SUTURA DARAJAR DAN ADAM:
Allah yayi umarni da rufe tsiraici ga
Maza da mata don tabbatar mana
da darajar mu ta Dan Adam, kuma
aka yi mana baiwa da fifikon
matsayi tsakanin mu da dabbobi
wato aka bamu hankali da tunani
yadda muke Jin kunyar tallata
tsiraicin mu a fili.
Addinin Islama ya shiryar damu
yadda Allah yake so mu kasance
wajen suture jikin mu. Mu tuna fa
yana daga siffar mutanen baya ana
ambata mana a da can suna yawo
tsirara don rashin addini. Allah
cikin rahmar sa ya shiryar da
wadanda Allah ya nufe su da
shiriya da rufe tsiraici maza da
mata har saura suka koya.
Sannan aka sanya narko da horo
ga wadanda sukayiwa umarnin
Allah tawaye game da kin rufe
tsiraicin su, kamar yadda akayi
umarni.
Yan uwa mu dubi halin da muke
ciki a yanzu yadda ake gasar nuna
tsiraici, wassu ke son koyi da
kafirai don nuna wayewa, da
bushewar zuciya, tsaurin Kai da
rashin tsoron Allah. Annabi saw
yayi hani da sanya matsats-tsun
tufafi ga mata har ya ambata mana
yana daga alamun yan wuta sanya
tufafin da zasu barki tsirara bayan
kin sanya su. Kuma ya Hana Maza
wuce iyaka wajen sanya tufafi na
jan kasa musamman don alfahari.
Yanzu sai aka juya umarnin mata
suke takaita girman tufa don son
tallar jiki, Maza kuma suna sanya
tufa ta zarce yadda ake so, ko don
mi, oho?
Mu sani hakika bijirewa dokar
Allah wajen rufe tsiraici haramun
ne, kuma tozarta Kai ne, rashin
tarbiyya ne, koyi da kafirai ne,
fadawa rundunar shaidan ne,
alamu ne na yan wuta, nuna
kiyayya da sunnnar Annabi saw
ne, tawaye ne ga dokar Allah,
kuma zai jawo yawan fasadi da
barna a bayan kasa, sannan
rayuwa ba zatayi albarka ba.
Tilas ne ga hukumomi, iyaye,
malamai da sauran masu tarbiyya
su kula da yadda ake sa tufafi a
kan tituna, ofisoshi, tashoshin
mota, makarantu, gidajen biki, da
sauran wuraren da wani zai ga
wata. Hakanan Teloli da masu
sayar da tufafi aji tsoron Allah a
daina taimakawa wassu suna yiwa
dokar Allah tawaye.
Duk Wanda bai kiyaye Kansa ya
nisanci abinda Allah ya hanashi
ba, har yanayi da ganganci ko
alfahari to ya jira abinda zai same
shi duniya da lahira.
Leave a Reply