RUWAN ZAMZAM MAI ALBARKA(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

Tarihin wannan ruwa, kamar yadda
yazo a cikin Sahihul Bukhari,
Lokacin da Annabi Ibrahim (AS) ya
ajiye matarsa,da dansa, a wajan,
Mala’ika Jibrilu, ya buga wajan da
duddugansa, sakamakon haka aka
sami ruwan Zamzam,
Wannan ruwa dashi aka wanke
zuciyar Annabi saw, a lokacin yana
dan shekara hudu, a wajan
Halimatus- Sadiya, da kuma
lokacin tafiya Isra’i
Manzon Allah saw yace: Ruwan
zamzam, (zaa sami biyan bukata
da niyar ) da aka sha. Sahihu ibn
Majah.
idan mutum zai sha ruwan
zamzam yasha da niyya mai kyau,
kuma yayi addu’a ta gari, kamar
yadda magabata sukeyi,
A wani hadisin yace : Ruwan mai
albarka ne, abincin mai cine, kuma
ruwan mai sha ne. Muslum 2473
A wata Riwayar, Ruwa ne mai
albarka, abincin mai ci, waraka
daga rashin lafiya, Assunanul
kubra Baihakiy, ajamiu- Sahih
2435
A wata, riwayar, Mafi alkhairin
ruwa a bayan kasa shine ruwan
zamzam. Sahihut-targib wat-tahib.
Nana Aishah ta kasance, tana
guzirin ruwan zamzam a cikin
kwalbah,
kuma tace: Manzon Allah saw,
yana guzirin ruwan zamzam, a
cikin salka, yana zubawa, marasa
lafiya, yana shayar dasu, Sahihut-
tirmiziy.
Mal,Ibnul- Qayyim yace, yaga abin
al’ajabi gamai da ruwan zamzam,
daya gamu da rashin lafiya a
maccah lokacin babu likita sai ya
gwada amfani da ruwan zamzam,
yana tofa suratul fatihah a ciki, ya
sha ya sami lafiya. Zadul- maad

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates