Abinda ya kamata Musulmi ya rinƙa tambar kansa a kullum shine: Meye dalilin halitta ta?
Meyasa Allah ya sanya ni a wannan duniya? shin ya sanya ni a wannan duniyar ne don na tara dukiya naji daɗi ko kuma akwai wani dalili na daban?
duk wani mai hankali ya kamata yayi wa kansa wannan tambaya, domin da ace wani mutum zai tashi ya bar garinsa ya tafi wani gari sai kwatsam wani ya tareshi ya tambaye shi me ya kawoka wannan gari? Sai yace masa gaskiya nima ban sani ba, da nan take wannan mutumi da yayi tambayar zai fara tunanin kodai wannan wanda ya tambaya ɗin bashi da cikakken hankali ne. Toh haka nan wanda yake acikin wannan duniya amma baisan haƙiƙanin abinda ya kawo shi ba akwai nau’i na rashin hankali a tattare dashi.
Domin sanin dalilin halittar mu da samar damu a ban ƙasa sai mu koma zuwa ga Al’qur’ani. Allah yace:
Ban halicci Aljanu da mutane ba face don su bauta min
Surah adh-dhariyat: ayah 56
wannan aya tayi bayani a fili game da dalilin halittar mu da kuma samuwarmu a ban ƙasa. Tambaya ta gaba shine shin munayin abinda Allah ya haliccemu don shi?
Matafiyi ne ya tashi daga Birnin kaduna zuwa birnin kano domin biyan wata buƙata tashi, bayan ya shiga mota sai yaji daɗin wannan mota bayan sun isa garin kano sai yaƙi sauƙa a wannan mota yace shi yaji daɗin mota bazai sauƙa ba sai dai mai motar yayi ta yawo dashi a cikin gari. Mai motan nan yayi yayi dashi ya sauƙa yaƙi sauƙa, sai ya ɗaukeshi ya ɗan zazzaga dashi domin ya samu ya ɗan kwantar masa da hankali ko zai sauƙa amma duk da haka sai yaƙi sauƙa, sai wannan mai mota ya haɗashi da ƴan sanda domin su sauƙar masa dashi a mota sukazo kuwa suka tambaye shi me ya kawoshi kano sai ya faɗa musu ya ma mance abinda ya kawoshi sabida zaƙin mota. anan take suka fitar dashi daga motar da ƙarfin tsiya mai mota yayi gaba da motarshi kuma ƴan sanda suka sanya dole sai wannan mutumi ya biya mai mota wani abu sabida ɓata masa lokaci da yayi da kuma sanya shi yawo dashi da yayi. Daga ƙarshe wannan mutumi bai samu yaje yayi buƙatar da ta kawoshi ba, sannan Kuɗin guzurin sa anan jikin mota ta ƙare.
To misalin wannan shine misalin mutumin da ya mance haƙiƙanin dalilin Halittar sa ya kama wani abu daban, yaƙi bauta wa Allah, ya cinye guzurin lahirarsa anan duniya, yana cikin Haka sai Allah ya turo mala’ikar mutuwa yazo ya ɗauki ransa, bazai ankara ba sai dai ya sami kansa a ƙabari.
shiyasa a kullum mu kula da duk abinda zai zamto shamaki ga barin samun lahira mai kyau, domin duk wani jin daɗi na duniya mai yanke wa ne. Kuma bashi bane ainahin abinda ya kawo mu duniyar. Duk wani abin jin daɗi da zamu samu a duniya wasila ce zuwa ga lahira, sai muyi amfani dashi domin cimma ainahin babban burinmu kamar yadda matafiyi zai shiga mota domin ya isar dashi garin da yakeso yaje, a lokacin da matafiyi ya riƙi zaƙin mota ya mance da garin da zaije da abinda ya fitar dashi toh haƙiƙa ya kauce hanya, kuma yana dab da faɗa wa ga halaka.
Allah yasa mudace
Leave a Reply