Tambaya: Meye Hukuncin Karanta Alqur’ani ko Yin Zikiri a kwance?
Amsa: babu laifi mutum ya karanta Alqur’ani ko Zikiri a kwance.
Dalili: An rawaito daga A’ishah Allah ya ƙara mata yarda tace:
Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya kasance yana kishingiɗa a wata Riwaya yana kwantar da kansa a Jiki na ta gaba alhali yana karanta Alqur’ani
Sahihul Bukhari: 297
Wannan Hadisi yana nuna halaccin Karatun Alqur’ani a kwance ko a kishingiɗe. Sannan babu laifi mutum ya karanta Alqur’ani yana jingine da iyalinsa koda kuwa tana Jinin Al’ada ne.
Allah shine mafi sani.
Leave a Reply