Shin karatun Alqur’ani da karanta Tarihin Annabi da Ayyukan alheri a ranar haihuwarsa da sunan Mauludi shine Bid’ah? Ai wannan duka ayyuka ne na alheri.
Amsa: Shin ƙara raka’a ɗaya a sallar asubahi ya zama raka’a uku, wanda acikin wannan raka’ar za’ayi tasbi da salatin Annabi da sauran ayyuka na ibada zai zama tsaɓa wa Allah? Ai wannan duka Ayyuka ne na Alheri.
Da irin wannan shubuhar ne masu Mauludi suke ruɗar mutane, sai suce mene ne aciki ai yabon Annabi ne da karanta Sirar sa.
To amsa kan wannan shubuhar shine kamar yadda muka amsa a sama, idan har mutum zai ƙara raka’a ɗaya a sallar Asubahi ko wani Sallah na farilla kuma ace masa yayi laifi bashi da Sallah duk da cewa abinda zaiyi acikin wannan raka’ar ba komi bane face ambaton Allah da salatin Annabi to haka nan duk wanda zai ƙirƙiri wani nau’in ibada ya nemi lada a wurin Allah dashi amma kuma babu umarnin Allah da Manzonsa kan aikata wannan ibada to shi mai laifi ne kuma bashi dada. Allah yasa mudace.
Leave a Reply