ME YA FARU A KARBALA 36(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Makokin Ashura
Juyayi da makokin Husaini babu
shakka wata bidi’a ce babba da
take da manufar ci gaba da tona
mikin da tuni wadanda suka yi shi
sun gamu da Allah ya hukunta su.
Da yana cikin addini a yi makokin
wani ai kuwa da an shar’anta ayi
na kakan Husaini wanda shi ne
fiyayyen talikai. In kuma sun ce ai
saboda an zalunce shi ne, to da shi
da mahaifinsa wa aka fi zalunta?
Shi ya yi fito na fito har ya samu
sa’ar halaka mutane 88 a cikin
masu fada da shi ya aika su zuwa
Jahannama a wurin kokarinsu na
kama shi, sannan shi ma suka
samu kashe shi bayan kama shi
din ya faskara. Amma shi
mahaifinsa kwanton bauna aka yi
masa yana hanyar tafiya masallaci
cikin duhun asuba aka kashe shi.
To, don Allah a tsakanin su biyun
wa aka fi zalunta? Kuma in
wannan ne dalilin yin makoki don
me da ba a yin na baban nasa?
Haka su ma Halifofi biyu da suka
gabaci Ali kowanensu yana
matsayin shugaban musulmi aka
kashe shi kuma a cikin birnin
manzon Allah mai alfarma. Idan
kuma sun ce don ya yi shahada ne
wajen kare addini, sai mu ce
wannan kam ai abin buki ne, in da
Shari’a zata amince da yin bukin.
Wane ne ba ya son ya samu
shahada? Sai a zauna ayi ta
kururuwa ana yanka jiki don wani
masoyinmu ya tafi aljanna? Kuma
da haka ne da shugaban Shahidai
Hamza baffan Manzon Allah ya fi
Husaini cancanta tunda shi ne
shugaban shuhada’u in ji manzon
Allah (S). In sun ce ai kisan na
wulakanci ne, to, ai kowa ya san
irin wulakancin da aka yi ma gawar
sayyidina Hamza, abinda ya
bakanta ran Manzon Allah matuka.
Amma duk da haka, masu hannu
ga wannan lamari na kisan sayyadi
Hamza (Wahshi da kuma Hindu)
duk sun tuba, kuma Annabi
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya karbi tubansu, ya bar
su da Allah idan tuba na gari suka
yi Allah ya sani. In ma ba haka ba
to, can su da Allah masanin gaibi,
mai gaggawar hisabi. Amma su
‘yan Shi’a har inda yau ke magana
suna nan suna cin zarafin
wadannan bayin Allah kamar su
suka fi manzon Allah jin zafin an
kashe ma sa baffa, ko kuma su sun
isa su shiga tsakanin Allah da
bayinsa su hana shi yin rahama a
gare su idan ya tashi yin haka.
Ita dai musiba idan ta sabka
umurnin Allah a gare mu shi ne mu
yi istirja’i (Suratul Baqarah:155-156
). Allah ya jikan babban malamin
Tabi’una; Rabee’u bin Khuthaim, a
lokacin da aka gaya masa an
kashe Husaini sai ya ce, sun kashe
shi? Aka ce masa, eh. Ya ce INNA
LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN.
Sannan ya karanta aya ta 46 a
Suratuz Zumar inda Allah ke cewa:
“Ka ce, Ya Allah! Mai kaga halittar
sammai da kasa, masanin fili da
boye, Kai ne ke hukunci a tsakanin
bayinka a cikin abinda suka
kasance suna saba wa juna a
cikinsa”. Bayan haka Malam
Rabee’u bai sake cewa uffan ba.
Duba AL AWASIM MINAL
QAWASIM na Al Qadi Abubakar
Ibnul Arabi Al Ishbili, shafi 131.
Alkur’ani ya fada mana cewa, Banu
Isra’ila sun yi ta kisan Annabawan
Allah. (Duba misali, Suratul
Baqara: 87 da kuma 91). In da
makoki Ibada ne don me da ba a
umurci Manzo Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya yi masu makoki
ba?
Ina ganin fa duk mun tafi da nisa
jama’a. Husaini dai kanen Al
Hasan ne. Kuma duk wata falala
da Allah ya ba su a tare ya ba su
ita. Idan har Al Hasan bai wuce
kanensa ba to, ba wani dalilin da
zai fifita Husainin a kan sa.
Sa’annan shi ma shahada ya samu
don an kulla makirci an sa masa
guba a abinci ya ci bai sani ba. Me
ya sa shi ba a nasa makoki?
Kai, don Allah ‘yan Shi’a ku fada
mana wa ya fara yin wannan
makokin? Wa ya ce ku sa bakaken
kaya? Wa ya ce ku shirya dirama?
Wa ya ce ku yanka jikinku da na
kananan yaranku? Ina kuka samu
irin wannan aiki a cikin addinin
manzon Allah (SAWW)?!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates