Ramadaniyyat: 1444 (6) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (6)
Ci gaba…..

Zahabi Yana Bayanin Ilimin Ibnu Taimiyya:

  1. A cikin wani bayani da aka samu daga babban malamin tarihin nan kuma masanin hadisi, ɗaya daga cikin almajiran Ibnu Taimiyya da ya yi a kan ilimin malamisa, inda yake cewa: “Ya karanci Alƙur’ani ya san Fiƙhu. Ya tattauna da malamai tare da kafa dalilai tun yana ƙarami bai balaga ba. Ya goge a Tafsiri. Ya yi fatawa ya karantar tun yana ƙasa da shekara ashirin. Ya yi rubuce-rubuce da yawa. Ya zama daga cikin manyan shehunai tun malamansa suna da rai. Ya wallafa manya-manyan littattfai da suka watsu a ko’ina. Ya riƙa gabatar da tafsirin Alƙur’ani da kai a duk ranar juma’a na tsawon shekara biyu. Yana da kaifin ƙwaƙwalwa.
  2. Ya ruwaici littattafan hadisai da dama daga malamai. Yana da malamai da ya yi karatu a hannunsu sama da ɗari biyu. Ya kai maƙura a fagen sanin tafsirin Alƙur’ani. A fagen haddar hadisan Manzon Allah (SAW) da sanin mazajensu da ingantattu da masu rauni, a nan ba wanda ya kama kafarsa. Yadda yake kuma jayo mas’alolin Fiƙhu da mazhabobin sahabbai da tabi’ai, ba ya ga mazhabobi huɗu, to a nan ma ba ya da na biyu. Ta vangaren sanin addinai da ƙungiyoyi da ilimin Aƙida da ilmul kalam, to ban san wani kamarsa ba. Ya san wani kaso mai tsoka a ilimin Luga, ga kuma Larabci mai ƙarfi sosai. Ta bangaren sanin ilimin Tarihi da Sira kuwa al’amarinsa yana da ban mamaki…”. [Ibn Abdulhadi].

Ibnu Taimiyya Da Dariƙun Sufaye:

  1. Ibnu Taimiyya ya soki lamirin ɗariƙun sufaye a zamaninsa, musamman bayan ya ga yadda wasu suka taimaka wa Tatar ‘yan ta’adda yayin da suka nufo garin Dimashƙa da bayan sun shigo gari. Sannan ya ga yadda suka cika addini da varna da ayyukan rufa ido da dabo. Suka gauraya tsakanin sunna da bid’o’i marasa tushe a Musulunci. Ya riƙa sukar maganganun wasu daga cikin manya shehunanusu da aƙidunsu tare da mayar musu da martani mai cike da hujjoji na ayoyin Alƙur’ani da sunna.
  2. Ya yi karon batta da mabiya ɗariƙar Rufa’iyya masu saddabaru suna shiga cikin wuta ba tare da ta ƙona su ba. Ya fallasa asirunsu, ya kuma ƙalubalance su da a hura wuta, su yi wanka shi ma ya yi wanka, su shigar wutar tare, amma sai suka noƙe, daga ranar asirinsu ya tonu. Wannan al’amari ya jawo wa Ibnu Taimiyya abokan hamayya da dama daga cikin mabiya waɗannan ɗariƙu da masoyansu…

Za mu ci gaba…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories