Neman tsarin Allah daga cututtuka

Danna nan domin shiga karatu Online

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana neman tsarin Allah daga abubuwa da dama, kaman daga damuwa, baƙin ciki, bashi, talauci. da sauransu. Haka nan kuma ya kasance yana neman tsarin Allah daga cututtuka kamar yadda zamuyi bayanin addu’ar da yakeyi

Addu’a tana da matuƙar tasiri a rayuwar musulmi, domin babu asara acikin yin Addu’a. Kodai Allah ya baka abinda kake nema, ko kuma ya canza maka da wanda yafi shi, ko kuma ya kare ka daga wata musiba da wannan addu’a ta ka. Sabida haka ko wacce mutum ya samu baiyi asara ba. Shiyasa ake son Musulmi ya yawaita addu’a a kowani lokaci. Kuma addu’a shine haƙiƙanin Ibada kamar yadda Annabi ya bada labari Acikin hadisi. Abu dawud: 1479. Tirmidhi: 2968. Ibn Majah: 3828

الدُّعاءُ هُو العبادةُ

Shi yasa bashi yiwuwa ga Musulmi ya karkata addu’a zuwa ga wanin Allah Subhanahu wa ta’ala, domin yin hakan shirka ne.

a lokacin da bala’oi da annoba sukayi yawa babban abinda mutum zaiyi riƙo dashi shine addu’a, da kuma hanyoyin kariya wadda masana suka tabbatar da ingancin su. Addu’a na da tasiri matuƙa amma tasirinsa yana da alaƙa da shi mai yin addu’ar. Ƙarfin Imaninsa da kuma halarto zuciya yayin addu’a yana da tasiri matuƙa wurin karɓar addu’a.

Addu’ar da Annabi yakeyi domin neman kariya daga cututtuka:

Anas Bin Malik Allah ya ƙara Masa yarda ya rawaito Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana faɗi:

اللهم إنِّي أعوذُ بك من البَرَصِ و الجنونِ و الجُذامِ ، و من سَيِّئِ الأسقامِ

Allahumma inni a’uzu bika minal barasi wal jununi, wal juzami, wamin sayyi’il asqami.

Fassarar Addu’ar:

Allah ina roƙon ka tsari daga Albaras, da hauka, da kuturta, da duk wani mummunan cuta.

Abu dawud: 1554.
Ahmad: 13027
Annasa’i: 5493

Yana da kyau Musulmi ya lazimci wannan Addu’ar a wannan lokaci da annoba sukayi yawa, sannan kuma a sani cewa yana daga cikin hanyoyin kariya lazimtar Azkar na safe da yamma.

Allah yasa mudace, ya kuma kare mu daga duk wani cuta. Ya kuma ba wa’inda suka kamu lafiya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates