻤﻌﻦ ﻣﻨﻪ
ﻓﻴﺴﺮﺑﻬﻦ ﺇﻟﻲ ﻓﻴﻠﻌﺒﻦ ﻣﻌﻲ
Ma’ana:
Na kasance ina wasa da
kawayena a daki. Idan Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya shigo sai su gudu, su buya, shi
kuma sai ya bi su ya tattaro su,
yana cewa: ku zo ku yi wasanku.
Amma a yau, sai ka ga wasu
mazaje idan za su shiga
gidajensu, sai su shiga babu
sallama, babu raha, sai gyaran
murya, ko su dunguri kwano da
kafarsu, ko su yi ham da mota, ko
su rika kada mukulli wai don matan
su shiga taitayinsu, kuma su suna
ganin yin sallama ga matan zai iya
jawo raini tsakaninsu, alhalin su ba
su san yin sallamar shi ne zai jawo
sukuni da nutsuwa da soyayya da
aminci a cikin. gidajensu ba.
Kuma wani abin mamakin ma shi
ne yadda za ka ga mai irin wannan
halin idan yana hira da abokansa a
gidansa, za ka ji shi yana wasa da
dariya, amma da zarar abokan sun
tafi, kamar an dauke ruwa, sai ya
zamo mai fuskar shanu. Shi a
gurinsa, tattaunawa da raha da su,
zai iya jawo raini ya shiga
tsakaninsu. Irin wannan hali bai
dace ba, domin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama wanda
shi ne fiyayyen halitta yana raha da
sakin fuska ga iyalinsa, kuma
shiriyar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ita ce mafificiyar
shiriya. Allah ya yi mana muwafaka
amin.
12- Yana daga cikin hakkin mace a
kan mijinta, rashin bayyana
sirrinta, musamman a kan abin da
ya shafi kwanciya. Domin hadisi ya
tabbata daga Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
« ﺇﻥ ﻣﻦ ﺃﺷﺮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺰﻟﺔ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ
ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻳﻔﻀﻰ ﺇﻟﻰ ﺍﻣﺮﺃﺗﻪ ﻭﺗﻔﻀﻰ ﺇﻟﻴﻪ ﺛﻢ ﻳﻨﺸﺮ
ﺳﺮﻫﺎ ».
Ma’ana:
Yana daga cikin mafi sharrin
mutane a wurin Allah, ranar gobe
alkiyama, mutumin da zai sake da
matarsa, ko kuma ita ta sake da
shi, sannan ya je yana bayyana
sirrinta.
13- Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, kada ya tilasta
mata a kan tazarar haihuwa (wato
tsarin iyali) har sai ya nemi izininta.
Haka kuma haramun ne ya sadu
da ita alhali tana cikin jinin al’ada
ko biki. Amma wannan bai hana ya
ji dadi da ita ba ta fuskar yin
wasanni da debe kewa har su
samu biyan bukatarsu (a lokacin
jinin al’ada). Haka kuma ba shi da
hakkin ya sadu da ita ta baya
(dubura) kamar yadda wasu
mazaje suke yi.
14- Yana daga cikin hakkokinta har
ila yau, ba ta izini yayin da ta nemi
zuwa ziyarar iyayenta ko danginta,
domin sadar da zumunci. Saboda
matan Annabi sallallahu alaihi wa
sallama da sahabbansa da sauran
magabata na kwarai, sukan fita
domin yin ziyara, cikin sutura ta
mutunci da kamala. Haka kuma
idan suka nemi zuwa masallacin
Juma’a, ko idi, ko salloli biyar, bai
kamata a hana su ba, domin
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﻻ ﺗﻤﻨﻌﻮﺍ ﺇﻣﺂﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺴﺎﺟﺪ ﺍﻟﻠﻪ .
Ma’ana:
Kada ku hana bayin Allah mata
zuwa masallatan Allah.
Haka kuma hadisi ya tabbata daga
Jabir Ibn Abdullah radhiyallahu
anhu ya ce:
ﻃﻠﻘﺖ ﺧﺎﻟﺘﻰ ﻓﺄﺭﺍﺩﺕ ﺃﻥ ﺗﺠﺪ ﻧﺨﻠﻬﺎ ﻓﺰﺟﺮﻫﺎ ﺭﺟﻞ
ﺃﻥ ﺗﺨﺮﺝ ﻓﺄﺗﺖ ﺍﻟﻨﺒﻰ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻘﺎﻝ »
ﺑﻠﻰ ﻓﺠﺪﻯ ﻧﺨﻠﻚ ﻓﺈﻧﻚ ﻋﺴﻰ ﺃﻥ ﺗﺼﺪﻗﻰ ﺃﻭ ﺗﻔﻌﻠﻰ
ﻣﻌﺮﻭﻓﺎ .
Ma’ana:
An saki kanwar mahaifiyata (tana
cikin idda), sai ta fita za ta je
gonarta, domin ta tsinko dabino,
sai wani mutum ya tsawatar mata
game da fita, sai ta fadawa
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama, sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
Ki je ki tsinko dabinonki, domin
watakila za ki yi sadaka ko alheri a
cikinsa.
Hadisai da yawa sun nuna cewa,
mata kan nemi izinin mazajensu
domin ziyara mai ma’ana, ko sadar
da zumunci, ko raka amarya,
kamar yadda wannan hadisin ya
nuna, wannan matar tana cikin
idda, amma duk da haka ta fita ta
je gonarta. Haka kuma Imamul
Bukhari ya rawaito hadisi cewa:
ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ : ﺃﻧﻬﺎ ﺯﻓﺖ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﺇﻟﻰ
ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻓﻘﺎﻝ ﻧﺒﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ) ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻌﻜﻢ ﻟﻬﻮ ؟ ﻓﺈﻥ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
ﻳﻌﺠﺒﻬﻢ ﺍﻟﻠﻬﻮ )
Ma’ana:
Nana A’isha ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta raka
wata amarya mutuniyar Madina
zuwa gidan mijinta, sai Annabi
sallallahu alaihi wa sallama ya
tambaye ta, ya ce: Ya A’isha ‘Shin
wane irin nishadi da wakoki kuke yi
yayin raka amarya gidan mijinta?
Domin mutanen Madina suna son
nishadi da wakokin biki yayin raka
amarya.
Amma abin mamaki sai ka ga
wasu mazaje suna hana matansu
zuwa sada zumunci, ko da kuwa
iyayensu ne ko kuma danginsu,
bisa dogaro da wasu kissoshi da
ake jingina wa Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama
wadanda ba su da tushe, bare
asali. Kissar farko ita ce wadda ake
cewa wai fitar mace uku ce:
Fitowarta zuwa duniya (wato
haihuwarta).
Fitowarta zuwa gidan mijinta.
Fitowarta daga gidan miji zuwa
kabarinta.
Wannan kissar kage ce da karya
aka jingina wa shugaban talikai.
Domin matan Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama da
matan Sahabbai radhiyallahu anhu
sukan fita fiye da wannan fitar uku,
wannan ke tabbatar da rashin
ingancin wannan kissar. Hasali ma
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama yakan yi wa matansa
kuri’a idan zai yi tafiya zuwa wani
wuri. Kai, hatta a fagen yaki ma
Annabi sallallahu alaihi wa sallama
yakan tafi da matansa. Haka kuma
hadisan da suka gabata na cewa:
Nana A’isha ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta kan
raka amare zuwa gidan
mazajensu. Kuma wani hadisin da
ya tabbata cewa, Nana Asma’u
ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ takan yi tafiya ta
tsawon kimanin kilomita hudu
(wato farsaki biyu da rabi) domin yi
wa dokin mijinta ciyawa, da sauran
hadisan da suka tabbata, duka
suna nuna halaccin fitar mace. Don
haka wajibi ne miji ya bar iyalinsa
su sadar da zumuncinsu. Haka nan
idan mahaifi ko mahaifiya ba su da
lafiya, tilas ne ta je ta duba su.
Kissa ta biyu ita ce wadda ake
jingina ta ga Anas Ibn Malik
radhiyallahu anhu wai ya ce, wani
mutum a zamanin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya yi
wata tafiya kuma ya cewa matarsa
kada ta sauko daga benenta zuwa
kasa, alhali kuma babanta ya
kasance a kasan benen, sai baban
nata ya yi rashin lafiya, sai matar ta
aikawa Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama tana neman ya
ba ta izini ta sauko domin ta je ta
gaisar da mahaifinta. Wai sai
Annabi sallallahu alaihi wa sallama
ya ce da ita: Ki yi wa mijinki
biyayya. Yayin da mahaifin nata ya
rasu, sai ta kara neman izinin
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama sai ya ce: Ki yi wa mijinki
biyayya.’ Yayin da aka binne
mahaifin nata, sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya aika
mata cewa Allah ya gafartawa
mahaifinki saboda biyayyarki ga
mijinki. (Ita ma wannan kissar kage
ce da karya aka yi wa Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama,
ba ta tabbata ba).
Irin wadannan kissoshi suna da
yawa, don haka sai a yi hattara da
irin wadannan karairayi da ake
jingina su ga Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama.
Babu shakka akwai wadansu
matan da suka mayar da fita don
biyan wata bukatarsu, ba don sada
zumunci ba, suna yin amfani da
fitar don zuwa gidajen bokaye da
wuraren da ba su dace ba,
musamman irin taron nan da ake
haduwa tsakanin dangin ango da
na amarya ana kida da rawa, ana
lika masu kudi (Mother’s night)
wadansu ma ko hijabi babu.
Wadansu matan kuma suna
amfani da fitar dare da sunan za su
je wata ziyara, amma sai su buge
da zuwa ana daukar su, ana
fasikanci da su. Don haka muna
kira ga iyayenmu mata da
kannenmu da yayyenmu, da su
sani cewa duk abin da suka aikata
cin amana ne kuma za a yi masu
hisabi a kansa ranar alkiyama. Don
haka su nisanci irin wadannan
abubuwa.
15- Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, ya rika yi mata
kyakkyawan zato. Domin
mummunan zato shi ne yake kawo
rashin zaman lafiya da rigingimu a
cikin gida. Sai dai idan abin da
yake zaton ya bayyana, ko kuma
ya dogara da wata babbar hujja da
zai iya kafawa domin kare kansa
da ita, a nan duniya da kuma ranar
gobe alkiyama. Domin hadisi ya
tabbata daga Jabir Ibn Abdullah
radhiyallahu anhu yayin da suka
dawo daga wani yaki, sai Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce musu:
( ﺍﻣﻬﻠﻮﺍ ﺣﺘﻰ ﺗﺪﺧﻠﻮﺍ ﻟﻴﻼ – ﺃﻱ ﻋﺸﺎﺀ – ﻟﻜﻲ
ﺗﻤﺘﺸﻂ ﺍﻟﺸﻌﺜﺔ ﻭﺗﺴﺘﺤﺪ ﺍﻟﻤﻐﻴﺒﺔ )
Ma’ana:
Ku saurara ku shiga da isha, domin
wacce kanta babu gyara ta taje,
wacce kuma mijinta ya dade baya
nan ta gyara jikinta.
16- Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, duk lokacin da
ya yi wata tafiya, kada ya dawo
mata da daddare, yana da kyau ya
sanar da ita cewa ga shi nan tafe.
Domin hadisi ya tabbata daga
Jabir Ibn Abdullah radhiyallahu
anhu ya ce:
ﻧﻬﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻥ ﻳﻄﺮﻕ
ﺍﻟﻤﺮﺀ ﺃﻫﻠﻪ ﻟﻴﻼ، ﺃﻭ ﻳﺨﻮﻧﻬﻢ ﻭﻳﻠﺘﻤﺲ ﻋﺜﺮﺍﺗﻬﻢ .
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya hana mutum ya zo wa
iyalinsa da dare (ba zato ba
tsammani) ko ya rika fakonsu
(domin ya kama su da laifi), ko.
kuma ya rika bin diddigin kura-
kuransu.
Kuma hadisi ya tabbata Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce:
ﺇﺫﺍ ﻃﺎﻝ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺍﻟﻐﻴﺒﺔ ﻓﻼ ﻳﻄﺮﻕ ﺃﻫﻠﻪ ﻟﻴﻼ .
Ma’ana:
Idan daya daga cikinku ya yi tafiya
ya dade bai dawo ba, kada ya
kwankwasa wa iyalinsa kofa da
dare (wato kada ya zo masu ba
zato ba tsammani).
Babban malamin nan Al-Hafiz Ibn
Hajar Rahimahullah, ya fada cewa:
Wannan hadisin yana kwadaitar da
ma’aurata, aikata abin da zai kara
dankon soyayya da kauna a
tsakaninsu. Hakika shari’ar
musulunci ta hana su bibiyar
al’aurar junansu duk da kuwa abin
da daya ya aikata ba zai buya ga
dan’uwansa ba. Haka kuma
wannan hadisin yana nuna cewa
ana son mace ta yi wa mijinta ado,
domin ado ba ya canja halittar
Allah. Abin fahimta a nan shi ne an
hana miji ya zo wa iyalinsa ba zato
ba tsammani don kada ya zo ya
tarar da su a cikin wani yanayin da
ransa ba zai so ba. Kuma har ila
yau, hadisin yana nuna mana
cewa shari’ar musulunci ta hana
mu yin abin da zai jawo
mummunan zato a tsakaninmu.
A takaice dai abin fahimta game da
wannan hadisin shi ne an hana
mutum ya dawowa iyalinsa
bagatatan, domin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama yakan
dawo gida daga tafiya lokacin
walaha (wato da hantsi) kuma
yakan sanar da su kafin ya iso.
Don haka tunda yanzu lokaci ne na
wayar salula (cellular phones), ya
kamata ya sanar da su kafin ya iso,
domin yin hakan zai kawar da
wadannan illoli idan Allah ya
yarda.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Mas'alolin aure Fitowa ta 27(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. Anas ibn ibrahim Avatar

    Assalamu,alaikum malam don allah inada tambaya menene hukuncin wanda akasamusu rana da budurwar bayan ansamusu rana dagabaya sai yakama xinada ita malam to yawannan auren xaikasance akwai wannan auren ko babu?daga anas ibn ibrahim tela dake nan banxaxxau

Leave a Reply

Categories
Latest updates