Ramadaniyyat: 1444 [4]
‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (4)
Ci gaba…..
Birnin Dimashƙa A zamanin Ibnu Taimiyya:
- Sheikhul Islam Ibn Taimiyya ya ci ga da neman ilimi a ƙarƙashin kulawar Babansa. Kasancewarsa tare da Banbasa ya yi matuƙar yi masa amfani a rayuwarsa ta ilimi. Sannan Ibnu Taimiyya ya taso cikin wani ma’adini da mahalli na ilimi watau Birnin Dimashƙa. Wannan birini shi ne birni na biyu da ya ƙunshi malamai waɗanda suka yi yo ƙwaura daga garuruwan gabas da yamma. Birni na farko shi ne birnin Alƙahira da ke ƙasar Masar. Malamai sun yi ta yin ƙaura suna dawo cikinsa, domin samin mafaka a wurin mahukuntansa waɗanda suka kasance masu ɗabi’ar karvar baƙin malamai da karrama su da ba su kulawa, har sukan yanka musu albashi na wata-wata da ware musu hubusi domin kulawa da rayuwarsu da ta iyalansu.
- A lokacin da mayaƙan kiristocin ƙasashen yamma suka riƙa kai hare-hare a kan garuruwan Musulmi, malamai da dama sun yi yo ƙwaura zuwa birnin Dimashƙa, sannan daga nan zuwa birnin Alƙahira. Hakanan a lokacin da ‘yan ta’addar ƙabilar Tatar suka riƙa kai hare-hare ƙasashen Musulmi da ke gabas, har ma suka mamaye su; suka cika su da varna da ta’addanci; suka ƙawace babbar birnin Daular Musulunci ta lokacin watau Bagadaza, to a nan ma malamai masu yawa sun fita gudun hijira zuwa Dimashƙa, wasu daga cikinsu suka yada zango a nan, wasu kuma tsoro da fargabar maƙiya ya sa suka ƙara gaba har zuwa birnin Alƙahira.
- Don haka Dimashƙa a zamanin Ibnu Taimiyya matattara ce ta malamai, shi ma nan ne wurin da iyayensa suka yi wo gudun hijira don neman mafaka. Birnin Dimashƙa birni ne da yake cike da makarantun ilimi, kama daga makarantu koyar da ilimin hadisi da na koyar da Fiƙihun Mazhabar Hanbaliyya da na koyar da Mazhabar Shafi’iyya da sauran fannunka. Sannan kuma gari ne da ya tara manya-manyan malamai na kowane fannin ilimi; ga irin su Malam Izzuddin bn Abdissalam; ga Imamun Nawawi; ga Ibnu Daƙiƙil Id; dukkansu malamai ne masu karantar da ilimin Fiƙihu da na Hadisi karatu mai zurfi. Suna nazari a kan fiƙihun mazahabobi na Musulunci daban-daban; suna kuma nazari a kan hadisi da isnadinsa da mazajensa da mataninsa da auna tsakanin riwayoyi mabanbanta. An tattara hadisai a cikin manya-manyan littattafai, ana kuma yin nazari a kansu cikin nutsuwa da basira. A cikin babi guda, mai karatu zai ga an tattatara hadisan wannan babi wuri ɗaya; da masu inganci da marasa inganci duka, tare da bayanin matsayin kowane daga cikinsu, sannan da warware duk wani rikici ko ƙulli da zai hana samun kyakkyawar fahimta game da su. Daga ƙarshe Mai karatu zai samu komai a sauƙaƙe.
- Bayan ilimin Hadisi da na Fiƙihu da suka shahara a birnin Dimashƙa, akwai kuma ilimin Aƙidar Musulunci. A wannan zamanin Aƙidar Ash’ariyya ita ce aƙidar da ta mamaye ko’ina. A kanta ne sarakuna suka taso, don haka suka rungume ta suka kuma ba ta goyon baya da taimako wajen yaɗa ta.
- Aƙidar Ash’ariyyanci ta ginu a kan bayanin Siffofin Allah da Ayyukansa ta hanyar amfani da ilimin Falsafa da na Manɗiƙi, wanda hakanne ya haifar da yamutsi mai yawa a game da Siffofin Allah da ayyukansa da wasu mas’aloli na gaibu, har ta kai an kauce wa hanyar magabata na ƙwarai; watau Sahabbai da Tabi’ai a kan fahimtarsu.
- Malaman Mazahabar Hanbaliyya, a wannan lokaci sun ginu a kan ƙaurace wa irin waccan hanya, sun yi tsaye a kan abin da Limamin Mazhabarsu ya yi fafutaka a kai, watau gina fahimtar mas’alolin aƙida a kan nassoshin Alƙur’ani da sunnar Annabi (SAW) da fahimtar magabata na ƙwarai. Wannan sabani shi ne ya zama babban jigon da ya haifar da rikita-rikita tsakanin Ibnu Taimiyya da sauran malaman zamaninsa waɗanda ba Hanbaliyya ba, har sabanin ya jefa shi cikin matsaloli masu yawa waɗanda suka yi kusa su je fa rayuwarsa cikin haɗari ba don taimakon Allah ba.
Za mu ci gaba insha Allah….
Leave a Reply