Aure ibada ne, kuma kamar yadda aka sani ibada akan samu wahala aciki da gajiya, kamar wanda zai tashi sallar asubahi a lokacin sanyi, haka nan aure, dole sai anyi haƙuri, a lokacin da ɗaya daga cikin ma’aurata ya ɓata wa ɗaya kuma yayi haƙuri toh haƙiƙah ba a banza yayi ba.
Allah zai bashi ladan wannan haƙuri, kamar yadda wanda zai tashi sallar asubahi a lokacin tsananin sanyi yayi haƙuri da wannan tsananin yaje ya bauta wa Allah. Allah zai saka masa, haka nan suma ma’aurata.
Kuma a sani babu abu mai tabbatar da zamantakewar aure irin haƙuri da yinsa don Allah.
Ya kamata ma’aurata su zamto masu:
- Haƙuri
- Tausayi
- Fara’a ga juna
- Tausa sa wa ga juna
Sannan kuma su guji yaɗa sirrin junansu.
Allah yasa mu dace.
Leave a Reply