Da yawa daga cikin wadanda suka zaba wa kansu sabanin shiriyar Manzon Allah cikin gudanar da addininsu suna ganin cewa: In har Idin Maulidi bidi’ah ne, to kuwa lalle Musabaka a kan haddar Alqur’ani Mai girma, ko haddar Hadithan Annabi masu daraja ko haddar wani ilmi na Musulunci su ma yin su bidi’ah ce!!!
*************************
A nan muna ganin cewa yawan nisantar wadannan mutane ga littattafan Shari’ah na maluman Musulunci ne ya sa ba su ma san cewa: Dukkan abin da halaccinsa ya tabbata ta yanyar Ijma’in Musulmi cikin wani zamani daga cikin zamuna, to dole ne ya zamanto daya daga cikin abubuwa uku:-
1- ko dai ya zamanto Mubaahi, watau abin da yin sa da rashin yin sa duk daya a idanun Shari’ah.
2- ko kuwa ya zamanto Mustahabbi, watau abin da in har ba a yi shi ba to ba a yi wani laifi ba, in kuma aka yi shi to ana da wani lada na musamman.
3- ko kuwa ya zamanto Waajibi, watau abin da in har ba a yi shi ba za a sami zunubi, in kuma an yi shi to an yi abin da Shari’ah ta tilasta yin shi.
******************************
shi kuwa Musabaka domin haddar Alqur’ani Mai girma abu ne da Maluman Sunnah, da su kansu masu bidi’ah na Duniya suka hadu a kan halaccinsa a bisa hujjar kiyasin shi a kan Musaabakokin da Nassi ya zo da halaccinsu. In kuwa haka lamarin yake, to ta kaka ne za a hada hukuncin Musaabaka domin haddar Alqur’ani da hukuncin Idin Maulidin da babu mai yin shi ko halatta shi in banda wasu daga cikin masu yin bidi’ah??
*********************
HUKUNCIN MUSABAKA:
1. Imam Ibnu Qudaamah mai rasuwa a shekara ta 620 watau da mutuwarsa yau shekaru 815 ke nan, ya ce cikin littafinsa mai suna Almugnii 13/404-405 :-
{لمسابقة جائزة بالسنة والاجماع، اما السنة فروى ابن عمر ان النبي صلى الله عليه وسلم سابق بين الخيل المضمرة من الحفياء الى ثنية الوداع، وبين التي لم تضمر من ثنية الوداع الى مسجد بني زريق. متفق عليه… واجمع المسلمون على جواز المسابقة في الجملة. والمسابقة على ضربين: مسابقة بغير عوض، ومسابقة بعوض. فالمسابقة بغير عوض فتجوز مطلقا من غير تقييد بشيء معين، كالمسابقة على الاقدام، والسفن، والطيور، والبغال، والحمر، والمزاريق، والمصارعة، ورفع الحجر ليعرف الاشد، وغير ذلك؛ لان النبي صلى الله عليه وسلم كان في سفر مع عائشة فسابقته على رجلها، فسبقته، قالت: فلما حملت اللحم سابقته فسبقني، فقال: هذه بتلك. رواه ابوداود. وسابق سلمة بن الاكوع رجلا من الانصار بين يدي النبي صلى الله عليه وسلم في يوم ذي قرد. وصارع النبي صلى الله عليه وسلم ركانة فصرعه. رواه الترمذي. ومر بقوم يربعون حجرا يعني يرفعونه ليعرفوا الاشد منهم فلم ينكر عليهم. وسائر المسابقات يقاس على هذا}. انتهى.
Ma’ana: ((Musabaka halal ce cikin sunnar Manzon Allah, da Ijma’in Maluma. A cikin Sunnah dai Ibnu Umar ya ruwaito cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya shirya Musabaka tsakanin dawakin da aka yi musu “Tadhmiir” (watau wadanda aka yi musu horon tinkarar yaki ta hanyar karanta abinci gare su da sanya musu tufafinsu da sauransu) a filin da ya taso daga Haifaa har zuwa Thaniyyatul Wadaa, haka nan ya shirya wata Musabakar tsakanin dawakin da ba a yi musu Tadhmiiri ba, a filin da ya taso daga Thaniyyatul Wadaa har zuwa Masjidu Bani Zuraiq. Buhari da Muslim ne suka ruwaito hadithin…Sannan Musulmi sun yi Ijma’i a kan halaccin Musabaka a dunkule. Sannan ita Musabaka ta kasu ne zuwa kashi biyu: Musabaka da ake yi tare da sanya wasu kudi cikinta (ga duk wanda ya yi nasara). Akwai kuma Musabaka da ake yi ba tare da an sanya kudi cikinta (ga duk wanda ya yi nasara ba). To ita Musabaka da ake yi ba tare da an sanya wasu kudi cikinta ba wannan ta halatta ba tare da sanya mata wani tarnaki a cikinta ba, kamar dai Musabakar da ake yi na tseren gudu da kafa, ko Musabakar tseren jiragen ruwa, ko Musabakar tsere tsakanin tsutsaye, ko Musabakar tsere tsakanin alfadaru, ko Musabakar tsere tsakanin jakuna, ko Musabakar tsere tsakanin giwaye, ko Musabakar yin harbi da kananan masu, ko Musabakar yin kokowa, ko Musabakar daga dutse mai nauyi sanoda gwada karfi, da dai nau’o’in Musabaka dabam daban. Saboda Annbi mai tsira da amincin Allah wata rana a hanyar tafiye-tafiyensa ya yi Musabakar tseren gudu da kafa tsakaninsa da matarsa Nana A’isha Allah Ya kara mata yarda, kuma ta yi nasara a kansa. Sai A’isha ta ce: da na yi kiba sai wata rana muka sake yin Musabakar tseren gudu da kafa sai ya yi nasara a kaina. Sai ya ce da ni: ni ma na rama wancan ci da kika yi mini. Wannan hadithi Abu Dawuda ne ya ruwaito shi. Kuma Salamah Dan Ak’wa ya yi Musabakar tsere da kafa tsakaninsa da wani mutum a gaban Annabi mai tsira da amincin Allah a ranar Ruwan Zuu Qarad. Sannan Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi Musabakar kokowa tsakaninsa da wani gwanin kokowa mai suna Rukaanah, kuma ya yi nasara a kansa ya kada shi. Tirmizii ne ya ruwaito hafithin. Sannan wata rana Annabi mai tsira da amincin Allah ya wuce wasu mutane suna Musabakar daga dutse mai nauyi saboda sanin wane ne ya fi karfi, amma bai hana su yin hakan ba. Sauran Musabakpkin sai a kiyasta su a kan wadannan)) [da nassi ya tabbatar]. Intaha.
2. Imamu Ibnu Qayyimil Jauziyyah wanda ya mutu a shekarar Hijira ta 751 watau yau shekaru 684 ke nan da suka wuce ya ce cikin littafinsa mai suna Alfuruusiyyah 1/318:-
{المسالة الحادية عشرة: المسابقة على حفظ القران، والحديث، والفقه، وغيره من العلوم النافعة، والاصابة في المسائل، هل تجوز بعوض؟ منعه اصحاب مالك، واحمد، والشافعي. وجوزه اصحاب ابي حنيفة، وشيخنا، وحكاه ابن عبد البر عن الشافعي. وهو اولى من الشباك، والصراع، والسباحة، فمن جوز المسابقة عليها بعوض، فالمسابقة على العلم اولى بالجواز، وهي صورة مراهنة الصديق لكفار قريش على صحة ما اخبرهم به، وثبوته. وقد تقدم انه لم يقم دليل شرعي على نسخه. وان الصديق اخذ رهنهم بعد تحريم القمار. وان الدين قيامه بالحجة، والجهاد، فاذا جازت المراهنة على الات الجهاد، فهي في العلم اولى بالجواز. وهذا القول هو الراجح}. انتهى.
Ma’ana: ((Mas’alah ta goma sha daya: Yin Musabakar haddace Alkur’ani, da Hadithi, da Fiqhu, da wasu Ilmummuka masu amfani, ko gane abin da yake daidai cikin wasu mas’alolin, shirya irin wannan Musabaka a bisa wani kudi, shin hakan zai halatta ko kuwa ba zai halatta ba? Mutanen Malik, da Ahmad, da Sha’fi’ii sun hana yin sa. Amma mutanen Abu Hanifah da Malaminmu (Ibnu Taimiyah) da ma hikayar Ibnu Abdil Barr daga Sha’fi’ii sun halatta yinsa. Shi wannan nau’i na Musabaka ya fi yin Musabaka a kan harkar iya sa tarko, ko kokowa, ko ninkaya, sanoda haka wadanda suka halatta shirya Musabaka a bisa kudi cikin wadannan, lalle shirya Musabaka cikin harkokin habaka ilmi shi zai fi cancantar halatta, kuma wannan ita ce surar Muraahanar da Sbubakar Siddiq ya yi da kafuran Quraishawa a kan gaskiyar labarin da ya ba su (na cewa Ruumaawa za su yi nasara a kan Faatisaawa bayan shekaru kadan). Dalili ya gabata na cewa babu abin da ya shafe ingancin wannan Muraahanar. Kuma shi Abubakar ya yi Muraahanar da su ne bayan haramta yin caca. Sannan ita tsayuwar Addini da ma tana samuwa ne ta hanyar kafa hujja, da yin jihadi, saboda wannan idan har Muraahanah za ta halatta a kan abubuwan karfafa jihadi, ke nan ta halatta a kan abubuwan karfafa ilmi da za su karfafa kafa hujja shi ne zai fi cancanta, kuma wannan magana ita ce abin rinjayarwa)). Intaha.
******************************
Lalle da wadannan bayanai ne mahankalta za su fahimci cewa ita Musabakar haddar Alkur’ani mai girma, ko musabakar haddar Hadithan Manzon Allah Masu daraja, ko musabakar haddar wani ilmi mai amfani -tare da sanya wani kudi ga wanda ya yi nasara ko kuwa ba tare da sanya wani kudi ga wanda ya yi nasara ba- abu ne da yake halal ta hanyar hujjoji biyu:-
1. Ijma’i.
2. Qiyaasi.
Wannan kuwa duka sabanin maida ranar haihuwar Annabi mai tsira da amincin Allah wani Idi ne, wanda babu Ijma’i a kansa, babu kuma wani Qiyaasi sahihi a kansa. Muna rokon Allah Ya taimake mu Ya tabbatar da dugaduganmu a kan Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah. Ameen.
Leave a Reply