YADA MANUFAR IZALA SHI NE WAJIBI BA WAI LAFUZAN IZALA BA(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

YADA MANUFAR IZALA SHI NE
WAJIBI BA WAI LAFUZAN IZALA
BA:
Lalle yada manufar Kungiyar
Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa
Iqamatis Sunnah wanda shi ne: Yin
aiki tukuru saboda kauda bidi’o’in
da aka cusa cikin addinin
Musulunci, da kuma yin aiki tukuru
saboda Musulmi su tsaida sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah
cikin aqidarsu, da Ibadarsu, da
kuma mu’amalarsu, yada wannan
manufa ta Kungiyar Izala shi ne
wajibi a kan dukkan wani malami
mai wa’azi a cikin Kungiyar.
Ikirarin wani na ya ce: Shi dan
Izala ne ba shi ne muhimmi ba a
wurin ma’abuta ilmin Shari’ah, a’a
abin da yake muhimmi shi ne: Yin
aiki da manufar Kungiyar Izalar,
watau bin sahihiyar sunnar Annabi
mai tsira da amincin Allah cikin
Aqidah, da Ibadah, da Mu’amalah.
Da za a kaddara wani zai ce: Shi
bai san Kungiyar Izala ba, to amma
kuma yana aiki da sunnar Annabi
cikin Aqidarsa, da Ibadarsa, da
Mu’amalarsa, to lalle wannan a
wurinmu shi mutumin kirki ne,
kuma dukkan wani dan Kungiyar
Izala dole ne ya so shi ya kuma
jibance ahi.
Da kuma za a kaddara cewa wani
zai ce: Shi dan Izala ne kuma mai
kaunar Kungiyar Izala to amma
kuma ba ya aiki da sahihiyar
sunnar Annabi cikin Aqidarsa, da
Ibadarsa, da kuma Mu’amalarsa, to
lalle wannan a wurinmu mutumin
banza ne, kuma dukkan wani na
kwarai cikin Kungiyar Izala ba zai
so shi ba’ kuma ba zai jibance shi
ba. Lalle wannan ita ce: Aqidar
Ahlus Sunnah Wal Jama’ah a duk
inda suke a Duniya.
***********************************
Babban Alamin Sunnah Alhafiz
Ibnu Rajab wanda ya mutu a
shekarar hijira ta 795 watau yau
shekaru 639 ke nan da suka wuce,
ya yi wa malaman Musulunci wata
maga da ya kamata a rubuta ta da
ruwan zinari, ya ce cikin littafinsa
mai suna Alhikamul Jadiratu Bil
Iza’ah shafi na 12:-
(( ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻼﻣﺔ ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ
ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ ﻋﻈﻴﻢ
ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺔ؛ ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍﻱ ﻣﻌﻈﻢ
ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﺍﻻﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ، ﻭﻣﻦ ﻫﻨﺎ
ﺭﺩ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺨﺎﻟﻒ ﺳﻨﺔ
ﺻﺤﻴﺤﺔ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﺍﻏﻠﻈﻮﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﺩ ﻻ ﺑﻐﻀﺎ ﻟﻪ، ﺑﻞ
ﻫﻮ ﻣﺤﺒﻮﺏ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻌﻈﻢ ﻓﻲ ﻧﻔﻮﺳﻬﻢ، ﻭﻟﻜﻦ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻭﺃﻣﺮﻩ ﻓﻮﻕ ﺍﻣﺮ ﻛﻞ
ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻓﺈﺫﺍ ﺗﻌﺎﺭﺽ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺃﻣﺮ ﻏﻴﺮﻩ
ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻭﻟﻰ ﺍﻥ ﻳﻘﺪﻡ ﻭﻳﺘﺒﻊ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((wajibi ne a kan dukkan
wanda umurnin Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya isa zuwa
gare shi, ya kuma san shi, ya
bayyana shi ga Al’ummah, ya
musu nasiha, ya umurce su da bin
umurninsa koda kuwa hakan ya
saba wa ra’ayin wani babba cikin
Al’ummah, saboda umurnin
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah shi ya fi cancantar a girmama
shi, kuma a yi koyi da shi a kan
ra’ayin dukkan wani wanda ake
girmamawa amma kuma
umurninsa ya saba wa umurnin shi
cikin sashin lamura cikin kure,
wannan shi ya sa ma Sahabbai da
wadanda suka biyo bayansu suka
yi wa dukkan wanda ya saba wa
Sahihiyar Sunnah raddi, wani
lokaci ma raddi mai kaushi, ba wai
kuma saboda suna nuna kiyayya
ba ne gare shi, a’a yana nan abin
so a gare su kuma abin
girmamawa a cikin rayukansu, to
amma Manzon Allah shi ne mafi
soyuwa a gare su, sannan
umurninsa shi yake sama da
umurnin ko wace halitta. Saboda
haka idan umurnin Manzon Allah
ya yi karo da umurnin waninsa, to
umurnin Manzon Allah shi ya fi
cancanta da a gabatar)). Intaha.
**************************************
Mujaddidi Shehu Uthmanu Dan
Fodiyo shi ma ya ce littafin Ihya’us
Sunnah shafi na 8:-
(( ﻗﺪ ﺍﻧﻌﻘﺪ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺁﺭﺍﺀ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪﻳﻦ ﻛﻠﻬﺎ
ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻃﺮﻕ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ ﻓﻤﻦ ﺳﻠﻚ
ﻣﻨﻬﺎ ﻃﺮﻳﻘﺎ ﻭﺻﻠﻪ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﻭﺻﻠﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺣﻘﺎ ﻭﻣﻦ
ﻋﺪﻝ ﻋﻨﻪ ﻗﻴﻞ ﻟﻪ ﺳﺤﻘﺎ! ﻭﻳﺠﻮﺯ ﺗﻘﻠﻴﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ
ﺭﺃﻱ ﺍﻻ ﻣﺎ ﺧﺎﻟﻒ ﻧﺺ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﺍﻭ ﻧﺺ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻭ
ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻟﺠﻠﻲ، ﻓﺎﻓﻬﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ijma’i ya kullu a kan
cewa: dukkan ra’ayoyin Mujtahidai
mashiga ce ta zuwa Aljanna, kuma
hanyoyi ne na alkhairai, wanda duk
ya bi wata hanya cikinsu tabbas za
ta kai shi inda suka kai, wanda
kuma ya baude ga barin su sai a
ce da shi tir. Sannan yana halatta a
yi koyi da su cikin ko wane ra’ayi,
amma banda abin da ra’ayin da ya
saba wa nassin Alkur’ani, ko
nassin Hadithi, ko saba wa
Ka’idodi, da Ijma’i, ko Kiyasi Jaliyyi,
ka fahimta)). Intaha.
*********************************
Maganganun wadannan maluman
Sunnah suna koya mana cewa
abin da yake muhimmi shi ne yin
aiki da ingantattun sunnonin
Annabi mai tsira da amincin Allah,
sannan kuma dukkan abin da
malamai suka san cewa: Annabi
mai tsira da amincin Allah ya yi
umurni da yin sa, to wajibi ne su
bayyanar da shi ga Al’ummah, da
kuma za a samu wani mai son
zuciya da zai yi kokarin hana su yin
hakan to ba za su saurara masa
ba.
Sannan kuma haramun ne a kan
kowane Musulmi ya bi ijtihadin
wani malami komin girmansa
matukar dai ijtihadin nasa ya saba
wa nassin Alkur’ani, ko nassin
Hadithi, ko nassin Ijma’i, ko Kiyasi
Jaliyyi.
********************************************
MALUMAN SUNNAH MASU
WA’AZI DOLE NE SU RIKA YIN
HAKURI
Lalle an sani sau da dama
karkatattu -mazansu da matansu,
malumansu da jahilansu- cikin ko
wane zamani su kan yi amfani da
lafuzan zagi da batunci ba tare da
kafa wata hujja ba, saboda kawai
neman hana mutane fahimtar
gaskiya da yin aiki da ita! Suna iya
siffanta mai musu wa’azi da cewa:
Kafuri ne shi, ko Munafuki ne shi,
ko mai raba kan al’ummah ne shi,
ko mai neman duniya ne shi, ko
mai neman mulki ne shi, da dai
sauran lafuzza masu kama da
wadannan.
To, amma irin wannan jinsi na
mutane maluma masu wa’azi ba za
su saurare su ba saboda rashin
sauraron nasu shi ne hanyar
Annabi mai tsira da aminci Allah,
Alhafizu Ibnu Katheer ya ce cikin
littafinsa Albidayatu wannihayah
3/55-56:-
(( ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﺒﻴﺮ ﻭﻋﻜﺮﻣﺔ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ
ﻗﺎﻝ: ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻠﻴﺔ ﻣﻦ ﺍﺷﺮﺍﻑ ﻗﺮﻳﺶ ﻭﻋﺪﺩ
ﺃﺳﻤﺎﺀﻫﻢ ﺑﻌﺪ ﻏﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻋﻨﺪ ﻇﻬﺮ ﺍﻟﻜﻌﺒﺔ،
ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ: ﺍﺑﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻓﻜﻠﻤﻮﻩ،
ﻭﺧﺎﺻﻤﻮﻩ ﺣﺘﻰ ﺗﻌﺬﺭﻭﺍ ﻓﻴﻪ، ﻓﺒﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻥ
ﺍﺷﺮﺍﻑ ﻗﻮﻣﻚ ﻗﺪ ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ ﻟﻚ ﻟﻴﻜﻠﻤﻮﻙ، ﻓﺠﺎﺀﻫﻢ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺮﻳﻌﺎ، ﻭﻫﻮ
ﻳﻈﻦ ﺍﻧﻪ ﻗﺪ ﺑﺪﺍ ﻟﻬﻢ ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻩ ﺑﺪﺀ، ﻭﻛﺎﻥ ﺣﺮﻳﺼﺎ
ﻳﺤﺐ ﺭﺷﺪﻫﻢ ﻭﻳﻌﺰ ﻋﻠﻴﻪ ﻋﻨﺘﻬﻢ، ﺣﺘﻰ ﺟﻠﺲ ﺍﻟﻴﻬﻢ.
ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻧﺎ ﻗﺪ ﺑﻌﺜﻨﺎ ﺇﻟﻴﻚ ﻟﻨﻌﺬﺭ ﻓﻴﻚ، ﻭﺍﻧﺎ
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﻌﻠﻢ ﺭﺟﻼ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺮﺏ ﺍﺩﺧﻞ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻪ ﻣﺎ
ﺃﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻚ؛ ﻟﻘﺪ ﺷﺘﻤﺖ ﺍﻵﺑﺎﺀ ﻭﻋﺒﺖ ﺍﻟﺪﻳﻦ،
ﻭﺳﻔﻬﺖ ﺍﻵﻟﻬﺔ ﻭﻓﺮﻗﺖ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ، ﻭﻣﺎ ﺑﻘﻲ ﻣﻦ
ﻗﺒﻴﺢ ﺍﻻ ﻭﻗﺪ ﺟﺌﺘﻪ ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻨﻚ ..)).
Ma’ana: ((Daga Sa’id Da Jubair da
Ikrimah, daga Dan Abbas ya ce:
Shugabannin Quraishawa sun
hadu a Dakin Ka’abah, sannan
suka aika wa Annabi mai tsira da
amincin Allah cewa suna bukatar
zama da shi, nan-da-nan Annabi
mai tsira da amincin Allah ya je ya
same su saboda tsammanin da
yake yi na cewa za su musulunta
ne, domin shi har kullum yana son
musu alheri ne kuma ba ya son
abin da zai wahalce su. Da ya zo
ya zauna a inda suke sai suka ce
da shi: Ya Muhammad! Lalle, mun
aika Maka ne domin mu yanke
uzurinmu gare ka, wallahi mu ba
mu taba ganin wani mutum daga
cikin Larabawa da ya kawo musiba
cikin jama’arsa ba kamar yadda ka
kawo musiba cikin jama’arka ba.
Hakika ka zagi iyayenmu, kuma ka
aibanta addininmu, sannan ka
maida masu hankalinmu wawaye,
ka kuma zagi allolinmu, ka raba
kawunan jama’armu. Babu dai
wani mummunan da ya rage
wanda ba ka sanya shi tsakaninmu
ba..)). Intaha.
***************************************
‘Yan’uwa Musulmi! Don Allah ku
dubi wadannan kafurai, wai daga
cikin laifuffukan da suke zargin
Manzon Allah da su akwai: Raba
kawunan jama’a! saboda kawai ya
ce: A bi Addinin gaskiya, kada a
karbi umurnin kowa matukar ya
saba wa umurnin Allah
Madaukakin Sarki, da ManzonSa
mai tsira da amincin Allah.
Wannan ita ce al’adar karkatattu,
sawa’un mushrukai ne su masu
bautar gumaka, ko kuwa kafurai ne
ma’abuta littafi, ko kuwa munafukai
ne, ko kuwa fasikai ne ‘yan bidi’ah
cikin Al’ummar Musulmi. Wannan
shi ya sa ma a shekarun farko na
kafuwar Kungiyar Izala babban
abin da ‘yan bidi’ah da ma’abuta
maslahar kai suke tuhumar masu
wa’azi a cikinta da shi, shi ne: Su
masu raba kawunan al’umma ne,
masu bata tafiyar Al’ummar
Musulmi ne, ba sa yin magana a
kan abin da aka yi ittifaki a kan sa
sun koma suna magana a kan
sabanin fahimta, maimakon su
shiga daji su musuluntar da
maguzawa sai ga shi sun koma
suna cewa wai Darikah ba ta da
kyau, wai Shi’ah ba Musulunci ba
be, wani abin dariya ma wai taron
radin suna bidi’a ne! wai addu’a
bayan salla cikin jam’i bidi’a ce, kai
lalle wadannan mutane sun cika
fitina tir da halayensu, kuma dole
ne a hadu a yake su domin
Musulmi su huta da musibarsu, a
samu hadin Al’ummar Musulmi
cikin wannan Kasa Nigeria!!!
*********************************************
Lalle yada manufar Kungiyar
Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa
Iqamatis Sunnah wanda shi ne: Yin
aiki tukuru saboda kauda bidi’o’in
da aka cusa cikin addinin
Musulunci, da kuma yin aiki tukuru
saboda Musulmi su tsaida sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah
cikin aqidarsu, da Ibadarsu, da
kuma mu’amalarsu, yada wannan
manufa ta Kungiyar Izala shi ne
wajibi a kan dukkan wani malami
mai wa’azi a cikin Kungiyar.
Sannan Ikirarin wani na ya ce: Shi
dan Izala ne ba shi ne muhimmi ba
a wurin ma’abuta ilmin Shari’ah,
a’a abin da yake muhimmi shi ne:
Yin aiki da manufar Kungiyar
Izalar, watau bin sahihiyar sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah
cikin Aqidah, da Ibadah, da
Mu’amalah. Allah Ya taimake mu.
Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “YADA MANUFAR IZALA SHI NE WAJIBI BA WAI LAFUZAN IZALA BA(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. Hafiz maiakwai Avatar

    Izala kungiya ce da ta dade tana karantar da jama’ar musulmi mutane da aljannu da duk abinda ake fada ya fahimta.Allah ya biya da alheri.

Leave a Reply

Categories
Latest updates