Mas'alolin aure Fitowa ta 26(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ci gaban bayani akan hakkokin
mata:
6- Kada miji ya kallafa wa matarsa
girke-girke wadanda ba za ta iya
ba, musamman a lokacin azumi
har ta kasa azumi ko ta kasa
samun sukunin gudanar da
ibadunta tsakaninta da
mahaliccinta. Sannan kuma yana
da kyau ya taimake ta a cikin
ayyukan gida gwargwadon iko.
Domin Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama shi ne fiyayyen
halitta, amma duk da haka yana
taimaka wa iyalansa a cikin
ayyukan gida kamar yadda hadisi
ya tabbata daga Nana A’isha ﺭﺿﻲ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
ﻛﺎﻥ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﻣﻬﻨﺔ ﺃﻫﻠﻪ ﻓﺈﺫﺍ
ﺳﻤﻊ ﺍﻵﺫﺍﻥ ﺧﺮﺝ
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya kasance yana cikin
hidimar iyalinsa (a cikin gida),
amma idan ya ji kiran Salla sai ya
fita (zuwa masallaci).
7- Yana daga cikin hakkokin mace
a kan mijinta, ya rika yin ado domin
ta. Saboda Abdullahi bin Abbas
radhiyallahu anhu yana cewa:
Nakan yi kwalliya domin matata (ta
gani) kamar yadda ni ma nake son
ta yi mini kwalliya, saboda Ubangiji
subhanahu wa ta’ala yana cewa:
… ﻭﻟﻬﻦ ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻬﻦ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ… ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ:
228
Ma’ana:
… Kuma (su mata) suna da hakki
(a kan mazajensu) kwatankwacin
irin wanda yake kansu (na
hakkokin mazajensu) bisa ga
kyautatawa…
Sannan ya guji amfani da
abubuwan da za su iya cutar da
ita, kamar cin tafarnuwa ko danyar
albasa ko shan taba da sauran
abubuwan da za su iya kawo warin
jiki.
8- Haka kuma yana daga cikin
hakkokin mace a kan mijinta, kula
da hakkinta wurin biyan bukatarta
ta ‘ya mace. Yana da kyau ya sani
cewa kamar yadda zai bukace ta ta
saurare shi, ita ma tana da hakkin
ta bukace shi ya saurare ta. Domin
haka dole ne ya saurare ta a
lokacin da ta bukace shi, sai dai
idan akwai wata larura da za ta iya
hana shi yin hakan.
9- Yana daga cikin hakkin mata a
kan mijinsu, yin adalci tsakaninsu
wurin rabon kwana, da girki da
tufatarwa da sauransu. Saboda
ana samun wasu azzuluman
magidanta idan suka tashi bayar
da kudin abinci ko cefane ko
bukatun gida, sai su tattara su
baiwa wadda aka fi so, duk wadda
take da wata bukata, sai ta biyo ta
kanta, wanda yin hakan zalunci ne.
Ya kamata kowacce mace ta zama
tana da hakkin tattaunawa da
mijinta kai tsaye yayin da duk wata
bukata ta taso mata ba tare da
wani ya yi mata shamaki ba.
JAN HANKALI
A nan muna son mu ja hankalin
al’umma da cewa dukkanin
hakkokin nan da muka ambata a
sama (kama daga ciyarwa da
tufatarwa da tsugunarwa) wajibi ne
a kula da su yayin da aka yi wa
mace saki daya ko biyu, kafin ta
gama idda, ko tana da ciki ko ba ta
da shi. Haka kuma, ko da saki uku
ne, idan tana da ciki, wajibi ne a ci
gaba da ba ta wadannan hakkoki
har ta haihu.
Babban abin takaici ne a yau irin
yadda ma’aurata suke yin watsi da
dokokin Allah, yayin da aka yi saki,
sai miji ya hana matar ta yi idda a
gidansa, ko kuma ita matar ta ki
zama, ko kuma danginta su zuga
ta ta bar gidan, ga shi kuma
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
ce:
… ﻟﺎ ﺗﺨﺮﺟﻮﻫﻦ ﻣﻦ ﺑﻴﻮﺗﻬﻦ ﻭﻟﺎ ﻳﺨﺮﺟﻦ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ
ﻳﺄﺗﻴﻦ ﺑﻔﺎﺣﺸﺔ ﻣﺒﻴﻨﺔ ﻭﺗﻠﻚ ﺣﺪﻭﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻦ ﻳﺘﻌﺪ
ﺣﺪﻭﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻘﺪ ﻇﻠﻢ ﻧﻔﺴﻪ ﻟﺎ ﺗﺪﺭﻱ ﻟﻌﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺤﺪﺙ
ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﺃﻣﺮﺍ (1) ﺍﻟﻄﻼﻕ 1 :
Ma’ana:
… Kada ku fitar da su (matan da
kuka saka) daga gidajensu, kuma
kada su fita, sai idan sun aikata
wata alfasha bayyananniya.
Wadancan iyakokin Allah ne, kuma
duk wanda ya ketare iyakokin
Allah, to, hakika ya zalunci kansa.
Ba ka sani ba mai yiwuwa ne Allah
ya farar da wani abu (na nadama
ko hakuri da taushin zuciya) bayan
wancan al’amari (na saki a dawo a
yi kome).

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates