- Sarki ya sa aka rubuta takarda a ranar 19 ga Ramadan na sherkarar 719 zuwa Dimashƙa. A cikin wannan takarda Sarki ya fito fili ya ƙara jaddada maganar dakatar da Ibnu Taimiyya daga yin fatawa. Aka tara alƙalai da malamai aka karanta wa Ibnu Taimiyya wannan takarda, aka kuma zarge shi da bijire wa umarnin Fada. Amma har aka tashi daga wannan taro Ibnu Taimiyya bai yi musu alƙawarin cewa zai amince ya daina fatawa ba. Don haka ya ci gaba da fatawoyinsa. Sarki ya sake aiko da takarda tare da jankunne karo na biyu, amma Ibnu Taimiyya ya sake bijire wa wannan umarni na mai martaba Sarki. To don haka Sarki ba zai iya ci gaba da kauda kai daga wannan lamari ba. Idan kuma har Sarki zai kauda kai, to su alƙalai da malamai ba za su iya ba, domin suna ganin Ibnu Taimiyya da fatawoyin nan nasa yana keta ijma’in da limaman Mazhabobi huɗu suka yi, wanda hakan a fahimtarsu ɓata ne mabayyani.
- Wannan ya sa aka sake kiran taron alƙalai da malamai na duka mazhabobi huɗu a fadar magajin gari. Ibnu Taimiyya ya halarci wannan wuri. Suka ƙara jan kunnensa da yi masa kashedi a kan ya daina fatawa game da waɗannan mas’aloli. Kuma kamar koyaushe sun fi son su yi kashedi da jan kunne a kan su ce za su jayayya da shi a kan abin da suke saɓani a cikinsa.
92.Da abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, sai suka yanke shawarar su tsare shi a Fadar Dimashƙa. To kuwa hakan aka yi, ya ci gaba da zama a tsare har tsawon wata biyar da kwana goma sha takwas. Tun daga 22 ga watan Rajab shekara ta 720 har lokacin sakin sa a ranar 10 ga watan Almuharram na shekara ta 712.
- Da fitowar Ibnu Taimiyya, sai ya koma ya ci gaba da darasinsa abinsa. Ya kuma ci gaba da ba da fatawa a kan waɗannan mas’aloli bai fasa ba, har su ma suka saba da jin su daga bakinsa, ko da kuwa ba sa so kuma ba su yarda ba. Shi kuma ya ci gaba da bincike da nazari da rubuce-rubucen littattafai. Ana la’akari da wannan zango na rayuwar Ibnu Taimiyya wanda ya fara daga shekara ta 712 shi ne lokacin da Ibnu Taimiyya ya samar da rubuce-rubucensa da suke da nasaba da mas’alolin fiƙhu masu muhimmanci sosai. Amma duk da haka ya ci gaba da karantar da aƙida da bayanin matsayinsa game da sufanci da sufaye da tsawatarwa a kan bid’o’in da suke yaɗa wa.
Za mu ci gaba in sha Allah…
Leave a Reply