A wannan zamani namu da hanyoyin sadarwa suka yawaita, kuma suka zamto suna da sauƙin samu hakan ya ƙara janyo yawaitar labaran ƙarya wanda mutane suke yaɗa wa cikin Al’ummah. Wanda wannan ba ƙaramin babban laifi bane.
Addinin Musulunci ya haramta yaɗa labarai da mutum bashi da tabbas akai. Allah maɗaukakin sarki yace:
Yaku Wa’inda kukayi Imani idan Fasiƙi yazo muku da wani labari toh kuyi bincike
Suratul-Hujurat: Aya No 6
Wannan ayah a bayyane take kan cewa duk inda mutum yaji labari kada yayi saurin yaɗa shi har sai yayi bincike akai, koda ko labari ne na alheri. Musamman in labarin ta fito ne daga wanda ba’a sanshi ba, ko kuma wanda yake ba adali bane.
An rawaito daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
Ya ishe mutum laifi, ya rinƙa bada labarin duk abinda yaji
Abu dawud: 4992
Wannan hadisi yana hanamu yaɗa labarai ba tare da bincike ba. sannan koda munyi binciken mu duba mugani shin yaɗa ta akwai alheri? In babu toh sai mu barta a inda muka ganta.
Ya yan’uwa musani fa duk amfani da mukeyi da wannan Kafafe za’a tambaye mu akansa Ranar tashin Al Qiyama, domin haka mu kula da abinda muke yaɗa wa da kuma faɗi, Allah yasa mudace.
Leave a Reply