Annabi Muhammad Tsira da
Aminci Su tabbata a gare shi yana
cewa duk wanda yayi riko da
Sunnah ta tamkar yayi riko da
garwa shin wuta ne.
In ka fahimci wannan Hadisin zaka
san da cewa duk wanda zai yi koyi
da karantarwan Annabi sai yaci
karo da matsaloli da yawa daga
makiya Sunnah masu cewa suna
son Annabi a baki.
Dole sai kayi koyi da Annabi kafin
kace mana kana son Annabi, shin
saka wandon ka irin na Annabi ne?
Ko mu’amalarka irin na Annabi ne?
Shin kana yin addini kamar yadda
Annabi yazo dashi? Ko kuma kana
ganin Annabi bai iya ba kaine ka
iya, shi yasa ka fito da sabon abu a
addini kuma da sunan neman lada,
in hakan ya tabbata sai ka binciki
kanka a ina ka samo shi? A wurin
Annabi ko a wurin sahabbai?
Addinin nan na Musulunci sauki
gare shi, dukkan Ibadan da zakayi
yana nan a rubuce, a Qur’ani ko a
Hadisi, ka koma ka bincika zaka
samu, kayi yadda Annabi yayi ko
yace ayi shi kenanan ka gama
naka.
Amma rayuwar in ka duba tarihin
Annabawa tun daga farko har
zuwa yau zakaga mafiya yawan
wadanda ake kashewa ko zagi ko
munanan kalamai gare su laifinsu
kawai sunce ayi addini yadda Allah
ya saukar,
Ya kai Malamin Sunnah dama mai
koyi da Sunnah, ka sani cewa aikin
da kakeyi ja ne, Dole sai kaji
munanan kalamai daga makiya
Sunnah, wasu ma sai sun dokeka,
wasu ma kashe ka zasuyi, dukkan
wadannan abubuwan anyiwa
Annabawa, anyiwa sahabbai,
anyiwa tabi’ai, anyiwa Mutanen
Sunnah da dama, to kai me zai
dameka ko yasa kaji tsoron wanin
Allah? Daga radda ka fara samun
wadannan matsaloli kayi ta
addu’an Allah ya amshi ranka ta
wannan hanyar, mutuwa dole sai
anyita, in kaji tsoron mutuwa da
bindiga ko takobi, kana iya shan
farfesun rago cikinka ya baci kayi
ta gudawa har ka mutu, mutuwa
bata sallama.
Kuma muna tabbatar muku da
cewa babu batun daga kafa kan
kira ga tafarkin Sunnah, dole sai
mun yaki bidi’ah koda ta wannan
Hanyar zaizama sanadiyar
komawar mu ga Allah.
Masu zagi, Masu Duka, Masu Kisa,
Masu Qage da sauransu muna
dada sanar daku bakwa gaban mu,
Kuma da ikon Allah sai kowa ya
fahimci kiran da mukeyi na abi
Sunnah a kawar da Bidi’ah.
Muyi ta kokarin yin addini domin
yardan Allah, Allah zai taimake mu,
Allah zai karemu da sharrin Masu
Sharri, Allah bamu ikon fadin
gaskiya ga kowanene.
Allah ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya
nuna mana karya karya ce ya
bamu ikon kauce mata.
Leave a Reply