‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (14)
Ci gaba…..
An Sake Gurfanar Da Ibnu Taimiyya Gaban Shari’a:
- An sake kai Ibnu Taimiyya zuwa gaban hukunci. Amma a wannan karon, a cikin alƙalan da za su dubi shari’arsa akwai waɗanda suka san wane ne Ibnu Taimiyya, suke kuma tuna ƙoƙarinsa da sadaukarwarsa a baya. Sun gane cewa, duk da irin saɓani da ya zo musu da shi, to amma kuma shi mutum ne mai tsoron Allah mai kwatanta gaskiya, don haka dole ne a yi la’akari da waɗannan abubuwa. Wannan ya sa suka wanke shi daga duk wani zargi da ake yi masa. To amma duk da haka an samu wasu da suka ci gaba da dagewa a kan dole sai an hukunta shi, wasu kuma suka kafe a kan ba za sake mayar da shi kurukuku ba. Ganin yadda jayayya ta kaure tsakanin ɓangarorin nan biyu, sai Ibnu Taimiyya ya raba gardama; ya zaɓi ya tafi kurkuku. Sai wani mai suna Nuraddin Azzawawi, wanda shi da ma bai amince da a sake tsare Ibnu Taimiyya ba, ya kada baki ya ce, “To sai dai a kai malam inda ya dace da matsayinsa”. Sai aka ce masa: “ Hukuma kam ba ta san da wani wurin tsare mutane ba sai kurkuku”. Daga ƙarshe aka aika da Ibnu Taimiyya zuwa kurkukun alƙalai, amma an yi masa izini ya tafi tare da mai masa hidima.
- Wannan dambarwar da ta kai ga tsare Ibnu Taimiyya ta kasance ne tsakaninsa da sufaye, ba tsakininsa da malaman fiƙihu ba. Wata ƙila ana iya cewa, wannan yana daga cikin dalilan da suka sa Ibnu Taimiyya ya sami masu ƙaddara shi a wannan karon, domin su kansu Fuƙaha’u ba su yarda da aƙidar ‘Wahdatul Wujudi’ ba, domin a fahimtarsu wannan aƙida ta fi duk wani ra’ayi da Ibnu Taimiyya yake kira a kai muni. Don haka a wannan karon sai suka riƙa ɗaukan sa a matsayin mai ba wa Musulunci kariya, don haka suka tausaya masa ƙari a kan ƙarfin hujjarsa da bayaninsa.
- Tsare Ibnu Taimiyya a kurkuku bai hana wa almajiransa damar zuwa wajensa safe da yamma ba. Sannan kuma ba da jimawa ba aka sako shi, bayan alƙalai da Fuƙaha’u sun sake duba shari’arsa a majalisin alƙalanci da ke Madrasatus Salihiyya, suka yanke hukuncin a sako shi.
Za mu ci gaba insha Allah…..
Leave a Reply