Mai rubutu: Hamza Diso
Idan muka kalli halal akan kansa zamu ga babu lada ko Alhaki ayinsa ko barinsa, ta wannan bangaren babu falala acikin barin halal don barin nasa shima halal ne, kenan babu banbanci tsakanin Wanda ya aikata shi da Wanda ya barshi, wata kila wani zai iya cewa: to ai an ruwaito wasu cikin magabata suna cewa” muna sanya shinge na halal tsakanin mu da haram”.. Kenan akwai falala acikin barin wani nau’i na halal!!
Abinda magabata suke nufi da wannan maganar shine barin halal din da zai iya kaiwa zuwa haram, ba don kasancewar sa a matsayin halal tsantsa ba, kenan dai shi halal akan sa babu falala akan barin sa.
To amma akwai abinda asalinsa halal ne sai dai yawan yinsa yana kaiwa zuwa ga haram, ko makaruhi to irin wannan shine abinda barinsa yake zuhudu ko tsantseni, kamar yadda akwai halal din da yinsa jifa-jifa bashi da laifi, sai dai dawwama akansa ko yaushe makaruhi ne to barin irin wannan aiki shima tsantseni ne kuma zuhudi ne, misali yawan wasanni a kowanne lokaci kamar WHOT (idan bata hana sallah ba bata hada rigima tsakanin mutane ba) yinta a wani lokaci Na faraga halal ne amma barinta zuhudu ne kuma tsantseni ne.
Amma duk wani halal Wanda ba wasa ba kuma baya kaiwa zuwa ga wani Abu mummuna to babu falala akan barinsa kamar saka tufafi mai kyau da cin Abinci mai dadi da hawa mota mai lafiya da gina gida mai yalwa, wadannan yinsu baya Kore zuhudu ko tsantseni, kada kace “to ai ga wasu cikin magabata suna gudun wadannan abubuwa” don zance maka shugaban masu tsantseni Annabin Rahama yana son Zaki da Zuma da nama.
Zuhudu shine barin makaruhi da kuma halal din da zai iya kaiwa zuwa ga haram, shiyasa cikin sahabbai akwai wasu yalwar Arziki masu saka kaya masu kyau da cin Abinci mai kyau da makamantansu
Watakila wani yace: to ai aikata halal yana sawa mutum yabar aikata mustahabbi a lokacin da yake aikata halal din, don haka Barin wannan halal din yafi falala!!
To ai aikata halal kamar yadda ya hana aikata mustahabbi haka kuma ya hana aikata makaruhi da haramun, saboda haka babu bangaren dayafi rinjaye, bari ma akwai halal din da barinsa gaba daya kuskure ne idan bai zama haramun ba, saboda barinsa zai jefa mutum cikin matsi, shi kuma matsi ba abun yabo bane a Addini
Leave a Reply