Mai Rubutu: Hamza Diso
Kuskure ne mutum ya ɗauka cewar Sallah da azumi da Zakka da Hajji da zikiri sune kawai addini, duk da cewa waɗannan abubuwan suna da matuƙar muhimmanci to amma fa ba su kaɗai ne addini ba.
Kamar yadda alaƙar da take tsakanin bawa da mahalicci (Sallah da azumi da makamantansu) suke ibada hakama alaƙar da take tsakanin bawa da bawa ko bawa da sauran halittu itama ake bautawa Allah da ita
Musulunci yana da tsarin sa a kasuwanci da tattalin Arziki da siyasa da dukkanin ɓangarorin rayuwa, gini akan haka kuskure ne ace masanin addini bashi da damar yin magana a sabgar kasuwanci ko siyasa ko makamancin haka.
Sai dai haka baya nuna cewar kowanne malamin Addini zai iya magana akan komai, dole ne mutum yayi magana akan abinda ya fahimta kawai banda wanda bai fahimta ba, saboda shi musulunci shine cikakke su kuma malamai ba cikakku bane.
Misali idan malami zai yi magana akan rainon ɗa acikin wata maccen daban da ba mahaifiyarsa ba, dole sai ya fahimci mas’alar da kyau kafin yayi hukunci akai, idan kuwa bai fahimta ba to dole yayi shiru har sai sanda ya fahimta tukunna, irin haka zaka faɗa akan mas’alonin da suka shafi ma’aikata da ƴan kasuwa kamar insurance da nau’ikansa wanda ya halatta da wanda bai hallata ba.
Taƙaita musulunci acikin masallaci ko a wajen aure da jana’iza da rabon gado ba dai-dai bane
Leave a Reply