Ramadaniyyat: 1444 (10) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (10)

Ci gaba…..

Jarrabawa Ta Farko:

  1. Ibnu Taimiyya yana da gaskiya da yaƙi yarda Alƙalin Malikiyya ya yi masa shari’a. Domin kuwa shi alƙali ne mai kaushin hali, ga rashin tausayi. Ya taɓa yanke wa wani mutum hukuncin kisa saboda ana tuhumar sa da ya yi izgili da ayoyin Alƙur’ani, ba kuma tare da wata ƙwaƙƙwarar shaida ba, sannan mutane da yawa sun shaidi mutumin nan da cewa mutumin kirki ne. Har ma lokacin da aka tambayi Ibnu Daƙiƙil Id game da shi, ya ba da shaida a kansa da cewa, ya san shi mutumin kirki ne, babu wani abin tuhuma tattare da shi. Amma duk da haka Alƙalin nan ya kafe a kan hukuncin kisa da ya riga ya yanke masa, ya ƙi sauraron duk wata shaida da ta wanke shi.
  2. Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya ya yi kyan kai da ya nuna rashin amincewarsa da hukuncin wannan Alƙali Bamalike. Bugu da ƙari kuma wannan Alƙali shi ne ya fara tuhumar Ibnu Taimiyya da wasu tuhumce-tuhumce, to kuma ba abu ne na hankali ba, mutumin da yake tuhumarka, shi ne kuma zai zama alƙalin da zai hukunta ka. Bayan ya zano wa Ibnu Taimiyya tuhumce-tuhumcen da yake yi masa, sai kuma ya hana shi damar ya kare kansa; ya kawo dalililansa masu rushe waɗancan tuhumce-tuhumce. To ka ga tun daga nan ya nuna ba zai yi masa adalci ba.
  3. Ibnu Taimiya ya shiga kurkuku a watan Ramadan na shekarar 705. Shigarsa kurkuku ke da wuya, sai aka shiga cutar da mabiya mazhabar Hanbaliyya a Masar, kuma Alƙalin da yake wakiltar wannan Mazhabar, wanda shi ne alƙali na huɗu, mutum ne mai rauni, ya kasa yin kataɓus don ba wa mabiyansa kariya a majalisar alƙalai ta ƙasar, ballantana ya taɓuka wani abin a zo a gani wajen ba wa Ibnu Taimiyya kariya. Saboda rauninsa ne ma Ibnu Kasir yake cewa: “An yi wa mabiya mazhabar Hanbaliyya babban wulaƙanci a Masar, kuma dalilin haka shi ne alƙalinsu mai ƙarancin ilimi ne, don haka abin da ya same su na cutarwa ya same su”. [Al-Bidaya wan-Nihaya, juz. 14, Sh. 38].
  4. Ibnu Taimiyya ya zauna a kurkuku tsawon shekara guda. Bayan shekara sai aka fara tunanin fito da shi. Sarkin Al-ƙahira ya kirawo alƙalan nan guda uku, wato alƙalin Hanafiyya da na Malikiyya da na Shafi’iyya da wasu daga cikin malamai, ya zanta da su game da sakin Ibnu Taimiyya, domin Sarki ya fahimci cewa zaman Ibn Taimiyya a tsare a kurkuku babu adalci ko addini ko mutunci a ciki, duba da yadda a baya ya taɓa jagorantar rundunar mayaƙa, ya ƙara wa sojoji ƙaimi, ya tunkari mutuwa da kansa, har sai da aka fatattaki ‘yan ta’adda, aka karya lagon Tatar, to kuma yanzu a ce shi ne za a yi wa irin wannan mummunar sakayya!
  5. Duk kuwa da cewa waɗannan alƙalai da waɗannan malamai ba su da ra’ayin sakin Ibnu Taimiyya, ba kuma sa jin tausayin sa kamar yadda Sarki shi yake ji, to amma da yake su ‘yan amshin shatan sarakuna ne, sun kasa fitowa fili su nuna ƙin amincewa da ƙudurin Sarki, don gudun kada su fusata shi. Abin da kawai wani daga cikinsu ya yi ƙarfin hali ya nuna shi ne, dole ne a sanya wa Ibnu Taimiyya sharaɗi na zai fito ya nuna ya tuba daga aƙidarsa, sauran alƙalan da malaman suka yarda da wannan sharaɗi.
  6. An aika wa Ibnu Taimiyya ana neman sa da ya halarci zama a fada don a karanta masa matsayar malamai da sharaɗin sakinsa, sai ya ƙi zuwa, don ya riga ya san ba gaskiya ko hujja suke nema ba, kawai so suke yi su tirsasa shi a kan wani rayi nasu da ba su da wata hujja a kansa. Aka aika masa ɗan aike har sau shida amma ya ƙi zuwa, don haka suka watse. Ibnu Kasir yana cewa: “Suka watse ba lada”.

Za mu ci gaba insha Allah……

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates