Tambaya: idan mutum yayi buda baki sannan sai jirgi ya tashi tashi, sai yaga rana bata gama fadiwa ba, yaya hukuncin azuminsa?
Amsa: Wanda bayan yayi bude baki abisa lokacin da akeyi, sai kuma jirgi ya tashi dashi sai yaga rana, to wannan babu komai akansa azuminsa tayi kuma babu wani kame baki dazai sakeyi. Wannan itace fatawar Manyan Maluma: Ibn Uthaimeen, Ibn Baaz, Abdurrazaq Al-Afifi.
Tambaya: Shin mace zata iya shan maganin da zai dakatar mata da jinin Al’ada domin yin azumin ramadana cikakke?
Amsa: Babu laifi mace tayi amfani da wani magani domin ya jinkirta mata Al’ada zuwa har ta kammala Azumin Ramadan Amma sai in an Tabbatar da cewa : Wannan Magani baya cutarwa” inhar ya zamto yana cutarwa toh haramunne yin amfani dashi, Wannan shine Mazhabar Hanabila, Kuma Sheikh Ibn Baaz Yana da ra’ayi haka. Sai dai wasu maluma suna ganin Rashin yin amfani da wani magani don jinkirta haila yafi, sabida Mace ta tsaya a Dabi’an da Allah yayi ta akai shi yafi.
Tambaya: Meye hukuncin daukan jini domin yin Gwaji a Cikin watan Ramadan.
Amsa: Babu laifi mutum yaje a dauki jininsa domin yin gwaji acikin watan Ramadana. Domin bashi da wani tasiri kan azumi. Wannan shine fatawar sheikh Ibn Baaz Da Uthaimeen.
Tambaya: Shin yin Allura yana Karya Azumi?
Amsa: yin Allura baya karya azumi, sai dai in ya zamto wannan allura tana zama maimakon abinci. Amma allurar da akeyinta dun magani wannan babu laifi ayi amfani da ita. Wannan shine abinda Majma’ul Fiqhil Islami suka tafi akai, Haka Nan Sheikh Ibn Baaz Da Uthaimeen.
Reference: a duba littafin
تلاثون مسألة فقهية معاصرة عن الصوم.(إعداد قسم العلمي بمؤسسة الدرر السنية)
Leave a Reply