Ramadaniyyat: 1444 (23) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (23)

Ci gaba…..

  1. Daga lokacin da aka ce an tsare Ibnu Taimiyya, sai duk wani mai mugun nufi ya bayyana mummunar aniyarsa a fili. Aka fara gallaza wa almajiran Ibnu Taimiyya da masoyansa. Shugaban alƙalai ya ba da umarni a tsare wasu daga cikin almajiransa, ya kuma wulaƙanta wasu daga cikinsu, yayin da ya sa aka ɗora su a kan jakai aka riƙa zagaya gari da su a na shela a kansu. Sannan daga bisani aka sake su bayan an tuhume su, amma kuma ba a saki babban almajirin Ibnu Taimiyya ba, wanda shi ne ya ɗauki tutar da’awarsa da karantarwarsa a bayansa, watau Shamsuddin Ibnu ƙayyimil Jauziyya.
  2. Wannan abu da aka yi wa Ibnu Taimiyya da almajiransa ya ɓata wa mutanen kirki da yawa rai, amma kuma ta ɓangare guda mahassadansa da ‘yan bid’a sun ji daɗi sosai. Waɗanda suka ji zafin abin da ya faru ba su taƙaita a kan mutanen Dimashƙa kaɗai ba, a’a har mutanen Bagadaza, abin ya ƙona musu rai sosai. Suka rubuta takarda zuwa ga Sarki Nasir suna koka masa wannan musiba da ta same su. A cikin takardar suka faɗa masa cewa: “Yayin da labari ƙuntata wa Sheikhul Islam Taƙiyyuddin Ahmad bn Taimiyya – Allah ya kuɓutar da shi- ya isa ga kunnuwan mutane gabas da nahiyoyin Iraƙi, al’amarin ya girmama a wurin Musulmi da masu addini, fanɗararrun mutane sun ƙar ɗago da kawunansu, abin ya yi wa ‘yan bid’a daɗi. Yayin da malaman waɗannan garuruwa suka ga girman wannan masiba da ta auku, da yadda ‘yan bid’a suke yi wa mutane masu daraja da malamai dariya, sai malamai suka yanke shawarar su kawo kukansu wannan fada mai daraja. Allah ya ƙara mata daraja. Suka kuma rubuto jawabansu waɗanda suke ƙunshe da goyon bayan fatawar Sheikh da nuna cewa a kan daidai take”.
  3. Wannan nuna goyon baya a kan fatawar Ibnu Taimiyya ya zo ne daga mabanbanta mazhabobi, daga cikinsu akwai Malikiyya, da Hanafiyya da Shafi’iyya. Wannan ya nuna lalle da’awar Ibnu Taimiyya ta kai zuwa ga ɗaukakin malamai a Masar da Sham da Iraƙi, kuma ya nuna lalle da’awar Ibnu Taimiyya ta yi tasiri a zukatan mafi yawancinsu. Kuma malaman bid’a a ko’in sun yi farin ciki da sake tsare Ibnu Taimiyya da aka yi.

Za mu ci gaba insha Allah…

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates