TSARABA DAGA GARIN JIMETA-YOLA MAGANAR ANNABI ITA CE GABA DA MAGANAR KOWA KOMIN GIRMANSA CIKIN ADDINI: 10/3/1435 H 11/1/2014 M (Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

‘Yan’uwa Musulmi! Barkanmu da war
haka, bayan haka, babban malamin
Musulunci Alhafiz Ibnu Rajab wanda
ya mutu a shekarar hijira ta 795
watau yau shekaru 640 ke nan da
suka wuce, ya yi wa malamai wata
maga da ya kamata a rubuta ta da
ruwan zinari, ya ce cikin littafinsa mai
suna Alhikamul Jadiiratu Bil Iza’ah
shafi na 12:-
(( ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻼﻣﺔ ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ
ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ ﻋﻈﻴﻢ
ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺔ؛ ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍﻱ
ﻣﻌﻈﻢ ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﺍﻻﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ، ﻭﻣﻦ
ﻫﻨﺎ ﺭﺩ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺨﺎﻟﻒ ﺳﻨﺔ
ﺻﺤﻴﺤﺔ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﺍﻏﻠﻈﻮﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﺩ ﻻ ﺑﻐﻀﺎ ﻟﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ
ﻣﺤﺒﻮﺏ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻌﻈﻢ ﻓﻲ ﻧﻔﻮﺳﻬﻢ، ﻭﻟﻜﻦ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻭﺃﻣﺮﻩ ﻓﻮﻕ ﺍﻣﺮ ﻛﻞ ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻓﺈﺫﺍ
ﺗﻌﺎﺭﺽ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺃﻣﺮ ﻏﻴﺮﻩ ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻭﻟﻰ
ﺍﻥ ﻳﻘﺪﻡ ﻭﻳﺘﺒﻊ ﻭﻻ ﻳﻤﻨﻊ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﺗﻌﻈﻴﻢ ﻣﻦ
ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻐﻔﻮﺭﺍ ﻟﻪ، ﺑﻞ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻤﺨﺎﻟﻒ
ﺍﻟﻤﻐﻔﻮﺭ ﻟﻪ ﻻ ﻳﻜﺮﻩ ﺍﻥ ﻳﺨﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﺍﺫﺍ ﻇﻬﺮ ﺍﻣﺮ
ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﺨﻼﻓﻪ( ( . ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((wajibi ne a kan dukkan
wanda umurnin Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya isa zuwa
gare shi, ya kuma san shi, ya
bayyana shi ga Al’ummah, ya musu
nasiha, ya umurce su da bin
umurninsa koda kuwa hakan ya saba
wa ra’ayin wani babba a cikin
Al’ummah, saboda umurnin Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah shi
ya fi cancantar a girmama shi, kuma
a yi koyi da shi a kan ra’ayin dukkan
wani wanda ake girmamawa amma
kuma umurninsa ya saba wa umurnin
shi cikin sashin lamura cikin kure,
wannan shi ya sa ma Sahabbai da
wadanda suka biyo bayansu suka yi
wa dukkan wanda ya saba wa
Sahihiyar Sunnah raddi, wani lokaci
ma raddi mai kaushi, ba wai kuma
saboda suna nuna kiyayya ba ce
gare shi, a’a yana nan abin so a gare
su kuma abin girmamawa a cikin
rayukansu, to amma Manzon Allah
shi ne mafi soyuwa a gare su,
sannan umurninsa shi yake sama da
umurnin ko wace halitta. Saboda
haka idan umurnin Manzon Allah ya
yi karo da umurnin waninsa, to
umurnin Manzon Allah shi ya fi
cancantar a gabatar kuma a bi,
wannan kuwa ba zai hana a girmama
mutumin da ya saba wa umurnin
Manzon Allah ba matukar dai ana
gafarta wa kuren cikin Sahari’ah,
kuma shi wannan da ya yi sabon
cikin kure ba zai nuna kyamar a saba
wa umurninsa matukar dai umurnin
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah ya bayyana a matsayin mai
saba masa)). Intaha.
*************************************
Sannan Sheik Uthmanu Dan Fodiyo
ya yi wata magana mai kyawun gaske
wacce za ta amfanar da masu wa’azi
a cikin littafinsa mai suna Ihyaa’us
Sunnah wa Ikhmaadul Bid’ah shafi na
8:-
(( ﻗﺪ ﺍﻧﻌﻘﺪ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺁﺭﺍﺀ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪﻳﻦ ﻛﻠﻬﺎ
ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻃﺮﻕ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ ﻓﻤﻦ ﺳﻠﻚ
ﻣﻨﻬﺎ ﻃﺮﻳﻘﺎ ﻭﺻﻠﻪ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﻭﺻﻠﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺣﻘﺎً ﻭﻣﻦ
ﻋﺪﻝ ﻋﻨﻪ ﻗﻴﻞ ﻟﻪ ﺳﺤﻘﺎ ! ﻭﻳﺠﻮﺯ ﺗﻘﻠﻴﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ
ﺭﺃﻱ ﺍﻻ ﻣﺎ ﺧﺎﻟﻒ ﻧﺺ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﺍﻭ ﻧﺺ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻭ
ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻟﺠﻠﻲ، ﻓﺎﻓﻬﻢ( ( . ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ijma’i ya kullu a kan cewa:
dukkan ra’ayoyin Mujtahidai mashiga
ce ta zuwa Aljanna, kuma hanyoyi ne
na alkhairai, wanda duk ya bi wata
hanya cikinsu tabbas za ta kai shi
inda suka kai, wanda kuma ya baude
ga barin su sai a ce da shi tir.
Sannan yana halatta a yi koyi da su
cikin ko wane ra’ayi, amma banda
abin da ra’ayin da ya saba wa nassin
Alkur’ani, ko nassin Hadithi, ko saba
wa Ka’idodi, da Ijma’i, ko Kiyasi
Jaliyyi, ka fahimta)). Intaha.
**********************************
‘Yan’uwa Musulmi! Dukkan abin da
mutum ya san cewa: Annabi mai
tsira da amincin Allah ya yi umurni
da yin sa, to wajibi ne ya bayyanar da
shi ga Al’ummah, sannan da za a
samu wani mai son zuciya da zai yi
kokarin hana shi yin hakan to ba zai
saurara masa ba, wannan shi ne
daidai kuma shi ne hanyar Annabi da
sauran Maluman Sunnah kamar su
Babban masani a ilmin Hadithi Ibnu
Rajab.
***********************************
Haka nan haramun ne a kan kowane
Musulmi ya bi ijtihadin wani malami
komin girmansa matukar dai ijtihadin
ya saba wa nassin Alkur’ani, ko
nassin Hadithi, ko nassin Ijma’i, ko
Kiyasi Jaliyyi, kamar dai yadda Sheik
Uthmanu Dan Fodiyo ya bayyana wa
dukkan al’ummar Musulmi.
********************************
‘Yan’uwa Musulmi! Hakika, mun sani
sau da dama karkatattu cikin ko wane
zamani suna amfani da lafazin “wane
na raba kan Al’umma” ko “Wane ba
ya son hadin kan Al’umma” saboda
neman rufe wata barna da Sari’ar
Musulunci ta ce a bayyana ta, ko
kuwa saboda kare wata barna da
shari’ar Musulunci ta ce a yake ta, to
amma irin wannan jinsi na mutane ba
za a saurare su ba saboda dillacin
Duniya ne yake gabansu, lalle rashin
sauraron wadannan shi ne hanyar
Annabi mai tsira da aminci Allah,
kuma shi ne hanyar Kungiyar
Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis
Sunnah tun lokacin kafuwarta
13/8/1978 M.
Alhafizu Ibnu Katheer ya ce cikin
littafinsa Albidayatu wannihayah
3/55-56:-
(( ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﺒﻴﺮ ﻭﻋﻜﺮﻣﺔ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﻗﺎﻝ :
ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻠﻴﺔ ﻣﻦ ﺍﺷﺮﺍﻑ ﻗﺮﻳﺶ ﻭﻋﺪﺩ ﺃﺳﻤﺎﺀﻫﻢ ﺑﻌﺪ
ﻏﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻋﻨﺪ ﻇﻬﺮ ﺍﻟﻜﻌﺒﺔ، ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ
ﻟﺒﻌﺾ : ﺍﺑﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻓﻜﻠﻤﻮﻩ، ﻭﺧﺎﺻﻤﻮﻩ ﺣﺘﻰ
ﺗﻌﺬﺭﻭﺍ ﻓﻴﻪ، ﻓﺒﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻥ ﺍﺷﺮﺍﻑ ﻗﻮﻣﻚ ﻗﺪ
ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ ﻟﻚ ﻟﻴﻜﻠﻤﻮﻙ، ﻓﺠﺎﺀﻫﻢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺮﻳﻌﺎ، ﻭﻫﻮ ﻳﻈﻦ ﺍﻧﻪ ﻗﺪ ﺑﺪﺍ ﻟﻬﻢ
ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻩ ﺑﺪﺀ، ﻭﻛﺎﻥ ﺣﺮﻳﺼﺎ ﻳﺤﺐ ﺭﺷﺪﻫﻢ ﻭﻳﻌﺰ
ﻋﻠﻴﻪ ﻋﻨﺘﻬﻢ، ﺣﺘﻰ ﺟﻠﺲ ﺍﻟﻴﻬﻢ . ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻧﺎ
ﻗﺪ ﺑﻌﺜﻨﺎ ﺇﻟﻴﻚ ﻟﻨﻌﺬﺭ ﻓﻴﻚ، ﻭﺍﻧﺎ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﻌﻠﻢ ﺭﺟﻼ
ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺮﺏ ﺍﺩﺧﻞ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻪ ﻣﺎ ﺃﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ
ﻗﻮﻣﻚ؛ ﻟﻘﺪ ﺷﺘﻤﺖ ﺍﻵﺑﺎﺀ ﻭﻋﺒﺖ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﻭﺳﻔﻬﺖ
ﺍﻵﻟﻬﺔ ﻭﻓﺮﻗﺖ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ، ﻭﻣﺎ ﺑﻘﻲ ﻣﻦ ﻗﺒﻴﺢ ﺍﻻ ﻭﻗﺪ
ﺟﺌﺘﻪ ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻨﻚ ..)).
Ma’ana: ((Daga Sa’id Da Jubair da
Ikrimah, daga Dan Abbas ya ce:
Shugabannin Quraishawa sun hadu a
Dakin Ka’abah, sannan suka aika wa
Annabi mai tsira da amincin Allah
cewa suna bukatar zama da shi, nan-
da-nan Annabi mai tsira da amincin
Allah ya je ya same su saboda
tsammanin da yake yi na cewa za su
musulunta ne, domin shi har kullum
yana son musu alheri ne kuma ba ya
son abin da zai wahalce su. Da ya zo
ya zauna a inda suke sai suka ce da
shi: Ya Muhammad! Lalle, mun aika
Maka ne domin mu yanke uzurinmu
gare ka, wallahi mu ba mu taba ganin
wani mutum daga cikin Larabawa da
ya kawo musiba cikin jama’arsa ba
kamar yadda ka kawo musiba cikin
jama’arka ba. Hakika ka zagi
iyayenmu, kuma ka aibanta
addininmu, sannan ka maida masu
hankalinmu wawaye, ka kuma zagi
allolinmu, ka raba kawunan
jama’armu. Babu dai wani
mummunan da ya rage wanda ba ka
sanya shi tsakaninmu ba..)). Intaha.
Ku dubi wadannan karkatattun!! Wai
daga cikin laifukan da suke zargin
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah cewa yana yi akwai raba
kawunan jama’a, saboda kawai ya ce:
A bi Addinin gaskiya, kada a karbi
umurnin kowa matukar ya saba wa
umurnin Allah Madaukakin Sarki, da
ManzonSa mai tsira da aminci.
Wannan ita ce al’adar karkatattu,
sawa’un mushrukai ne su masu
bautar gumaka, ko kuwa kafurai ne
ma’abuta littafi, ko kuwa fasikai ne
da ‘yan bidi’ah cikin Al’ummar
Musulmi. Wannan shi ya sa a
shekarun farko na kafuwar Kungiyar
Izala babban abin da ‘yan bidi’ah da
ma’abuta maslahar kai suke tuhumar
masu wa’azi a cikinta da shi, shi ne:
Su masu raba kawunan al’umma ne,
masu bata tafiyar Al’ummar Musulmi
ne, ba sa yin magana a kan abin da
aka yi ittifaki a kan sa sun koma
suna magana a kan sabanin fahimta,
maimakon su shiga daji su
musuluntar da maguzawa sai ga shi
sun koma suna cewa wai Darikah ba
ta da kyau, wai Shi’ah ba Musulunci
ba be, wani abin dariya ma wai taron
suna bidi’a ce! wai addu’a bayan
salla cikin jam’i bidi’a ce, kai lalle
wadannan mutane sun cika fitina tir
da halayensu, kuma dole ne a hadu a
yake su domin Musulmi su huta da
musibarsu!!
‘yan’uwa masu kaunar Sunnah!
Wannan shi ne abin da yake faruwa
har kullum tsakanin masu neman a
kudurta gaskiya, a kuma fadi gaskiya,
sannan a yi aiki da gaskiya cikin
dukkan kome.
Muna rokon Allah da Ya tabbatar da
dugaduganmu a kan bin sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah.
Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories