Ramadaniyyat: 1444 (25) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (25)

Ci gaba…..

  1. An kai matuƙa wajen takura Ibnu Taimiyya, har an kai ga hana shi littattafai; an hana shi rubutu; an raba shi da alƙaminsa da tawadarsa. Amma hakan bai hana ra’ayinsa watsuwa ba, bai yi masa shamaki ba. Idan wani lokaci ya matsu da sai ya rubuta wani abu da ya bijiro masa, ko wani tunani da ya ɗarsu a zuciyarsa, to yakan yi amfani da baƙin gawayi ya yi rubutun da shi a wata yasasshiyar takarda. Irin waɗannan takardun da ya riƙa rubuta wa da baƙin gawayi an tattara su an aje su a matsayin kayan tarihi na Ibnu Taimiyya.
  2. Ibnu Taimiyya ya yi matuƙar haƙuri da juriya da jarrabawar da ta same shi, domin ya san wannan duka jihadi ne don Allah. A kan haka ne ma yake cewa: “Wallahi na rantse da Allah, mu muna cikin wannan babban jihadi ne don Allah. Kai! Wannan jihadin namu yana daidai da jihadin da muka yi a lokacin ƙazan, da ‘yan Jabaliyya da Jahmiyya da Ittihadiyya da makamantansu. Wannan yana daga cikin manyan ni’imomi da Allah ya yi mana, ya kuma yi wa mutane, sai dai yawancin mutane ba su san haka ba”.
  3. Wannan maganar tana daga cikin maganganun da aka samu ya rubuta da baƙin gawayi a wata yasasshiyar takarda. [Duba, Al-Uƙudud Durriyya, sh. 382].
    Ibunu Taimiyya Ya Amsa Kiran Ubangijinsa:
  4. Zaman Ibnu Taimiyya a wannan ƙuntataccen wuri bai tsawaita ba, domin Allah ya karɓi abinsa a ranar ishirin ga watan Shawwal, na shekarar 728 bayan wata ‘yar rashin lafiya da ya yi.
  5. Ibnu Taimiyya ya mutu yana babban mutum, kamar yadda ya rayu yana babban mutum. Wazirin Dimashƙa ya je wajensa lokacin yana cikin jinya, don ya ba shi haƙuri ya kuma nemi afuwarsa a kan abubuwan da yake ganin ya aikata masa waɗanda ba su dace ba, amma sai Ibnu Taimiyya ya ba shi amsa da cewa: “Na yafe maka, na kuma yafe wa duk wanda ya nuna mini ƙiyayya ba tare da ya san ni ne mai gaskiya ba. Na ya yafe wa mai martaba Sarki Nasir a kan tsare ni da ya yi, domin ya yi haka ne don taƙilidi ga wasu, ba ya yi haka ne ba don huce haushi. Duk wanda wani abu ya shiga tsakanina da shi, to na yafe masa, sai dai wanda ya zamanto maƙiyin Allah ne da manzonsa”. [Al-Bazzar, Al-a’lamul Aliyya, sh. 81-82].
  6. Ibnu Taimiyya ya rasu. Garin Dimashƙa ya yi tsit babu wani motsi. Kowa jikinsa ya yi sanyi, saboda babban malaminsu, Allah ya yi masa rasuwa. Jama’a suka fito dodo-dodo domin su yi bankwana da shi. Allah ya ƙaddara wannan baban mutum zai komo ga Allah ba tare da wani ɗan da ‘ya mace ta haifa yana da abin da zai goranta masa ba. Alaƙarsa da Sarki Nasir ta yi ƙarfi sosai, har sai da ta kai ga Sarki ya ba shi wuƙa da nama a kan sha’anin malaman da suka daɗe suna cutar da shi, a kan cewa ya yanke musu duk hukuncin da ya ga dama, amma bai faɗi komai a kansu ba sai alheri.
  7. Da a ce lokacin da Ibnu Taimiyya ya rasu yana nan tare da Sarki a Fada, da wasu mutane sun riƙa cewa, ‘ai shi malamin fada ne, mai fushi da fushin Sarki, ba don Sarki ya ɗaure masa gindi ba da ba wanda ma ya san shi’. To Allah da ƙudurarsa bai bari haka ta faru ba, sai ya nuna wa duniya wanene haƙiƙanin wannan malami ɗan baiwa mai tsoron Allah. Malamin da tsoron wani mahluƙi bai hana shi faɗar gaskiya ba komai ɗacinta. Malamin da ya zama kamar ƙatuwar inuwar bishiya wadda kowa yake fake wa a ƙarƙashinta. Wanda bai dogara da kowa ba sai Allah. Da a ce shi ɗan-kanzagin Sarki Nasir ne, da bai kai shi gidan kurkuku ya rufe shi ba. Wannan kaɗai ya isa dalili mai nuna cewa, shi shugaba ne abin koyi, ba ɗan-kanzagin wani ne ba, ba kuma wani ne mai ba shi umarni yana bi ido-rufe ba.
  8. Ibnu Taimiyya ya koma ga Mahaliccinsa bayan ya shafe sama da shekara talatin yana fafutuka cikin hanyar Allah, tun daga lokacin da tauraronsa ya ɗago har zuwa lokacin da ransa ya bar gangar jikinsa. Allah ya ƙara masa rahama, ya ji ƙan sa, ya kuma karɓi kyawawan ayyukansa, ya yafe masa kurakuransa. Amin.

Za mu ci gaba in sha Allah…

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories