Ina kira ga ‘yan’uwa musulmai dasu kaurace wa wannan dabi’ah ta kallon fina finan tarihin musulunci wanda ake nuna sahabban annabi(Sallallahu alaihi wasallam) aciki. Ko kuma wasu Magabata masu daraja. Hakan yana da matukar hatsari sosai. Musamman ga yara. Ka kiyaye kada ka rinka barin yaranka suna kallon wa’innan fina finai. Domin yana da matukar tasiri azukatan mutane. Wanda inhar mutum ya kalli irin wa’innan film din toh aduk lokacin da yaji sunan wani sahabi toh hoton da zai rinka zuwa zuciyarsa shine hoton da ya kalla a wannan film din. Wanda wa’innan masu shirya fina finai irin shiga da sukeyi ta tsabawa ta sahabban da kuma surarsu baki daya… Malamanmu na wannan zamani sun nuna haramcinsa . Sai mu kiyaye. Allah kiyayemu.
Leave a Reply