‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (2)
Ci gaba…..
Tasowarsa:
- Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya ya taso a gidan ilimi; gidan da babu abin da suka sa a gaba sai darasi da bincike da rubuce-rubuce da neman ilimi. Don haka ya sami kansa cikin wani yanayi mai cike da son ilimi da malamai da sanin mahimancin neman ilimi. Wannan yanayi ne ya yi wa Ibnu Taimiyya tasiri babba a rayuwarsa. Tun yana ƙarami ya haddace Alƙur’ani mai girma, ya kuma lizimci karatunsa da tilawarsa dare da rana, ya mayar da shi ya zama abokin hirarsa tun daga wannan lokaci har zuwa lokacin da aka tsare shi a kurkuku, ya zamanto ba shi da abin karatu sai Alƙur’ani. Kamar yadda masana tarihi suka faɗa cewa, a zamansa na ƙarshe a kurkuku ya yi hatma (wato sauka) ta Alƙur’ni har sau tamanin.
- Baya ga Alƙur’ani, Ibn Taimiyya ya mayar da hankali sosai a kan ilimin Hadisi, ya shiga nemansa gadan-gadan ba ji ba gani, musamman saboda kasancewar mahaifinsa Abdul-Halim shi ma babban malamin hadisi ne shararre a zamaninsa, domin kuwa isowarsa garin Dimashƙa ke da wuya, sai ga shi an ba shi babbar kujerar karantarwa irin wadda ake ba wa manyan malamai a garin, duba da yadda labarin zurfin iliminsa ya bayyana ya kuma watsu ko’ina a gari. An ba wa Mahaifin Ibnu Taimiyya kujerar karantawa a babban masallacin Banu Umayyah, (Al-Jami’ul Umawi) da ke birnin Dimashƙa. Sannan ya zama babban Shehin Makarantar Darul-Hadis As-Sukkariyya.
- Mahaifin Ibnu Taimiyya, watau Shihabud-Din Abul Mahasin Abdul-Halim Al-Harrani, malami ne da aka yi wa shaida da zuzzurfan ilimi. Masana tarihi sun ce, yakan hau kujerar karantarwa ya yi ta zuba karatu da ka, na tsawon sa’o’i ba tare da yana riƙe da ko tsinke a hannunsa ba balle kuma littafi. A hannu wannan bijimin Malami ne Ibnu Taimiyya ya taso, Allah kuma ya kimsa masa son ilimin hadisi da fiƙihun Hadisi, waɗannan fannoni biyu kowa su ne tushen ilimin addini.
- Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya ya taso tun yana ƙarami da wasu siffofi guda uku:
a) Koƙari da ƙwazo da juriya da mai da hankali wajen neman ilimi, tare da ƙaurace wa wasanni irin na yara sa’anninsa.
b) Zurfin fahimtar abubuwan da suke kewaye da shi, wanda hakan ya gadar masa bin abubuwan da suke faruwa ƙeƙe da ƙeƙe tare da kykkyawar fahimta mai inganci a gare su.
c) Kaifin ƙwaƙwalwa da lafiyayyen tunani. Kaifin ƙwaƙwalwarsa ta zama abin labari a tsakanin yara matasa sa’anninsa, kai har abin ya zarce zuwa ga manya, labarinsa ya kewaye garin Dimashƙa baki ɗaya. A ruwaito labarai masu yawa iri-iri waɗanda idan mutum bai tava bin duddugin tarihin wannan bawan Allah ba, sai ya zaci cewa zuzuta shi ne kawai wasu masoyansa suke yi, alhali labarai ne ingantattu da suka faru a rayuwar wannan bijimin malami. Babu shakka Ibnu Taimiyya ya gaji irin wannan zarangwana ne daga iyaye da kakanni.
Za mu ci gaba insha Allah……….
Leave a Reply