ME YA FARU A KARBALA 32(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Matsayin Malaman Sunna Game
Da Tawayen Mutanen Madina
Game da tawayen mutanen
Madina malamai magada
Annabawa ba su ja bakinsu ba
suka yi shiru lokacin da abin yake
faruwa. Sun bayyana ma mutane
abinda Allah ya wajabta na da’ar
shugaba ko da fasiki ne. Maslahar
da ke cikin wannan ita ce, kauce
ma abinda zai zubar da jinainan
jama’a da kawo tashin hankalin da
ba a san karshe ko iyakarsa ba.
Littafan Sunnah na hadisi da na
Akida a cike suke da wadannan
hadisan. Sheikh Abdus Salam bin
Barjis ya tattara su tare da
maganganun magabata a cikin
littafinsa MU’AMALATUL HUKKAM
FI DAU’IL KITAB WAS SUNNAH,
bugun Riyadh 1415H.
Abinda duniya take fama da shi a
yau ya zama sheda a aikace kan
ingancin wannan matsayi na
Ahlus-sunna wanda manzon Allah
(S) ya dora su a kan sa. Tun daga
rikicin Somalia bayan kawar da
Siyad Bare zuwa kawar da
Saddam da Bin Ali da Ghaddafi da
Mubarak dss a ina ne ba a yi
hasarar dubun dubatar jama’a
al’ummar manzon Allah ba? Kuma
wace irin nasara aka samu? Ko
wane irin ci gaba aka kawo? Ashe
duk ba a gwammace da an bar su
ba duk da zaluncinsu da
kangararsu?
Zamu kawo misalai biyu da za su
bayyana mana matsayin malaman
Sunnah a lokacin faruwar wannan
fitina ta juyin mulki a kan Yazid.
Ku dakace mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates