SALLAR TAHAJJUD CIKIN JAMA'A A CIKIN RAMADAN(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

‘yan’uwa Musulmi! Nafilfilin nan da
ake yi cikin jama’ah bayan an
gama sallan tarawihi a cikin
masallatan Musulmi na duniya ana
kiran su ne cikin littattafan fiqhu da
sunan: “Salaatut Ta’aqib”
Babban Malami cikin mazhabar
Hambaliyya Ibnu Qudaamah ya ce
cikin littafin Al-Mugnii 2/515:-
(( ﻓﺼﻞ: ﻓﺄﻣﺎ ﺍﻟﺘﻌﻘﻴﺐ: ﻭﻫﻮ ﺃﻥ ﻳﺼﻠﻲ ﺑﻌﺪ
ﺍﻟﺘﺮﺍﻭﻳﺢ ﻧﺎﻓﻠﺔ ﺃﺧﺮﻯ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺃﻭ ﻳﺼﻠﻲ ﺍﻟﺘﺮﺍﻭﻳﺢ
ﻓﻲ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺃﺧﺮﻯ. ﻓﻌﻦ ﺃﺣﻤﺪ: ﺃﻧﻪ ﻻ ﺑﺄﺱ ﺑﻪ، ﻷﻥ
ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﻗﺎﻝ» :ﻣﺎ ﻳﺮﺟﻌﻮﻥ ﺇﻻ ﻟﺨﻴﺮ ﻳﺮﺟﻮﻧﻪ
ﺃﻭ ﻟﺸﺮ ﻳﺤﺬﺭﻭﻧﻪ. ﻭﻛﺎﻥ ﻻ ﻳﺮﻯ ﺑﻪ ﺑﺄﺳﺎ، ﻭﻧﻘﻞ
ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﻜﻢ ﻋﻨﻪ ﺍﻟﻜﺮﺍﻫﺔ ﺇﻻ ﺃﻧﻪ ﻗﻮﻝ ﻗﺪﻳﻢ.
ﻭﺍﻟﻌﻤﻞ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ. ﻭﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﺑﻜﺮ :
ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺇﻟﻰ ﻧﺼﻒ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺃﻭ ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮﻩ ﻟﻢ ﺗﻜﺮﻩ
ﺭﻭﺍﻳﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ. ﻭﺇﻧﻤﺎ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﻓﻴﻤﺎ ﺇﺫﺍ ﺭﺟﻌﻮﺍ ﻗﺒﻞ
ﺍﻟﻨﻮﻡ. ﻭﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﺃﻧﻪ ﻻ ﻳﻜﺮﻩ. ﻷﻧﻪ ﺧﻴﺮ ﻭﻃﺎﻋﺔ ﻓﻠﻢ
ﻳﻜﺮﻩ ﻛﻤﺎ ﻟﻮ ﺃﺧﺮﻩ ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮ ﺍﻟﻠﻴﻞ)).
Ma’ana: ((Amma At-Ta’aqiib,
wanda shi ne: a sallaci wata nafila
daban cikin jama’ah bayan
tarawihi, ko kuwa a sallaci tarawihi
cikin wani jama’ah daban, toh, an
ruwaito daga Ahmad cewa babu
wani laifi cikin yin sa; saboda Anas
Dan Malik ya ce: Ai ba sa dawowa
su sake salla sai saboda wani
alheri da suke tsammani ne, ko
saboda wani sharri da suke
gujewa ne. Ya kasance ba ya
ganin wani laifi cikin hakan. Amma
Muhammad Dan Al-Hakam ya
ruwaito daga gare shi (Imam
Ahmad) karhantawa sai dai fa
wannan tsohon zance ne. Abin da
ake yin aiki da shi shi ne abin da
jama’ar (Almajiran shi Ahmad)
suka ruwaito. Abubakar ya ce:
Salla har zuwa tsakiyar dare, ko
zuwa karshensa ba a karhanta ta
ba riwaya ce daya (daga Imam
Ahmad). An samu sabani ne game
da idan sun sake dawowa zuwa ga
yin nafilan kafin su yi barci, kuma
abin da yake ingantacce hakan ma
ba makruhi ba ne; saboda shi aikin
alheri ne da da’a ba za a karhanta
shi ba, kamar dai da zai jinkirta yin
shi zuwa karshen dare)). Intaha.
Wannan magana ta Ibnu
Qudaamah ya sake kawota cikin
littafin Al-Kaafii 1/154, kuma akwai
irinta cikin littafin Al-Mubdi2/16.
*************************************
‘Yan’uwa Musulmi! Sallar Ta’aqiibi
da wasu ke karhantawa ita ce
nafilar da ake yin ta cikin jama’ah
bayan an yi sallar tarawihi da kuma
sallar witiri, kamar yadda hakan ya
zo cikin littafin Al- Insaf na
Mardaawii 2/142, da kuma littafin
Sharhu Muntahal Iraadat1/245.
Toh amma nafilar da ake yi bayan
sallar taraawihi kafin a yi sallar
witiri kamar yadda ake yi cikin
kasashen duniya daban daban
wannan ba su karhanta ta ba,
saboda kasancewarta wacce ake
rufe ta da sallar witiri.
*************************************
‘Yan’uwa Musulmi! Ita wannan
sallar da ake kira “Salaatut
Ta’aqiib” ko “Tahajjud” da kuma
sallar da ake kira “Salaatut
Taraawih” dukkansu biyun sun
samo asali ne daga sunnar Annabi
mai tsira da amincin Allah. Zan
ambaci hadithai biyu kawai a nan:-
(1) Imam Ahmad ya ruwaito cikin
Musnad hadithi na 21,038, da
Imamut Tirmizii cikin Sunan hadithi
na 800, da Imamun Nasaa’ii cikin
Sunnan hadithi na1,606, da isnadi
sahihi cewa: Sahabi Abuu Zar
Allah ya kara masa yarda ya ce:-
(( ﺻﻤﻨﺎ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻠﻢ
ﻳﺼﻞ ﺑﻨﺎ ﺣﺘﻰ ﺑﻘﻲ ﺳﺒﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﻬﺮ ﻓﻘﺎﻡ ﺑﻨﺎ ﺣﺘﻰ
ﺫﻫﺐ ﺛﻠﺚ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺛﻢ ﻟﻢ ﻳﻘﻢ ﺑﻨﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﺩﺳﺔ ﻭﻗﺎﻡ ﺑﻨﺎ
ﻓﻲ ﺍﻟﺨﺎﻣﺴﺔ ﺣﺘﻰ ﺫﻫﺐ ﺷﻄﺮ ﺍﻟﻠﻴﻞ، ﻓﻘﻠﻨﺎ ﻟﻪ ﻳﺎ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻮ ﻧﻔﻠﺘﻨﺎ ﺑﻘﻴﺔ ﻟﻴﻠﺘﻨﺎ ﻫﺬﻩ؟ ﻓﻘﺎﻝ ﺇﻧﻪ ﻣﻦ
ﻗﺎﻡ ﻣﻊ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺣﺘﻰ ﻳﻨﺼﺮﻑ ﻛﺘﺐ ﻟﻪ ﻗﻴﺎﻡ ﻟﻴﻠﺔ. ﺛﻢ
ﻟﻢ ﻳﺼﻞ ﺑﻨﺎ ﺣﺘﻰ ﺑﻘﻲ ﺛﻼﺙ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﻬﺮ ﻭﺻﻠﻰ ﺑﻨﺎ
ﻓﻲ ﺍﻟﺜﺎﻟﺜﺔ ﻭﺩﻋﺎ ﺃﻫﻠﻪ ﻭﻧﺴﺎﺀﻩ ﻓﻘﺎﻡ ﺑﻨﺎ ﺣﺘﻰ ﺗﺨﻮﻓﻨﺎ
ﺍﻟﻔﻼﺡ، ﻗﻠﺖ ﻟﻪ: ﻭﻣﺎ ﺍﻟﻔﻼﺡ؟ ﻗﺎﻝ: ﺍﻟﺴﺤﻮﺭ )).
Ma’ana: ((Mun yi azumi tare da
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah bai yi salla (na nafilan dare)
tare da mu ba sai da kwana bakwai
kadai suka rage daga watan
(Ramadhan) sai ya yi mana limanci
(cikin sallar nafilan dare) har
( tsawon) kashi daya cikin uku na
dare ya tafi, sannan bai yi mana
salla ba a dare na shidan, sai
kuma ya yi mana salla a dare na
biyar sai da rabin dare ya tafi, sai
muka ce: Ya Manzon Allah! Da ka
ci gaba da yi mana limancin
nafilarmu cikin abin da ya rage na
wannan dare namu? Sai ya ce:
lalle yadda lamarin yake duk
wanda ya yi salla tare da liman har
(shi liman) ya gama ya tafi, toh za
a rubuta masa ladan sallatar
daransa, daga nan bai sake yi
mana salla ba sai da kwana uku ya
rage daga watar, sai ya yi mana
salla a dare na ukun, ya kuma kira
iyalansa da matansa, ya yi mana
limanci har muka ji tsoron Falaahi.
Sai na ce da shi: mene ne Falaahi?
Sai ya ce: Suhuur)). Intaha.
(2) Imamul Bukharii ya ruwaito
hadithi na1,988, da Imamu Muslim
hadithi na 1,734 daga Nana A’isha
Allah Ya kara mata yarda cewa
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah:-
((ﺧﺮﺝ ﻟﻴﻠﺔ ﻣﻦ ﺟﻮﻑ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻓﺼﻠﻰ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ،
ﻭﺻﻠﻰ ﺭﺟﺎﻝ ﺑﺼﻼﺗﻪ، ﻓﺄﺻﺒﺢ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﺘﺤﺪﺛﻮﺍ،
ﻓﺎﺟﺘﻤﻊ ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻨﻬﻢ، ﻓﺼﻠﻰ ﻓﺼﻠﻮﺍ ﻣﻌﻪ، ﻓﺄﺻﺒﺢ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﺘﺤﺪﺛﻮﺍ ﻓﻜﺜﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻴﻠﺔ ﺍﻟﺜﺎﻟﺜﺔ،
ﻓﺨﺮﺝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺼﻠﻲ
ﺑﺼﻼﺗﻪ، ﻓﻠﻤﺎ ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻟﻠﻴﻠﺔ ﺍﻟﺮﺍﺑﻌﺔ ﻋﺠﺰ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ
ﻋﻦ ﺃﻫﻠﻪ ﺣﺘﻰ ﺧﺮﺝ ﻟﺼﻼﺓ ﺍﻟﺼﺒﺢ، ﻓﻠﻤﺎ ﻗﻀﻰ
ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺃﻗﺒﻞ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﺘﺸﻬﺪ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﺃﻣﺎ ﺑﻌﺪ ﻓﺈﻧﻪ
ﻟﻢ ﻳﺨﻒ ﻋﻠﻲ ﻣﻜﺎﻧﻜﻢ. ﻭﻟﻜﻨﻲ ﺧﺸﻴﺖ ﺃﻥ ﺗﻔﺮﺽ
ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻓﺘﻌﺠﺰﻭﺍ ﻋﻨﻬﺎ ))
Ma’ana: ((Wani daren (cikin
Ramadan) ya fita cikin dare, sai ya
yi salla cikin masallaci, sai wasu
mutane suka bi shi salla, sai
mutane suka wayi gari suna ta
tadin lamarin, sai (kashe gari)
wadanda suka fi su yawa suka
taru, sai (Annabi) ya yi salla suka yi
salla tare da shi, sai mutane suka
wayi gari suka yi ta tadi, sai
mutanen masallaci suka yi yawa a
dare na uku, sai Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya fito aka yi
salla da sallarsa, toh da dare na
hudu ya zo sai masallaci ya kasa
daukar jama’arsa, har dai ya fito
saboda sallar asuba, toh a lokacin
da ya gama sallar safiya sai ya
fiskanci mutane ya shaida babu
abin bauta a bisa cancanta sai
Allah, sannan Muhammadu kuma
manzonSa ne, daga nan sai ya ce:
Bayan haka, lalle matsayinku bai
boyu gare ni ba, sai dai na ji tsoron
kada a farlanta muku sannan ku
kasa yin ta)). Intaha.
******************************
Muna rokon Allah da Ya karba
mana azuminmu, da kuma sallolin
Taraawiihinmu, da sallolin
Ta’aqiibinmu, ko Tahajjudinmu.
Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “SALLAR TAHAJJUD CIKIN JAMA'A A CIKIN RAMADAN(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. Aminu musa Avatar
    Aminu musa

    Jaxakallahu Khairan.

  2. […] SALLAR TAHAJJUD CIKINJAMA’A A CIKIN RAMADAN(Dr Ibrahim Jalo Jalingo). […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories