Tambaya: Shin idan ana bin Mutum Sallah dole sai ya rama su a jere? Misali ana bin mutum Sallar La’asar har magrib ya shigo shin zai fara ƙaddamar da sallar la’asar ne kafin magrib? Ko kuma zai fara yin magriba ne kafin La’asar?
Amsa: Ya kamata mu sani cewa jinkirta sallah ba tare da wani dalili ba babban laifi ne. Baya halatta Musulmi ya jinkirta Sallah sai dai in akwai dalilin yin hakan.
Jeranta Sallah wajibi ne awurin Jamhurin Maluma kamar yadda yazo acikin Mausu’atul Fiqhiyya: 11/164
Jamhurun Maluma na Mazhabar Hanafiyya da Malikiyya da Hanabila sun tafi kan cewa wajibi ne a jeranta tsaƙanin Salloli da suka wuce, Hakanan jeranta Sallar da ta wuce da wadda ake cikin lokacin ta idan har akwai lokacin yin hakan
Mausu’atul Fiqhiyya: 11/164
Wannan yake nuna cewa idan ana bin Mutum Salloli masu yawa to zai jeranta su ne daga na farko har zuwa na ƙarshe.
Sai dai Imamu Malik da Abu Hanifa suna ganin cewa idan har sallolin da ake bin mutum ya wuce na kwana ɗaya to ba dole sai ya jeranta su ba.
Saboda haka zamu fahimci abubuwa kaman haka:
- Jamhurun Maluma sun tafi kan cewa Jeranta salloli da suka wuce wajibi ne. Amma Imamu Malik da Abu Hanifa suna ganin cewa idan sallolin sun wuce na kwana ɗaya to ba dole sai an jeran ta su ba.
- Wanda ake binsa Sallah kuma kafin ya rama ta, sallar da ake cikin lokacin ta zata wuce zai gabatar da wadda ake cikin lokacin ta kafin ya rama wadda ta wuce.
An tambayi Sheikh Bin Baz Allah yayi masa rahama game da mutumin da ake binshi salloli da yawa kuma yana tsoron idan ya tsaya yin wa’innan salloli da ake binshi lokacin Sallar da ake ciki zai fita yaya zaiyi?
Sheikh yace: Zaiyi sallah gwargwadon iko. Zai fara gabatar da sallar da ake lokacin ta, idan yaji tsoron fitan lokaci. Sannan sai yayi sallolin da ake bin shi, amma idan lokacin yana da faɗi to zai fara gabatar da Salloli ne da ake bin shi
Danna nan domin karanta Nassin Fatawar ta Sheikh Bin Baaz.
Allah shine mafi sani.
Leave a Reply