Ramadaniyyat: 1444 (13) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (13)

Ci gaba…..

  1. Ibnu Aɗallah Assikandari, wani malami ne sufi wanda ya rubuta littafin “Al-Hikam’, mutum ne mai babban matsayi a wurin mabiya Ibnu Arabi da kuma sauran gama garin sufaye. Shi ne wanda ya ja zugar magoya bayansa suka nufi Fada suka kai ƙarar Ibnu Taimiyya gaban Sarki. Sai Sarki ya kirawo taro zuwa majalisar shari’a, inda Ibnu Taimiyya ya halarci wurin taron da ƙarfin gwiwarsa duk kuwa da ana tsoratar da shi cewa: ‘Lalle mutane sun maka taron dangi’, shi kuma yana amsa wa da cewa: ‘Allah ya ishe mu, kuma madalla da abin dogaro’. A nan ne ya tattauna da abokan husumarsa, ya dabaibaye su da hujjoji da dalilai masu ƙarfi, ya fito da bayani sarai yadda kowa zai iya fahimta ba tare da rikitarwa ba.
  2. To tun daga wannan lokaci ne, sufaye suka yi ta kiran tarurruka na tattaunawa a junansu, shi kuwa Ibnu Taimiyya ko a jikinsa, bai san ma suna yi ba, ya ci gaba da ƙalubalantar su da ƙarfi. Ana tsaka da haka ne, sai suka samu wata gaɓa da za su soki Ibnu Taimiyya da ita, domin shi a fahimtarsa, ba ya halatta a nemi agajin da ba mai iya yin sa sai Allah, a wurin wani ba Allah ba; ko da kuwa Annabinmu Muhammadu (SAW) ne. Ibnu Taimiyya ya yi wannan bayani ne lokacin da yake tsaka da tattauna wa da Ibnu Aɗallah Assikandari, to nan take sai wani cikin mahalarta taro ya ce, wannan maganar babu laifi a cikinta. Sai shugaban alƙalai a wurin ya ce, ‘Akwai ƙarancin ladabi a wannan magana’, amma dai bai ce kafurci ne ba.
  3. Hukuma ta shiga damuwa ƙwarai da irin wannan ka-ce-na-ce da ake ta yi a gari, suka duba suka ga babu hanyar dakatar da ita sai hanya ɗaya tak, watau shi ne su rufe bakin wannan baƙon nasu (Ibnu Taimiyya) wanda shi ne ya taso da maganar. Sai suka ba shi zaɓin ɗayan abu uku: Ko dai ya koma Iskandariyya da zama; ko ya koma can garinsa Dimashƙa; ko kuma a tsare shi a kurkuku. Sai ya zaɓi ya tafi kurkuku, domin zai kasance ne a cikin takunkumi idan ya zaɓi ya koma Iskandariyya ko garinsa Dimashƙa, saboda ba za a ƙale shi ya sake bayyana aƙidarsa ba, don haka sai ya ce: “Kurkuku shi ya fi soyuwa a gare ni”. Ya zaɓi zama a kurkuku a kan a yi masa takunkumi a hana masa faɗar ra’ayinsa. Abin da ya yi Imani da shi, shi ne a ƙale malami da ‘yancin faɗar abin da ya yi Imani da shi ya fi masa a kan a ba shi ‘yancin walwala da yawo ko’ina, amma a rufe masa baki ba ya da ikon faɗin abin da ya yi imani gaskiya ne.
  4. Duk da Sheikhul Islam ya zaɓi zaman kurukuku, to amma almajiransa sun fi zaɓa masa koma wa garinsa Dimashƙa. Sai ya kama hanya a ranar sha takwas ga watan Shawwal na shekarar 707 ya nufi Dimashƙa. Ya kama hanya ke nan sai mahukunta suka yi shawarar su dawo da shi, don haka suka aika masa waɗanda suka juyo da shi zuwa Alƙahira. Suka kuma sanar da shi cewa, hukuma ta ce kawai za ta sake mayar da shi gidan kurkuku. Da alama waɗannan mutane sun fahimci idan har ya koma Dimashƙa, to zai kasance a tsakiyar magoya bayansa ne, kuma zai yi watsi da duk wani sharaɗi da suka gindaya masa na ya ja bakinsa ya yi shiru, kada ya sake cewa komai a kan batutuwan Musulucni.

Za mu ci gaba insha Allah…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates